GICCIYEN ALMASIHU GASKIYA NE, BA ALMARA BA

GICCIYEN ALMASIHU GASKIYA NE, BA ALMARA BA

JOHN GILCHRIST


Gicciyen Almasihu: Gaskiya Ne, Ba Almara Ba

Littafi Mai Tsarki kamar kan maƙera ne in da an sha buga guduma masu yawa sun kakkarye ba su yi masa kome ba, duk da haka maƙiya ba su taɓa gajiya ba cikin ƙoƙarin su na yi masa lahani. Ahmed Deedat na Cibiyar Farfaganda a Durban ya ɗan ci gaba da ɓatanci a cikin ɗan littafinsa mai suna da turanci “Was Christ Crucified?” (wato Ko an Gicciye Almasihu), ko da shike an rarrabar da dubban ɗaruruwan littattafai ba su yi wa Littafi Mai Tsarki kome ba, maimakon Deedat ya ƙyale wannan batu, sai ya wallafa wannan ɗan littafi na turanci “Crucifixion or Cruci-fiction”

Dukan tsaikon ɗan littafin nan shi ne, wai Yesu mai karyayyen hali ne, ya shirya juyin mulki wanda bai yi nasara ba a Urushalima, wanda kuma ya ci sa’a, an gicciye shi amma bai mutu ba a kan gicciyen. Wannan ra’aiyi ba shi da wani tushe bisa ga Littafi Mai Tsarki, Kur’ani ma ya nuna akasin wannan ra’ayi, don shi ya koyar da cewa ba a taɓa gicciye Yesu ba (Suratun Nisa 4:157). Ahmadiyya ne kaɗai suke aiki da wannan ra’ayi su da ke a Pakistan wanda an ɗauke shi ba aikin addinin Musulinci ba ne, na tsafi ne. Deedat ne kaɗai ya san dalilin da ya sa ya ci gaba da ɗaure wa wannan mataccen ra’ayi gindi, yana ta fafitikar rayar da ra’ayin da matacce ne ga Kirista na gaskiya, har da Musulmi na ƙwarai.

A cikin ɗan littafin nan, muna kafa suka ne a kan rubutun Deedat cikin ɗan littafinsa, muna mai da hankali kaɗai a kan batun da ke gabanmu kawai ba tare da bi ta kan wasu abubuwa da dama ba da suke cikin rubutunsa inda ya kauce, ya ke rubutu zallan daɗin baki kawai.

1. KO YESU YA YI SHIRIN JUYIN MULKI?

A sashin farko na littafinsa, Deedat ya taƙarƙare a kan batunsa wai cikin makon ƙarshe na zaman Yesu a Duniya, sai ya shirya Juyin Mulki a cikin Urushalima wanda bai yi nasara ba. A ƙarƙashin kan magana mai suna da turanci, “An aborted coup”, wato Juyin Mulkin da bai yi Nasara Ba, a ciki ya ce, “ ...dogon bagensa ya ci tura. Dukanin aikinsa ya ruguje gaba ɗaya... ” (Ɗan littafin Deedat mai suna Crucifixion or Cruci-fiction? Wato Gicciye ko Almara? shafi na 10). Dole wannan ya zama abin banmamaki ga dukan Kirista duk da Musulmi a ji wannan muhawara ta faru bayan wajen shekara dubu biyu bayan zaman Yesu a duniya, a ce wai Yesu ya shirya juyin mulki irin na siyasa. A kan wannan al’amari ne Yesu ya yi ta kaucewa, yana ƙin shigar da kansa cikin harkokin siyasa na zamaninsa. Ya ƙi yarda a yi muhawara da shi a kan ko daidai ne a biya haraji ga mai mulkin danniya na Roma (Luka 20:19-26), ya fice daga cikin taron mutane lokacin da suka nemi naɗa shi ya zama shugabansu na siyasa (Yahaya 6:15), a kai – a kai kuma ya sha koya wa almajirinsa kada su zama kamar waɗannan masu neman ikon siyasa (Luka 22:25-27).

Yahudawa sun yi kowane abu don su rinjayi Bilatus, gwamna Barome cewa Yesu yana goyon bayan tayarwa gāba da Kaisar(Luka 23:2), ko Deedat kansa ma, ya yi suɓul da baki, ya zamar masa dole ya yarda cewa, wannan zargin da aka yi wa Yesu “ƙarya ne tsagwaronta” (shafi na 27). Ta haka ne yake da muhimmanci ƙwarai a ga cewa Deedat ma ya san cewa Yesu “bai yi kama da masu zaƙuwa ba, masu tsananin ƙudurin siyasa, ɗan ta’adda, Yesu bai yi kama da wannan ba!” (shafi na 27, cikin ɗan littafinsa) ya kuma ci gaba da faɗa a cikin ɗan littafinsa:

Nasa mulkin ruhaniya ne, mai mulki da zai ceci al’ummarsa daga zunubi da sauran takalidai (Deedat, Crucifixion or Cruci-fiction?, shafi na 27).

Saboda haka, abin mamaki duka shi ne, a ga cewa Deedat yana ƙoƙarin tabbatarwa a cikin ɗan littafinsa wai lalle Yesu ya shirya maƙarƙashiyar kifar da mulkin siyasa, don a shafi na 27 ya bankaɗo ainihin gaskiyar! Inda ya yarda cewa Yesu bai yi maƙarƙashiyar kawo juyin juya hali ba.

Wannan ra’ayi a cikin kowane al’amari abin ba’a ne kamar yadda za a gani daga ƙididdigar wasu daga cikin gardandamin Deedat na goyan bayan wannan ra’ayi, za mu yi la’akari a taƙaice a kan waɗannan don mu tabbatar da batun. Za mu fara da yadda ya ɗauki maganar da Yesu ya yi gab da lokacin kama shi, inda ya faɗa wa almajiransa cewa, wanda ba shi da takobi ya sayar da rigarsa ya sayi takobi (Luka 22:36). Ya fassara wannan da nufin cewa Yesu yana kiran almajiransa su yi ɗamara su yi shirin shiga yaƙin jihadi, ko ma me ke nan. Abin da ya biyo bayan wannan batu na Yesu yana da babban muhimmanci. Almajiransa suka ce:

Ya Ubangiji, ai, ga takuba biyu”. Ya ce musu, “Ya isa” (Luka 22:38).

Takobi biyu ba su “isa” a tada juyin juya hali ba har a ce Yesu yana nufin “sun isa don wannan shiri”, Yesu yana nufin cewa wannan rashin fahimtarku ne ga abin da nake faɗi. Amma duk da haka, da yake Deedat yana so ya rinjayi hankalin masu karatun rubutunsa a kan lalle Yesu ya yi shirin juyin mulki, sai ya dāge da jiɓin goshi da cewa, lalle takobi biyun nan sun isa ya ture mulkin Yahudanci da kuma mulkin danniya na Romawa! Kamar yadda muka saba gani, gardamar Deedat da wuya ta yi rinjaye. Da ya ga ba abin yi sai ya ƙara da cewa, almajiran Yesu sun “ɗauki kulake da duwatsu” (shafi na 13 cikin ɗan littafin Deedat) sai kace wasu garken ’yan iska. Babu ko alamar da ta goyi bayan wannan a cikin Littafi Mai Tsarki. Deedat ne ya ƙago wannan fassara mara tushe don a ɗauka cewa Yesu yana nufin cewa takobin biyu sun isa a yi babban tawaye da su! A wani wuri kuma Deedat ya ce:

A koyaushe, almajiran Yesu ba sukan fahimce shi ba (Ɗan littafin Deedat, Crucifixion or Cruci-fiction? shafi na 23).

Kalman nan “koyaushe” an buga ta da baƙi sosai duk sa’ad da aka ɗauko ta daga ɗan littafin nasa. Deedat ba da saninsa ba ya rikitar da kansa, domin idan Yesu yana niyyar sa almajiransa su yi ɗamarar yaƙi kamar yadda Deedat ya ke iƙirari, to, almajiran Yesu sun fahimci Yesu ke nan sosai da sosai ainihin yadda su suka fahimci maganarsa ke nan. Amma kuma Deedat ya yi daidai da ya ce loto-loto almajiran ba sukan fahimci Yesu ba a nan kamar sauran lokatai. Muna bukatar mu yi la’akari da abin da Yesu ya ce bayan cewa su sayi takuba , wannan zai sa mu fahimci al’amarin nan. Ya ce:

“Ina dai gaya muku, lalle ne a cika wannan Nassi a kaina cewa ‘An lasafta shi a cikin masu laifi, Gama abin da aka faɗa a kaina, tabbatarsa ta zo” (Luka 22:37).

Nassin da ya faɗa daga Ishaya 53 ne, surar annabcin da aka rubuta wajen shekara ɗari bakwai tun kafin abin ya faru, Ishaya ya hango wahalar da Masiha zai sha a madadin mutanensa, cikin wahalar yake yin hadayar kansa domin zunubi (Ishaya 53:10). Ga dukanin ayar da Yesu ya ambato , tana cewa:

Saboda haka zan ba shi matsayi mai girma, matsayi a cikin manyan mutane masu iko. Da yardarsa ya ba da ransa ya ɗauki rabo da masu laifi. Ya maye gurbin masu zunubi da yawa, ya kuwa sha hukuncin da ya cancanci masu zunubi. Ya yi roƙo dominsu (Ishaya 53:12).

A sarari Yesu ya faɗa cewa, annabcin yana gab da cika a kansa, ma’anar annabcin kuma a fayyace ta ke. Zai “tsiyaye ransa har ga mutuwa” kwana guda bayan gicciyen “an lasafta shi tare da masu laifi” (tabbatacce an gicciye shi a tsakanin ɓarayi biyu-Luka 23:33). Duk da haka “Ya ɗauki zunubin mutanne masu yawa” da ya yi kafara domin zunuban duniya a kan gicciye, zai kuma “yi roƙo domin masu zunubi” (Ya yi addu’a daga kan gicciye domin masu kisansa – Luka 23:34). Saboda aikin alherin nan Allah zai ba shi “damar wahalar da ya sha ba ta banza ba ce” (Ishaya 53:11) zai kuma ba shi “ganimar” nasararsa – fayyataccen dukan abin da Yesu ya faɗa game da batun nan domin batun ya rikitar da manufar Deedat, domin a sarari yake cewa Yesu yana sane da gicciyensa da ke tafe, da mutuwarsa, da kuma tashinsa daga matattu a matsayin Mai Ceton duniya, kuma ba ya shirin yin juyin mulki sai ka ce mai nemar wa kansa muƙami ko ta halin ƙaƙa. Al’amuran da za su faru ba da daɗewa ba za su ɗauke Yesu daga almajiransa, gargaɗinsa gare su na su sayi jaka da takuba wani salon magana ne na shawartar su da su yi shiri su nemi abin masarufi don kansu da zarar ya tafi.

Gardamar Deedat cikin tsaikon batunsa ya dāge ne a kan shigar Yesu cikin Urushalima mako guda kafin a kashe shi, lokacin da mabiyansa suka ɗaukaka shi lokacin da suka yi tattaki tare da shi da ya ke shiga cikin Urushalima. Deedat ya mori ainihin kalmomin nan da ya ce:

Tattakin shiga Urushalima bai yi nasara ba (Ɗan littafin Deedat, Crucifixion or Cruci-fiction?, shafi na 21).

A ƙarƙashin kan maganan mai cewa. Tattakin shiga Urushalima, Deedat ya yarda cewa lalle Yesu ya yi hawa zuwa cikin birni a kan jaki. Ba shakka wannan ba mahayin juyin mulki ba ne ko kaɗan! A sarari Yesu ya zaɓi wannan hanya domin jakuna alamar salama ce, da kuma sauƙin sarrafawa, ya so kuma ya nuna wa Urushalima cewa zuwa ne cikin salama yana kuma cika wannan alkawari na Allah da ke rubuce cikin wani annabci ɗaruruwan shekaru da suka gabata:

Ki yi murna ƙwarai, ya Sihiyona! Ta da murya ya Urushalima! Ga sarkinki yana zuwa wurinki, shi mai adalci ne mai nasara, shi kuma mai tawali’u ne, yana bisa jaki, a kan aholaki (Zakariya 9:9).

Ya zo cikin tawali’u da salama a kan dabba mai nuna alamar manufarsa. “Zai umarta salama ga al’ummomi, haka annabcin ya ci gaba (Zakariya 9:10). Babban rashin hankali ne a ce Yesu yana shugabantar “zangazanga” ko yana kutta tashin hankali “kokawa da makami” kamar yadda mutane suke cewa a yau.

Cikin dabara, Deedat ya kauce wa gaskiyar cewa, ana cikin kiciniyar kama Yesu, sai almajiransa suka ce, “Ya Ubangiji, mu yi sara da takuba ne?” (Luka 22: 49). Ɗayansu ya fille kunnen bawan babban firist, amma nan da nan Yesu ya tsauta masa, ya kuma warkar da wanda aka yi wa raunin. Dukan abin shaida yana nuna cewa ba ya shirin aiwatar da juyin mulki ko kaɗan, amma yana shirin babban al’amari na ƙauna da zai nuna wa duniya cikin shan azabar da ke jiransa da mutuwa a kan gicciye sabili da zunuban mutane. Mun karanto wani alkwari da Allah ya yi:

“ ...zan kawar da laifin al’umman nan rana ɗaya” (Zakariya 3:9).

Ranar kuwa ta zo, Yesu yana shiryar da kansa domin ya “samo mana madawwamiyar fansa” (Ibraniyawa 9:12) ta wurin ɗauke zunuban duniya a wannan Juma’a mai banrazana wadda saboda haka ne ya zo.

Ra’ayin nan mai cewa ya yi shirin juyin mulki da bai yi nasara ba babban lahani ne ga mutuncinsa mai alheri, kuma mugun ƙazafi ne wanda ba a ko zaton samunsa daga mutumin da bisa ga zato ya gaskata cewa Yesu yana daga cikin mutane mafiya girma da aka taɓa yi a duniya.

Deedat bai taɓa samun wata horarwa a kan aikin mayaƙa ba, ya kuma fallasa jahilcinsa a kan wannan a shafi na 14 na ɗan littafinsa in da ya ke cewa, Yesu ya tafi da Bitrus, da Yakubu da kuma Yahaya zuwa Lambun Gatsemani don su zama matsara na ciki, saura takwas kuma suna tsaron ƙofar shiga lambun. Gabagaɗi ya ke cewa ya yi kyakkyawan shiri irin wanda zai “ba da ƙarin daraja da duk jami’in mayaƙa da ya fito daga ‘Sandhurst’, – wata shaharriyar makarantar aikin soja da ke a England” (shafi na 14). Wani tsohon soja daga sojan Birtaniya ya taɓa yin sharfi a kan wannan iƙirari, ya ce mini bai taɓa jin an taɓa koyar da irin waɗannan dabaru ba a Sandhurst! Deedat ya faɗi magana a kan almajiran Yesu da ya bar su a ƙofar lambun:

Ya kakkafa su a bakin ƙofar lambun, sun sha ɗamarar yaƙi sosai da sosai, ko da ko menene zai faru (Ɗan littafin Deedat, Crucifixion or Cruci-fiction? shafi na 14).

Ya ci gaba da cewa, Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yakubu da kuma Yahaya, “waɗannan ’yan ta kife (dakarun yaƙi ’yan Irish na zamaninsu)” (shafi na 14), don ya shirya ƙaƙƙarfan tsaro na ciki. Wannan gardama ba ta da kan gado. Bitrus da Yakubu da Yahaya masunta ne masu son zaman salama daga Galili (Yesu yana da Zeloti guda ɗaya kaɗai a cikin almajiransa, ba daga cikin su ukun nan yake ba - Luka 6:15), su ne kuma mafiya kurkusa da shi a cikin dukan lokacin aikinsa a nan duniya. Lokacin sāke kamanninsa a kan dutse, waɗannan ukun ne dai suke tare da shi, sauran kuma suna ta fama da taron mutane a nan ƙasa (Matiyu 17:1,14-16). Haka kuma lokacin da ya ta da ɗiyar Yiyirus daga matattu, ya shiga tare da ukun nan cikin gidan (Luka 8:51). Sau da dama yakan ɗauki almajiran nan su uku, Bitrus, Yakubu, da Yahaya, su ya fi amincewa da su a wasu al’amura na musamman, wannan kuma ya nuna a sarari cewa ko kaɗan Yesu ba ya yin wani shiri na tsaron kansa a Lambun Gatsemani lokacin da ya shiga tare da su daga can cikin lambun. Kuma yakan biɗi zumunci na ƙud da ƙud a muhimman lokatai daga almajiransa mafiya kurkusa da shi. Dukan wannan yana nuna cewa wannan ma ba sai an faɗa ba, lalle Yesu bai yi wani shirin juyin mulki ba.

2. SIFFAR YESU A CIKIN ƊAN LITTAFIN DEEDAT

(Baƙin fentin da Deedat ya shafa wa Yesu a cikin ɗan littafinsa)

Ɗaya daga cikin abubuwa mafiya girma a game da ɗan littafin Deedat shi ne ƙazafin da ya gabatar a kan Yesu Almasihu, ai, wannan baƙon abu kuwa, da shike ya kamata Musulmi su girmama Yesu a matsayinsa na Masihi, wanda kuma yake ɗaya daga cikin annabawan Allah mafiya girma. Batu ɗaya ko biyu daga littafinsa masu ta da hankali ne ƙwarai ga Kirista, da kuma Musulmi na gaske waɗanda suka koyi girmama Yesu a shi mutum ne mai martaba da mutunci dole ne su ji zafin wannan ƙwarai da gaske. Ba mamaki yadda wani lokaci a ka nuna “ƙin” ɗan littafin Deedat, wato Darakatan maɗaba’a Afrika ta Kudu ya yi wannan (a farkon 1985). A wani wuri ya ce:

Yesu ya ƙi jin gargaɗin Farisiyawa cewa ya kwaɓi almajirinsa saboda suna wuce gona da iri (Luka 19:39). Ya yi shayin da ba shike nan ba. Yanzu dole ya sami sakamakon kāsawarsa. (Ɗan littafin Deedat, Crucifixion or Cruci-fiction?, shafi na 10).

A wani shafi ya ce, “Yesu ya yi kuskuren yin shayi” (shafi na 19) inda ya tsammaci zai iya dogara ga almajiransa don su kāre shi, kuma zai ji wa Yahudawa. Kamar waɗannan zarge-zarge ba su isa ba, sai ya ƙara da ɓata Yesu gaba da baya, ya cika mudunsa na ɓatanci inda ya ke cewa:

Ana iya yin barataccen iƙirari cewa Yesu Almasihu (Pbuh) “Shi ne mafi rashin sa’a daga cikin manzannin Allah” Ɗan littafin Deedat, Crucifixion or Cruci-fiction?, shafi na 23).

Mun tabbata, ko Musulmi za su ga irin wannan batu muguwar tsokanar tada hankali ce ƙwarai da gaske. Kirista za su ɗauki wannan sāɓo ne muraran. Duk da haka, ba son mu ba ne mu bayyana jin haushi, amma mu nuna yadda wawancin iƙiraran Deedat suke ne.

Ba sai an yi doguwar ƙididdiga ba na sa’o’in ƙarshe na rayuwar Yesu gab da gicciyensa a ga cewa ko kaɗan babu ko ƙamshin gaskiya a game da iƙirarin cewa Yesu ya yi kuskuren shayi. Abu guda da ya nuna haka shi ne a darensa na ƙarshe ya wayar da almajiransa a kan dukan abin da zai faru da shi, kuma da yardar ransa zai sha wannan duka.

Ya san cewa Yahuza Iskariyoti zai bashe shi (Markus 14:18, - Ya san da wannan tun tuni, za a ga wannan a cikin Yahaya 6:64), Bitrus zai yi musun saninsa har sau uku (Matiyu 26:34). Ya kuma yi annabcin cewa za a kama shi, almajiran kuma za su gudu su bar shi (Markus 14:27). Ko kaɗan ba za a iya ganin ko a kan me iƙirarin Deedat ya dogara ba cewa, Yesu ya sa zuciya almajiransa za su yi yaƙi domin sa, har da za a ce ya yi “kuskuren shayinsa”. Domin ayoyin nan sun nuna a fili cewa Yesu ya yi lissafi zahiri ko me zai faru da shi, almajiransa duka sun yi abin da ya ce za su yi.

Ya kuma sha nanata musu a daren nan mai banrazana cewa yana gab da rabuwa da su (Yahaya 13:33; 14:3,28; 16:5), kada kuma su karai, saboda shan wuyarsa zai zama duka bisa abin da aka yi annabci ne cikin annabce- annabcen annabawa na dā (Luka 22:22). Da Yahudawa suka zo don su kama shi, ko kusa babu batun kāre shi, shi da kansa ya tafi ya miƙa kansa gare su. Muna karanta cewa:

Yesu kuwa da ya san duk abin da zai same shi, ya yiwo gaba, ya ce musu, “Wa ku ke nema?” Suka amsa masa suka ce, “Yesu Banazare,” Yesu ya ce musu, “Ni ne” Yahuza kuwa da ya bashe shi na tsaye tare da su (Yahaya 18:4,5).

Yesu ya yiwo gaba, yana sane da dukan abin da zai auku gare shi. Ya san cewa ana gab da gicciye shi, amma zai tashi a kan rana ta uku, kamar yadda ya sha faɗa sau da dama a sarari (Matiyu 17:22, 23; 20:19; Luka 9:22; 18:31-33). A gaskiya, babu bukatar fito-na-fito da Yahudawa ko kaɗan. Idan da Yesu ya so kauce wa kama shi, da kawai sai ya bar Urushalima ne. Amma a maimakon haka, sai ya tafi ainihin wurin da ya san cewa Yahuza Iskariyoti zai iya kai Yahudawa don su same shi a wurin (Yahaya 18:2), da suka zo kuwa, da yardar ransa ya miƙa kansa gare su. Bugu da ƙari, da wuya ya bukaci ƙoƙarin almajiran nan sha ɗaya don su kāre shi, domin ya faɗa a fili cewa, idan yana so, ai, da ya kira runduna goma sha biyu na mala’iku su zo don su taimake shi (Matiyu 26:53). Mala’ika guda ɗaya kaɗai ya isa ya halakar da dukan birane da mayaƙa (2Sama’ila 24:16; 2Sarakuna 19:35) balle fa a ce runduna goma sha biyu na mala’iku su zo su kāre shi, ai, da kowa ya ji jiki.

Ko kaɗan babu wani abin kamawa a cikin iƙirarin Deedat mai cewa wai Yesu yana shirya maƙarƙashiya amma abin ya ci tura don bai auna daidai ba. A akasin haka, sai ga shi ya san ainihin abin da zai faru da shi tun da fari. Ko kusa babu “cin tura” a ciki, shi ne mutumin da ya fi kowa nasara da ya taɓa zama a duniya – mutumin kuma da shi kaɗai ne ya taɓa ta da kansa daga cikin matattu zuwa rai madawwami da ɗaukaka. Muhammadu ya kāsa yin nasara da mutuwa. Mutuwa ta gama da shi a cikin Madina a 632A.D, ta kuma riƙe shi har ya zuwa yau. Saboda haka, Yesu ya yi nasara a duk inda Muhammadu ya kāsa. Shi ne “Mai cetonmu, Yesu Almasihu, wanda ya share mutuwa, ya kawo rai da rashin mutuwa zuwa haske ta wurin bishara” (2Tim. 1:10). Ya yi nasara da mutuwa, ya kuma hau zuwa sama inda yake zaune yana kuma mulki. Wulakancin Deedat ya yi yawa da ya ce wai Yesu ne mutum “mafi rashin sa’a” daga dukan manzannin Allah. Gaskiyar ita ce, Yesu ne mutum mafi girma da ya taɓa zama a duniya.

Ya zama jazaman, zai kuma ci gaba da zama haka, cewa ɗan littafin Deedat ba kome ba ne in banda daddagula Maganar Allah. Ya hana a ga ma’anar matanai (ayoyi) abin da ya ke ji wannan ne zai iya cin ma manufarsa, a sawwaƙe yake danne saura masu sèkar ra’ayoyinsa gaba ɗaya.

3. KO YESU YA K ĀRE KANSA A LOKACIN SHARI’ARSA?

A shafi na 28 na ɗan littafin Deedat ya yi iƙiƙarin ƙasƙantar da labarin gicciyen Yesu a cikin Bishara ta wurin ƙalubalantar annabcin da ke cikin Ishaya 53:7, inda a ka yi annabcin cewa bai buɗe bakinsa don ya kāre kansa ba, lokacin da ake yi masa shari’a amma aka ja shi zuwa inda za a gicciye shi, yana shiru “kamar tunkiya a wurin masu sausayarta bai ce uffan ba”. A fili yake daga annabcin nan ba ana nufin cewa Yesu ba zai ko ce ƙala ba idan an kama shi, amma abin da ake nufi shi ne, ba zai buɗe baki ya yi magana da niyyar kāre kansa a cikin shari’ar da ake yi masa ba. Dukan gardamar Deedat ta dogara ne a kan wasu maganganu da Yesu ya yi, da su ne yake ƙoƙarin nuna wa duniya cewa Yesu ya yi maganar kāre kansa a gaban masu saransa.

Ya yi ƙoƙarin yi wa Yesu ba’a ta wurin yin tambaya wai ko Yesu ya yi magana “da bakinsa a rufe ne” lokacin da ya faɗa wa Bilatus cewa, mulkinsa ba na wannan duniya ba ne (Yahaya 18:36), lokacin da ya kira ɗaya daga jami’an Babban firist ya shaida idan ya faɗi wani abin da ba daidai ba (Yahaya 18:23), da kuma lokacin da ya yi addu’a ga Allah cewa idan zai yiwu, a kawar da ƙoƙan shan wahalan nan da yake fuskanta daga gare shi (Matiyu 26:39).

Akwai bukatar a nuna cewa, babu ko ɗaya daga cikin maganganun nan da Yesu ya yi a lokacin da ake tuhumarsa a gaban Sanhedrin a cikin gidan Kayafa babban firist, ko a gaban gwamnan Romawa Bilatus Babunte. Magana ta fari ya yi da Bilatus ne lokacin da ya ke tattaunawa da Bilatus a kaɗaice a cikin farfajiya; magana ta biyu kuma a lokacin da Yesu yake a gaban Hanana, surukin Kayafa wanda ba shi nan lokacin tuhumar Sanhedrin kamar yadda Deedat ya ke ɗauka (shafi na 28) – an yi shari’ar ne kaɗai bayan wannan al’amarin a cikin gidan Kayafa kamar yadda Bishara ta nuna a sarari (Yahaya 18:24; Matiyu 26:57); magana ta uku kuwa ya yi ta ne a cikin lambun Gatsemani kafin a kama Yesu. Abin shaidar da Deedat ya kawo ko kaɗan bai shiga ba, bai kuma iya tabbatar da kome ba ko kaɗan. Abin da ya dame mu shi ne, ko Yesu ya kāre kansa a gaban Sanhedrin a cikin gidan Kayafa ko a lokacin da ake tuhumarsa a bainar jama’a a gaban Bilatus. Bai ba mu mamaki ba a ga cewa Deedat ya ƙi ganin abin da Bisharu suka, faɗa a sarari a game da tuhuma biyu a hukumance. Bayan an saurari shaidu gāba da Yesu a gaban Sanhedrin, sai Kayafa ya matsa Yesu ya amsa wa masu saransa, abin da ya gudana kuwa muhimmi ne ƙwarai:

Sai babban firist ya miƙe ya ce “Ba ka da wata amsa? Shaidar da mutanen nan ke yi a kanka fa?” Amma Yesu na shiru. Sai babban firist ya ce masa, “Na gama ka da Allah Rayayye faɗa mana ko kai ne Almasihu, Ɗan Allah” (Matt. 26:62,63).

Maimakon Yesu ya kāre kansa, sai nan take ya shaida, cikin amsa tambaya ta gaba, cewa ba shaka shi Ɗan Allah ne - shaidar da ta tunzura Sanhadrin su yanke masa hukuncin kisa.

Muhimmin batu shi ne, amsa wa masu saransa, mun karanta a sarari cewa Yesu bai ce uffan ba. Haka ma muka karanta, lokacin da Bilatus ya yi masa irin tambayan nan, bai ce ƙala ba. Bai buɗe bakinsa ba don ya faɗi abin da zai kāre kansa.

Amma da manyan firistoci da shugabanni suka kai ƙararrakinsa bai ce kome ba. Sai Bilatus ya ce masa, “Ba ka ji yawan maganganun da suke ba da shaida a kanka ba?” Amma bai ba shi wata amsa, ko da ta kalma ɗaya ba, har mai mulki ya yi mamaki ƙwarai (Matiyu 27:12-14).

Deedat cikin dabara ya rufe abubuwan nan da suka faru masu faɗa mana a sarari cewa Yesu bai ce ƙala ba a gaban Sanhedrin lokacin da masu shaidar zur suke saran sa, bai kuma amsa da kome ba – ko da ta kalma ɗaya a kan zargin da ake yi masa - lokacin da ake ƙararsa a gaban Bilatus. Cikin al’adar da ya saba, Deedat ya danne abubuwan shaida da suke da dangantaka ta kaitsaye ga batun da ake yi, a maimakon haka sai ya jawo muhawararsa daga wasu sassan da ko kaɗan ba su dace da al’amuran da ake magana a kai ba.

Wani abin sha’awa kuma shi ne, yadda aka ga abin ya faru daidai a lokacin da Yesu ya bayyana a gaban Hirudus, sarkin Yahudawa, kafin ya aika shi baya zuwa ga Bilatus.

Da Hiradus ya ga Yesu, ya yi murna ƙwarai, saboda tun da daɗewa yake son ganinsa, don ya riga ya ji labarinsa yana kuma fata ya ga wata mu’ujiza da Yesu zai yi. Sai ya yi ta masa tambayoyi da yawa amma bai amsa masa da kome ba. Manyan firistoci da malaman Attaura na nan tsaitsaye, suna tsananta kai ƙararrakinsa ainun (Luka 23:8-10).

Har yanzu dai, lokacin da ake ƙarar Yesu bai ba da amsa ba. A kowane karon da ake yi wa Yesu ainihin shari’a a gaban Sanhedrin, da Hirudus ko Bilatus, ko kaɗan bai ce kome ba don ya kāre kansa, kuma ta haka annabcin Ishaya ya cika cewa, faufau bai buɗe bakinsa don ya yi maganar kāre kansa ba. Ba ko ɗaya daga cikin maganganun da Deedat ya kwaso, waɗanda Yesu ya yi a lokacin da ake yi masa ainihin shari’a, don haka dukan gardamarsa sun fāɗi ƙasa warwas.

4. RA’AYIN CEWA YESU BAI MUTU A KAN GICCIYE BA

Ba za mu taɓa daina mamaki a kan dalilin da ya sa Ahmed Deedat ya ci gaba da haɓaka ra’ayinsa ba mai cewa, lalle an gicciye Yesu, amma ya sauko daga kan gicciye da rai. Akwai abin la’akari guda biyu da suke ba mu mamaki. A gefe guda kuma, wannan ra’ayi sai Ahmadiya kaɗai masu ratsewannan na Musulmi suke riƙe da wannan ra’ayi, su da dukan Kirista da Musulmi na gaskiya suka musunce su. A gefe guda kuma, an sha sèkar wannan ra’ayi, amma Deedat ya ci gaba da ciyar da shi gaba, ba shi kuma iya amsa dukan muhawarar da aka samar gāba da wannan.

Alal misali, a shafi na 36 na sabon ɗan littafinsa, ya yi iƙirarin cewa, lokacin da babban hafsa ya ke kallon Yesu a kan gicciye “ya ga ya riga ya mutu” (Yahaya 19:33), wannan yana nufin “zato ya yi” cewa Yesu ya mutu, babu wani abin da zai tabbatar da mutuwar. Cikin amsa ga ɗan littafinsa na fari mai suna ko an Gicciye Yesu Kuwa? (Was Christ Crucified?), ya nuna a sarari cewa hafsan, shaidarsa ce mafi duka mai nuna cewa lalle Yesu ya mutu. Dole ne hafsan ya shaida abin da yake tabbas a gaban gwamnan Romawa cewa mutumin da aka gicciye ya mutu, idan kuwa rahotonsa bai faɗi gaskiya ba, to a bakin ransa. Muna karanta cewa:

Bilatus ya yi mamaki ko ya mutu. Sai ya kira jarumin ɗin, ya tambaye shi ko Yesu ya jima da mutuwa. Da ya san haka daga bakin jarumin ɗin sai ya bai wa Yusufu jikin (Markus 15:44,45).

Gwamnan Romawa wato Bilatus ya san cewa, muddin hafsan nan wato jarumin nan ya tabbatar da mutuwar, to, shi ya yarda, domin a wancen zamani duk sojan da ya bari wani ɗaurare ya tsere to, a bakin ran wannan sojan, kashe shi za a yi.

Lokacin da Manzo Bitrus ya tsere daga kurkuku (ta hannun mala’iku), nan take aka hukunta mutuwa a kan matsaransa, aka karkashe su (Ayyukan Manzanni 12:19). Haka kuma wani mai tsaron kurkuku da ya zaci cewa, su Bulus da Sila sun tsere daga kurkuku, “sai ya zaro takabinsa yana so ya kashe kansa” (Ayyukan Manzanni 16:27). Sai da ya ga ashe ba su tsere ba. Ya gwammace ya kashe kansa da kansa, da a kashe shi a hukumance. Hukuncin bari ɗaurarre ya tsere mutuwa ne – me jarumin yake sa zuciya zai same shi, har idan mutumin da aka zartas da hukuncin kisa a kansa ya tsere saboda ya yi sakaci da aikinsa? Babu wani, sai dai jarumin nan ne kaɗai tattibin mashaidi ga mutuwar Yesu a kan gicciye!

Ko da shike an ƙarfafa, an tabbatar da rashin tasirin Deedat cikin gardamarsa mai cewa, jarumin “ya ga kamar Yesu ya riga ya mutu ne”, an shaida lalle Yesu ya mutu, duk da haka, Deedat ya ci gaba da haɓaka tsohuwar gardamarsa. Loto-loto yakan ƙi da gangar, ba ya duba ƙaƙƙarfar shaida gāba da ra’ayinsa. Ba wani kataɓus; maimaita tsofaffin gardandaminsa na dā kaɗai ya ke iya yi duk da cewa an yi nasara da shi a kan wannan batu.

Ba cikakken duban da jarumi ya yi kaɗai ba, amma ɗaya daga cikin sojojin ya soki kwiɓin Yesu da māshi - domin dai ya tabbatar Yesu ya mutu. Ɗaya daga cikin dabarun Romawa na kashe mutane ita ce “su zurɗe su da takobi”. Wannan ne ainihin abin da sojan nan ya yi wa Yesu, wannan kuwa ko da lafiyayyen mutum ne aka yi wa haka, nan zai mutu. Amma duk da haka, Deedat, cewa ya ke wannan hanya ce da aka bi “don a kuɓutar” da Yesu a taimake shi ya farfaɗo ta wurin tuƙa hanyar jininsa don “jinin ya ci gaba da gudana cikin jikinsa” (shafi na 39). Ba shakka, ko kiɗimammun masu karatunsa ma ba za su gaskata wannan rashin hankali ba – a ce dukan mutuwa da ya sha, ga sèka – da māshi duk cikin jikinsa, har a ce zai sami wani taimako har ya farfaɗo! Lokacin da mutum ya zaɓi zama cikin irin wannan rashin kangado, a sarari yake cewa gardamarsa ba ta da wani tasiri ko kaɗan.

Wani soki – burutsun da ke gaban mai karatu a cikin wasu ’yan shafofi na ɗan littafin Deedat shi ne inda ya yi magana a game da lokacin da Maryamu Magadaliya ta zo don ta shafe gawar Yesu da mai ba da daɗewa ba bayan gicciyensa:

A cikin kwanakin nan uku, jikin yana ruɓewa daga ciki – abubuwan da ke riƙe da jiki duk sun saki. Idan wani ya goga, ko murza irin wannan ruɓaɓɓen jiki, zai wargaje. (Ɗan littafin Deedat mai suna, Crucifixion or Cruci-fiction? shafi na 44).

Wannan ma wani rashin tunani ne a kimiyyance. Yesu ya mutu wajen ƙarshen la’asar ran Juma’a, yini da dare biyu ne kaɗai, kamar yadda Deedat ya yarda a cikin shafin littafinsa, cewa Maryamu Magadaliya ta zo don ta shafe jikin Yesu da mai. Babu jikin da zai ruɓe har ya “wargaje” cikin wannan ɗan lokaci. Cikin haruffai masu kauri Deedat ya ƙara da cewa Maryamu ta zo ita kaɗai don ta taimaki Yesu ya farfaɗo, amma cikin Matiyu 28:1 da kuma Luka 24:10 mun ga cewa tana tare da a ƙalla wasu mata biyu Yuwana da Maryamu mahaifiyar Yakubu, kuma domin su kawo kayan ƙanshin da suka shirya bisa ga al’adar binnewa ta Yahudawa. Gardamar Deedat ba ta da wani tasiri ko kaɗan a nan. Gicciye da tashin Yesu daga matattu gaskiya ne na tarihi – ra’ayinsa ne almara mai cewa Yesu ya farfaɗo a kan gicciye.

Ba mu nufin mu shiga batun kawar da dutse, ko Yesu ya yi ƙoƙarin nuna wa almajiransa cewa bai mutu ba tukuna, ko kuma batun Alamar Yunusa (Yunana). Ko da shike dukan waɗannan batutuwa mun taɓa su sosai cikin ɗan littafin Deedat, mun ba da amsa cikakkiya a cikin ɗan littafi na biyu cikin wannan jerin mai suna A Gaskiya Menene Alamar Yunusa? wanda masu karatu za su samu daga Zumuntarmu ba da biya ba (Kyauta).

Wata gardamar da Deedat ya sāke maimaita ta, an kuma sha sèkar ta ita ce, abin da yake cewa Yesu ba ya so ya mutu. Sukar da aka yi wa ɗan littafinsa na baya, a kan batun gicciye, na riga na nuna a sarari cewa Yesu ya damu kaɗai saboda Uba ya yashe shi, cikin ɗumbin zunubai da muguntar zunubabbun mutane. Wannan tsoro ya kai matuƙa a cikin Lambu a daren nan kafin a gicciye Yesu, cikin sa’ar da ta zo da za a ba she shi ga mutane masu zunubi (Matiyu 26:45). Ya damu da zai mutu, wannan tsoro ya kai matuƙa ne kaɗai da ya fuskanci gicciyewa kashegari, amma bayan mala’ika ya ƙarfafa shi a daren da ya wuce (Luka 22:43), sai ya fuskanci mutuwa gabagaɗi, wato banda tsoro. Ya yi tafiya a natse kamar yadda muke gani. Ya bi ta rariya a natse kamar yadda muka gani. Ya bi ta rariyar da lalle ya sani ta nufi zuwa inda za a gicciye shi ya mutu.

A natse ya sha dukan raunuka kashegari, ba tare da ya nuna alamar jin tsoro ko ƙin yarda a gicciye shi ba. Da ake fitar da shi daga cikin Urushalima ya nuna damuwa a game da matan birnin da ’ya’yansu a maimakon ya damu da kansa (Luka 23:28). Ba shakka, a maimakon a ce ya damu yana tsoron zai mutu, sai muka gano a cikin labarun Bishara cewa ya kafa fuskarsa ga gicciye, bai riƙe su ba amma ya ci gaba, ya ƙudurta ya fanshi mutane daga zunubansu.

Har yanzu, wata gardama ta Deedat haka ta zo a wofi. Mun ga ya shiga mummunar ruɗewa a wani wuri inda ya ce:

Allah Mai Iko Dukka ba zai taɓa yarda a kashe “shafaffensa” na gaskiya ba (Almasihu) – (Maimaitawar Shari’a 18:20.) (Ɗan littafin Deedat, Crucifixion or Cruci-fiction?, shafi na 15).

Batun cewa “Allah ba zai taɓa yarda a kashe shafaffensa ba, ai, akwai faɗi na musamman a cikin annabcin babban annabi” (Daniyel 9:26). A gaskiya ma ta daɗa morar ainihin kalman nan mashiah a cikin matanin nan cewa Yahudawa za su kira Mai Ceton Duniya da suke jira “Masihi”, duk da haka daidai ne cikin matanin nan da muka karanta cewa wannan ainihin Masihin ne za a datse (kashe) – fayyataccen gicciye da mutuwar Yesu.

Musamman muna da sha’awar mu gano abin da Deedat ya ɗauko daga cikin Maimaitawar Sahria’a 18:20 a kan zuwan “Shafaffe”, “Almasihu”, Masihi wato Yesu. A cikin ɗan littafin Deedat mai suna a turance “What the Bible says about Muhammed” ya yi matuƙar aiki don ya tabbatar cewa annabci a kan annabin da ke zuwa a cikin Maimatawar Shari’a 18 a kan Muhammadu ne, ko da shike mun ƙara tabbatarwa cewa duban hanyar zuwan Masihi, Yesu ne. (Kur’ani ma yana tabbatar da cewa Masihi kaɗai, shi kaɗai ne “shafaffe”, al-Masih, Yesu ne – Suratu Al Imrana 3:45). Saboda haka, abu mafi muhimmanci ne mu gane cewa Deedat yakan yi suɓul da baka lokaci - lokaci ya yarda da gaskiyar, kamar yadda aka ɗauka daga cikin ɗan littafinsa yadda annabcin a kan Yesu, Masihi ne, ba a kan Muhammadu ba.

Zai yiwu, gardamar Deedat mafi rashin kangado duka ita ce maganar da ya yi cewa Allah da ya ji addu’ar Yesu a cikin lambun Gatsamani, ya aiko da mala’ikansa don ya ƙarfafa shi “da begen cewa Allah zai cece shi” (shafi na 35). Ya ci gaba da gardama cewa Allah ne ya sa cikin tunanin sojojin nan musamman su ji a ransu cewa Yesu ya riga ya mutu a kan gicciye, ya kuma ce wannan, “Wani mataki ne cikin shirin Allah na kuɓutarwa” (shafi na 36). Ga yadda gardamar tasa take, wai bayan shan bulala, da duka, ga ƙayoyi sun huda kansa, aka kuma tilasta shi ya ɗauko gicciyensa, da aka gicciye shi ya suma domin ya galabaita gab da mutuwa bayan shan haƙuba wadda ba ta misaltuwa, ya kuma ji azabar zurɗawa – da takobi, sai Allah ya shigo ta hanyar banmamaki don ya “cece” shi ta wurin wawantar da kowa da kowa don su yi tunanin cewa Yesu lalle ya riga ya mutu alhali kuwa yana dai bakin mutuwa ne kawai.

Mutum zai yi fama ainun don ya ga ko akwai tsarin tunani mai ma’ana. Idan Allah yana da niyyar “ceton” Yesu, ba shakka da nan da nan ya ɗauke shi, kamar yadda ɗumbin mafiya yawan Musulmi suka gaskata. Wace irin “ta’aziyya” ko “ƙarfafawa” ce mala’ika ya yi masa idan sai daga bayan Yesu ya sha haƙuba marar masaltuwa sa’an nan Allah ya sa hannun taimako lokacin da yake gab da mutuwa a kan gicciye?

Da fari dai, irin raɗaɗi da shan azaban nan da ba su zama wajabi ba, don ceton Allah ya zo a makare bayan ya sha dukan haƙubar. Abu na biyu, da bai zama ta’aziyya ga Yesu ba idan ya san cewa ya fuskanci azabar gicciye, sai yana gab da mutuwa sa’an nan a cece shi. Bugu da ƙari kuma, idan an saukar da Yesu da rai daga kan gicciye zalla domin yana gab da mutuwa dukan mutane kuwa suna tunani ya riga ya mutu, ba mu ga yadda Allah ya “cece” shi ko ya sa hannu cikin wannan ba. Wannan ba kome ba ne illa tsautsayin da mafarkin ƙarya ya haddasa.

Dukanin gardamar ba shakka ta ƙure, ba ta daidaita da al’amuran dake cikin Bisharu ba. Gaskiyar abin duka ita ce, cikin jiki Yesu yana gab da shiga wuswasin shan azaba domin zunubi. Ya faɗa wa almajirinsa ke nan cewa, yana “shan wahala matuƙa – har ma kamar na mutu” (Markus 14:34).

Allah ya ji addu’ar Yesu, mala’ika kuma ya ƙarfafa shi domin ya ci gaba ya jure da gicciye da mutuwar, domin ya cika aikinsa, ya fanshi masu zunubi daga zunubi da mutuwa, da gidan wuta.

A ceci Yesu daga macewa alhali yana bakin mutuwa bayan sa’o’i na shan haƙuba a kan gicciye, wannan ya zama rashin hankali ko tunani. A cece shi daga mutuwa ta wurin ta da shi cikin ɗaukaka, da cikakkiyar lafiya wannan yana da ma’ana, kuma kan ka’ida, kuma a gaskiya shi ne ainihin labarin Littafi Mai Tsarki na gicciye.

Mun matsa a kan gardamar Deedat cewa wai, Yesu ya ɓadda kamanninsa bayan ya farfaɗo daga gicciye don kada a gane shi, Deedat ya kira wannan “cikakken dodo!” (shafi na 49). Ya ce lokacin da Yesu ya haɗu da almajirai biyu a hanyar zuwa Imuwasu a ranar da ya fito daga kabari da rai (Luka 24:15), sai ya ɓoye kamanninsa har sai lokacin da ya bayyana shi cikin kakkarya gurasa a gabansu, daga nan ya tafi abinsa. Wannan ba wani abu ba ne amma ƙoƙari ne na narkar da abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki wanda yake da zahirin gaskiyar abin da ya faru:

Sa’ad da yake cin abinci tare da su, sai ya ɗauki gurasa, ya yi wa Allah godiya, ya gutsura, ya ba su. Idonsu ya buɗe, suka kuma gane shi. Sai ya ɓace musu. Suka ce wa juna, “Ashe, zuciyarmu ba ta yi annuri ba sa’ad da yake magana da mu a hanya, yana bayyana mamu Littattafai?” (Luka 24:30-32).

Wannan ya buɗe asirin nan take. Nan da nan idanunsu suka buɗe, shi kuma ya ɓace musu! Idan muka nuna a hakanli a nassin nan, za mu iya ganin ainihin abin da ya faru lokacin da suka gane da Yesu.

Littafi Mai Tsarki ya faɗi cewa, bayan tashinsa, jikinsa zai ɗauki surar da dukan adalai za su samu a sama. Ya iya tuɓe dukanin kāsawar da ke duniya, yana kuma iya bayyana ko ya ɓata yadda ya ga dama. Yana iya bayyana ba labari cikin ɗaki yana kulle (Yahaya 20:19) yana kuma iya ɓoye ko ya nuna kansa yadda ya ga dama.

Saboda haka, a nan ba Yesu ne ya tuɓe “ɓadda kama” ba. Aya ta faɗa a sarari cewa, “idanunsu suka buɗe”. Nan da nan suka gane da ko wane ne shi. Haka kuma muke karanta cewa Yesun nan ya tashi, cikin jikinsa na dawwama, ba idanun mutanen kaɗai ya buɗe ba, amma har da tunaninsu ya buɗe don su fahinci ma’anar bayyananniyar maganar Allah (Luka 24:45).

Kamar dai yadda ya bayyana ba labari cikin ɗaki (Luka 24:36), haka kuma ya ɓace wa ganinsu. Abin da halin labarun nan ya ke nunawa a cikin Luka 24, ba a iya bayyana shi ta wurin kawo dalilan rinjayaswa. Ƙusar da aka buga a kan dukanin suran nan shi ne, tashin Yesu daga cikin matattu (Ka gwama da 24:46) abubuwan da ake ta ka ce – na ce.

Dukanin tsaikon labarun da ke cikin Bisharu shi ne gicciye, da mutuwar Yesu da kuma tashinsa daga cikin matattu. Sai mutum ya yi faman gaske na mummurɗe – kalma kafin ya kawo wata fassarar wannan dabam. Misali, kamar yadda Deedat ya ce wai Bisharun suna koyarwa a sarari cewa wannan ba wani abu ba ne, amma kabari ne wanda Yusufu na Arimatiya ya fafe musamman cewa Yusufu ya ɗauke jikin Yesu, ya “kwantar da shi a cikin sabon kabari da ya tanarda wa kansa” (haka kuma yake a cikin Markus 15:46; Luka 23:53). A cikin Yahaya 19:41,43 sau biyu ya ce an sa Yesu cikin kabari an naɗe shi bisa ga al’adar-binnewa ta Yahudawa. Ƙoƙarin Deedat na azabtar da labarin nan na jana’iza cikin nasa surkullen mai cewa wai an sa Yesu cikin wani “babban ɗaki” don ya “farfaɗo” shaida ce da kanta mai nuna cewa gardamar Deedat ba ta da wani tasiri ko kaɗan.

A ƙarshe za mu yi la’akari da maganganunsa guda huɗu a shafi na 50 cikin ɗan littafinsa in da ya nuna cewa, mutane da yawa sun yi shaida ranar tashin cewa yana da rai. Ya rubuta kalmar da manyan harufai, ya ja layi a ƙarƙashinsu, ya kuma bi da alamar mamaki a kowanne. Ya mai da wannan tamkar yana goyan bayan ra’ayinsa ne mai cewa wai Yesu bai mutu ba a kan gicciye, amma yana nan da ransa. Muna mamakin wannan irin tunani ga dukanin batun tashi daga matattu, kamar yadda aka nuna shi a ckin Bisharu, ainihin gaskiyannan ita ce Yesu ya tashi da rai daga matattu. To, menene, ne, Deedat yake ƙoƙarin tabbatarwa? Shaidun cewa Yesu yana da rai su ne cibiyar dukanin gaskatawar Kirista, cewa Yesu ya tashi daga cikin matattu bayan da aka kashe shi a kan gicciye.

Da Deedat ya ɗauko daga Luka 24:4,5, sai ya ɗauki waɗannan: “me kuke neman rayayye a cikin matattu?” Da gangar ya bar sauran kalmomin nan da suka bi baya:

“Ku tuna yadda ya gaya muku tun yana Galili cewa, ‘Lalle ne a ba da Ɗan mutum ga mutane masu zunubi, a gicciye shi, a rana ta uku kuma ya tashi’.” (Luka 24:6,7).

A cikin kalmomin nan mun gani a sarari mala’ika yana maganar Yesu da aka gicciye ya kuma tashi a rana ta uku. Sun yi iƙirari a sarari cewa yana da rai domin ya taso ke nan daga cikin matattu. Daidai haka kuma ’yan’uwa suka faɗa a Urushalima ga almajiran da suka zo daga Imuwasu:

“Hakika Ubangiji ya tashi, har ya bayyana ga Bitrus!” (Luka 24:34).

Haɗaɗɗiyar shaida ta dukansu ita ce, Yesu yana da rai domin hakika ya tashi daga matattu. “Ya tashi” (Markus 16:6), ita ce shaidar dukan duniya a ranan nan. Ya fito daga matattu da rai, ya kuma yi nasara da dukan ikon mutuwa. Ya sa ya yiwu ga mutane su tashi zuwa rai madawwami cikin nasara a kan mutuwa da zunubi (I Korantiyawa 15:55-57). Ya cika iƙirarin da shi kansa ya yi:

“Ai, ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai. Wanda ya gaskata da ni, ko ya mutu zai rayu (Yahaya 11:25).

Abin tausayi, dukanin gardamar Deedat ba’a ce yake ta turawa a kan al’amarin ɗaukaka da aka bayyana a cikin Bisharu. Yadda muka ɗauki gardamarsa mai cewa Yesu ya sauko daga kan gicciye da rai, kuma ya farfaɗo, wannan ya nuna mana dukan abin da ya ke faɗa cin iska ne kawai. Gardandaminsa da ya gabartar masu ɓatarwa sun kai ga ƙarasawa da cewa ya kāsa sarai ya tabbatar da ra’ayinsa, gicciye – “almara” (Cruci- “fiction”) ya zo daga cibiyar “farfagandar” – da ba ta dace ba!

5. MUGAYEN MAGANGANU A CIKIN ƊAN LITTAFIN DEEDAT

Ɗaya daga cikin abubuwan da sukan buga ni a kai -a kai a duk sa’ad da na karanta ’yan littattafan Deedat shi ne rashin aunawarsa in zai yi maganganunsa, sai ya yi marasa amfani, marasa iko. Kamar dai yana yawo da hankalin Musulmi marasa sanin Littafi Mai Tsarki, yana kuma sa zuciya masu karantawa za su yarda da duk abin da ya faɗa ba tare da sun tambaya ba. Ya tabbata ba zai iya ƙoƙarin rinjayar Kirista masu karanta rubuce-rubucensa ba, su da suka san Littafi Mai Tsarki sosai, waɗanda kuma sai dai su yi mamakin zace-zacensa. Da farin farawa, a cikin ɗan littafinsa ya ce:

Daga “kira a yi ɗamarar yaƙi” a ɗaki bene, da kuma rarraba askarawa matsara a Gatsemani, da kuma addu’a mai jiɓin gudajin jini wadda ya yi ga Allah mai jinƙai don ya taimake shi, wannan ya nuna cewa Yesu bai san kome ba a game da kwantaragin da aka yi na gicciye shi (Ɗan littafin Deedat, “Crucifixion or Cruci-fiction” shafi na 16).

Magana ta ƙarshe, a kan cewa Yesu bai san kome ba a game da gicciye shi da za a yi, maganar ruɗi ce kawai marar kāriya daga ɗumbin gaskiyar da take akasin maganarsa. Sau da dama Yesu ya sha faɗa wa almajiransa cewa za a gicciye shi a kashe shi, ya kuma tashi daga cikin matattu a rana ta uku cikin maganganu kamar waɗannan:

Ya ce, “Lalle ne Ɗan mutum ya sha wuya iri iri, shugabanni da manyan firistoci da malaman Attaura su ƙi shi, har a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi” (Luka 9:22).

“To, ga shi, za mu Urushalima, za a kuma ba da Ɗan mutum ga manyan firistoci da malaman Attaura, za su kuwa yi masa hukuncin kisa, su bashe shi ga al’ummai, su yi masa ba’a, su yi masa bulala, su kuma gicciye shi. A rana ta uku kuma za a tashe shi” (Matiyu 20:18,19).

Bayan da ya tashi daga matattu, sai da ya tsauta wa almajiransa saboda ba su gaskata da dukan abubuwan da ya gaya musu ba, da kuma rashin gaskata annabce-annabcen annabawan dā cewa, za a kashe shi ya kuma tashi a rana ta uku (Luka 24:25,26,46). A lokatai da dama ya sha faɗa a sarari cewa, wannan ne dalilin da ya sa ya zo duniya. Ya faɗa musu cewa ya zo domin ya ba da ransa fansar mutane da yawa (Matiyu 20:28), za a farfasa jikinsa, a zubar da jininsa domin duniya ta rayu (Yahaya 6:51), yana kuma da iko ya ba da ransa domin duniya ta rayu (Yahaya 10:18). Hakika wannan wauta ce a ce Yesu bai san kome ba a game da gicciyen da ke jiran sa. A akasin wannan, da yake fuskantar wannan maƙurar lokaci na rayuwarsa a duniya, a matsayin Mai Ceton duniya, zai ceci ɗan adam, ya shirya hanya domin mutane da yawa zuwa shiga rai madawwami, ya yi shela, “Da ma na zo ne takanas domin wannan lokaci” (Yahaya 12:27). Saboda haka, yana sane da matuƙar ƙaddarar da ke jiran sa, kuma ya sha ambaton ta da cewa “lokacina” (Yahaya 2:4; 7:6). Ba mutumin da aka taɓa faɗar haka a kansa, “lokaci ya zo, mutumin ya zo”. Lokacin ceton duniya ya zo. Allah kuma ya aiko da mutumin nan kaɗai wanda zai kammala wannan, shi ne, Yesu Almasihu.

Deedat ya yi suɓul-da-baka lokacin da ya ce, sunan nan “Ɗan Allah” a cikin Littafi Mai Tsarki, “wani bayani ne marar lahani a cikin tauhidin Yahudanci” (shafi na 25). Akasin wannan shi ne, Musulmi suna gāba ƙwarai da tarayyar Allah da kowane abu, wanda wannan bai yarda cewa zai yiwu Allah ya kasance Ɗa ba, don haka Yahudawan wancan zamani, har zuwa na yau ma suna ƙin wannan ra’ayi gaba ɗaya. Da babban firist ya tambayi Yesu ko shi Ɗan Allah ne, kamar yadda ya ke ji ana faɗa masa irin wannan iƙirari, sai Yesu ya amsa “Ni ne” (Markus 14:62). Idan wannan “bayani ba shi da lahani” kamar yadda Ɗeedat ya yi iƙirari, ai, da babban firist bai zama dabam ba har ya ƙi yarda da haka, amma nan take ya yi ihu “ya yi sāɓo” (Matiyu 26:65). Da aka kai Yesu a gaban Bilatus, Yahudawa suka yi kururuwa:

“Ai, muna da shari’a, bisa ga shari’an nan kuwa ya wajaba a kashe shi, saboda ya mai da kansa Ɗan Allah” (Yahaya 19:7).

Har a yau ma Musulmi suna kauce wa wannan al’amari, suna kuma zargin Kirista da mai da annabi Isa ya zama Ɗan Allah. Amma da wuya ga Yahudawa su amince da iƙirarin nan a kan mabiyan Yesu lokacin da Yesu kansa ya yi wannan furci a gabansu. Suka yi ihu, “Ya mai da kansa Ɗan Allah”, dalilin da ya sa suka zargi Yesu ke nan cewa ya yi sāɓo. Duk da haka, ta wurin tashinsa daga matattu Allah ya ba da tabbaci ga dukan mutane cewa hakika Yesu ƙaunataccen Ɗansa ne kamar dai yadda ya yi iƙirari (Romawa 1:4).

Deedat ya yi irin wannan iƙirari cikin surkulle lokacin da ya ce, “duk wani Kirista masani zai tabbatar” cewa, an rubuta Bishara ɗaruruwan shekaru bayan zamanin Yesu. Sananne ne ga dukan masanan Littafi Mai Tsarki nagari cewa Bisharun nan huɗu (Matiyu, Markus, Luka da Yahaya) duka an rubuta su wajen AD 55-60 (ƙasa da shekara talatin bayan tashin Yesu daga matattu), Bishara daga hannun Yahaya kuma har zuwa A.D 70. Sai “masana” masu nukura kaɗai za su ce ba haka ba, ko ma masu tsananin sèka sun yarda da kwanakin nan (shekaru). Ta yaya za a ce an rubuta Bisharu bayan an yi ɗaruruwan shekaru alhali rubuce-rubucen farko da aka samu suna nuna suna nan tun farkon A.D. 120 har marubuta Kirista na farko sun ɗauko daga cikin Bisharu a cikin tsara ta fari ta zamanin manzanci?

Deedat ya yi wata magana mafi baƙin ciki lokacin da ya ce a wani wuri wai “ceto yana da arha a cikin Kristanci” (shafi na 61). Muna shakka, in har Musulmi za su ɗauki yardar da Ibrahim ya yi ya miƙa ɗansa hadaya a ce “hadaya mai arha”. Hakika kuma, babu wata arha a cikin yarda da Allah ya yi ya ba da Ɗansa ya zama hadaya domin zunubanmu. Littafi Mai Tsarki yana faɗa mana a sarari, “sayenku aka yi da tamani” (IKorantiyawa 6:20) wane tamani!- , Manzo yana iya magana kaɗai a kan sakamakon “baiwar Allah da ta fi gaban a faɗi” (2Korantiyawa 9:15). Ba yadda zai yiwu a ƙiyasta tamanin da aka biya ba, domin ceton cikin Kristanci shi ne mafi tsada da duniya ta taɓa gani - ran Ɗa makaɗaici na Allah madawwami. Haka kuma babu mutumin da zai sami wannan ceto sai dai ya miƙa dukanin ransa ga Allah ta wurin ba da gaskiya ga Ɗansa, ya kuma miƙa dukanin kansa da halinsa ga nufin Allah.

A ƙarshe, a cikin ɗaya daga cikin zarge-zargrnsa marasa zama daidai, Deedat ya yi iƙirari cewa, labarin bayyanar Yesu a gaban almajirinsa mai shakka, Toma, kamar yadda yake a cikin Yahaya 20:24-29, “babban laifi ne ‘ai ƙaga labarin bisharar a ka yi’” (shafi na 31). Har kuma ya yi gaggawar ƙara yin wani iƙirarin:

Manyan masanan Littafi Mai Tsarki suna zuwa ga ƙarasawa da cewa, “Toma mai shakka”, labarinsa daidai yake da na macen da aka “kama cikin jina” – (Yahaya 8:1-11); wato an ƙaga shi ne! (Ɗan littafin Deedat “Crucifixion or Cruci-fiction?, shafi na 76).

Abu mafi muhimmanci da Deedat bai faɗa mana ba shi ne, su wanene waɗannan da ya ke kira “manyan masana Littafi Mai Tsarki”. Babu ko ɓarɓashin abin shaida a ko’ina da ya goyi bayan iƙirarin cewa labarin shaidarsa ta ganin Yesu, har ya ce shi ne Ubangijinsa da Allahnsa kuma, a ce wai “ƙage” ne. Har yanzu labarin yana nan, ana samun sa cikin dukan rubuce-rubucen farko da muke da su waɗanda ba su da wani bambanci cikin karatu, abubuwan shaida kuma suna nunawa gaba ɗaya suna goyon bayan ainihin labarin. Babu goyon baya na kowane iri ga wannan ra’ayi na wai wai cewa wannan labari ƙaga shi aka yi.

Zai yiwu Deedat ya kafa tushen iƙirarinsa a kan zato cewa ba ƙusance Yesu aka yi a kan gicciye ba, amma ɗaure shi kaɗai aka yi da igiyoyi. Ya kuma yi wata magana mummuna da ya ce, “ba kamar yadda duk ake gastawa ba, ba a ƙusance Yesu a kan gicciye ba” (shafi na 31). Abubuwan da aka haƙo na tarihi a ƙarƙashin ƙasa a ƙasar Falisɗinu suna tabbatar da cewa Romawa suna gicciye kamammunsu ta wurin ƙusancewa ga gicciye (an sami ƙasusuwa, wato ƙwarangwal da ƙusa ga dukan ƙafafu a ’yan shekarun da suka wuce). Bugu da ƙari, shaida ce a duniya gaba ɗaya ta annabce - annabce, ga kuma labarun tarihin gicciyen Yesu cewa an ƙusance shi ga gicciyensa (Zabura 22:16: Yahaya 20:25; Kolosiyawa 2:14). Gardamar Deedat ba “akasin gaskatawar da aka saba da ita” kaɗai ba ne kamar yadda ya ɗauka, amma, kamar batutuwansa masu yawa, shi ma akasi ne ga Maganar Allah, akasin labarin tabbatattun tarihin kuma, akasi kuma ga abubuwan shaida, kamar kuma duka, sau da yawa akasin tunani mai kyau. Ya kāsa samar da ko ɗan ɓarɓashin shaidar da za ta goyi bayan iƙirarinsa cewa an ɗaure Yesu da igiyoyi ne ga gicciye maimakon ƙusoshi; don haka iƙirarinsa fanko ne, da ƙarfin halin kai hari a kan ƙwaƙƙwaran tarihi na gaskiya cewa an ƙusance Yesu ne a kan gicciye, babu kuma wata shaida ta kowace iri mai nuna cewa wannan labari “ƙage” ne.

Idan akwai wani tasiri ko ƙaƙa a cikin dukan farmakin Deedat a kan labarun Littafi Mai Tsarki na gicciye, da mutuwa da kuma tashin Yesu Almasihu daga cikin matattu, da zai yi wuya ya ƙarasa da irin waɗannan iƙirari da suke abin ba’a kamar waɗannan da muka bi ciki. Iƙiraran Deedat sun nuna matsayinsa na fidda zuciya cikin sèka da ya ke faman yaƙi cikin rashin kangadonsa don ya tabbatar da abin da ba shi yiwuwa.

6. DA GANGAR DEEDAT YA DANNE GASKIYAR BISHARA

Bayan dukan abin da ya gudana a baya, ba zai zama abin mamaki ga masu karantunmu ba su gane cewa da gangar Deedat ya rufe wasu kalmomi daga Littafi Mai Tsarki waɗanda ba su dace da manufarsa ba. Ana gobe za a gicciye Yesu, sai manyan firistoci suka zo wurin Bilatus, a cikin Matiyu 27:62-64 kuma muna karanta cewa, sun roƙi a hatince kabarin. Ga yadda yake a cikin ɗan littafin Deedat:

“Ranka ya daɗe, mun tuna cewa wancan mayaudarin ya ce... In ka yarda ka umarta, yadda za a tsare kabarin har rana ta uku, don kada... ruɗami NA ƘARSHE ya yi muni fiye da NA FARIN (kuskure)” (Ɗan littafin Deedat, “Crucifixion or Cruci-fiction”shafi na 42).

Sau biyu cikin ayar da ya kwaso, mutum zai sami wurin da ya sa ɗigo-ɗigo uku kamar akwai abin da aka tsallake saboda ba shi da muhimmanci ko bai dace da al’amuran da ake batu a kai ba. Gardamar Deedat ita ce, wai Yahudawa nan da nan suka gane cewa har yanzu zai yiwu Yesu yana da rai, kuma zai yiwu an “cuce” su ne (shafi na 42). Zai yiwu sun je wurin Bilatus don su sa ya hatimce kabarin don kada ya farfaɗo ya tsere. Duk da haka in ji Deedat, sun makara da kwana guda, kuma kuskurensu na “ƙarshe” shi ne da suka yardar wa wasu almajiran Yesu su sami zarafi “su yi wa mutumin nan mai raunuka taimako” (shafi na 43).

Dukan abin da ya faru a nan shi ne, ya zamar wa Deedat tilas ya share kalmomi kashi biyu daga ayar da ya ɗauko, ya yi haka ba don kalmomin ba su da muhimmanci ba ne, amma domin sun sāke gardandaminsa ne gaba ɗaya, don kuma ya tilasta wa mai karatunsa ya sami hoto na dabam na ainihin abin da ke gudana. Za mu rubuta abin da ke cikin ayoyin nan duka kamar yadda suke, za a rubuta kalmomin da Deedat ya share ya maye su da ɗigo-ɗigo, za a sa su da siraran haruffai. Ga yadda suke a cikin ayoyin:

“Ya mai girma, mun tuna yadda mayaudarin nan, tun yana da rai ya ce bayan kwana uku zai tashi daga matattu. Saboda haka, sai ka yi umarni a tsare kabarin nan sosai har rana ta uku, kada almajiransa su sace shi, sa’an nan su ce wa mutane wai ya tashi daga matattu. Yaudarar ƙarshe za ta fi ta farkon muni ke nan” (Matiyu 27:62-64).

Nan da nan mun ga cewa ko kaɗan Yahudawa ba su gaskata cewa ya sauko daga kan gicciye da rai ba. Sun je wurin Bilatus, suna faɗar abin da Yesu ya faɗa tun yana rai. Waɗannan kalmomi ana iya fassara su da ma’anar cewa, bisa ga ganewarsu Yesu ba shi da sauran rai. Sun roƙi Bilatus ya hatince kabarin, ba don suna jin tsoro kada mai raunin nan zai murmure ba, amma domin suna jin tsoro kada almajiransa su sace gawar, su kuma yi shelar cewa ya tashi daga matattu. Wannan ce ainihin ma’anar ayoyin nan muraran.

Dalilin da ya sa Deedat ya tsallake kalmomin nan masu siraran haruffai a fili yake. Kalmomin sun kāshe shi gaba ɗaya. A ƙashin gaskiya, mun ga yadda ya ke morar wannan dabara loto-loto a cikin ’yan littattafansa gāba da Kristanci. Yana dagula maganar Allah ta wurin murɗe wasu matani daga ainihin wurinsu a cikin nassi yadda ya ke ji za su cika muradinsa, loto-loto kuma yakan yi watsi da wasu gaba ɗaya waɗanda ya san za su hana tasiri ga ra’ayoyinsa. A wannan wurin ne kaɗai ya yi haka da wannan nassin ya murɗe wasu kalmomin nassin don ya yi ƙoƙarin tabbatar da cewa Yahudawa sun yi tsammani har yanzu Yesu yana da rai, waɗanda kuma ya ga nan da nan za su nuna cewa wannan ko kaɗan ba shi ne abin da ke cikin tunaninsu ba, sai ya dagular da su.

Ba shakka, duk Musulmi na gaskiya zai iya ganin cewa, dukanin tsaikon ɗan littafin Deedat a kan gicciye murɗe gaskiya ne kurum, kuma a kai-a kai ya sha rikitar da fayyatattun maganganun da ke cikin Bishara masu shaida ainihin gaskiyar gicciye, da mutuwa da kuma tashin Yesu Almasihu daga cikin matattu ba tare da wata ƙumbiya-ƙumbiya ba.

Zai yiwu mu ƙara da cewa ba wannan ne lokaci na fari ba da muke samun littattafai da aka buga daga santar (cibiya) Deedat inda suke kwasowa daga rubuce-rubuce, su mummurɗe su. Muna ba da shawara ga dukan masu karatu su bi cikin wuraren nan da aka kwaso, inda aka soke wasu kalmomi, aka cike gurbinsu da ɗigo-ɗigo guda uku, su bi su da lura ainun. Abin da ya ragu an riga an murɗe shi yadda zai bi irin fassarar yadda dukan abin da aka kwaso daga nassi ba zai yiwu ya shiga daidai ba idan an bi shi da lura sosai.

Yahudawa sun tuna yadda Yesu ya sha maimaita faɗar annabci cewa zai tashi daga matattu bayan kwana uku, su kuwa suna so su hana kowace yiwuwar cikar annabcin nan-ko ta ainihin tashinsa daga matattu, ko kuma ta wurin dabarar almajiransa. Babu abin da ya yarje wa iƙirarin Deedat na cewa “Yahudawa sun yi shakkar mutuwar Yesu” har kuma suna “kyautata zaton ya tsere wa mutuwa a kan gicciye” (shafi na 79). Kalmomin da Deedat ya tsallake na ayoyin da ya kwaso ya sa cikin ɗan littafinsa a shafi na 42, ya nuna a sarari cewa sun gamsu, lalle Yesu ya mutu, amma ba su so almajiransa su yi iƙirari cewa ya tashi da rai.

Kirista ba su ƙin duk wata sèka da ƙididdiga a kan littattafansu. A gaskiya, muna maraba da su, domin ƙalubala ne a gare mu don mu tabbatar da abin da muka gaskata, kuma babu Kirista na gaskiya da zai so ya gaskata abubuwan da ba za su jure wa sèkar ƙiddiga ba. A ƙashin gaskiya wallafe-wallafe kamar irin na Deedat sun yi mana laifi, kamar nasa mai suna “Crucifixion or Cruci-fiction?” wanda ba abin da ke ciki sai shaidu masu karkatarwa da dagular da bangaskiyarmu, kuma wannan an yi su duka domin raunata jinmu a rai (wato don dai a ji mana). Mun haƙƙaƙe cewa haka yawancin Musulmi ma za su ji idan wata wallafar Kirista ta daddagula Islama kamar yadda Deedat ya ke cin mutuncin Kristanci.

Mun ta’anzantu da gane cewa, akwai Musulmi da yawa a Afrika ta kudu da suka bayyana rashin yardarsu da irin rubuce-rubucen nan. Wata mujallar Musulmi ba da jimawa ba ta yi magana a kan dabarun Deedat kamar haka:

Sananniyar gaskiya ce cikin Afrika ta Kudu, har ma a cikin rukunonin Kiristan bishara ta gaskiya cewa, musamman Mr. Ahmed Deedat ya gane cewa, jama’ar Musulmin Afrika ta Kudu gaba ɗaya ba su yarda duka-duka da hanyarsa ta yin fargagandar Islama ba. Wannan mujalla mai suna a turance, “Muslim Digest” ita kanta ta tanadar da shaida mai dama masu nuna cewa sun yi sakaci shekaru masu yawa ba su yi sèkar dabarar farfagandar Islama ta Mr. Deedat ba, musamman a tsakanin Kirista. Ko ƙanƙani babu wasu ƙungiyoyin addinin Musulinci, da mutane ɗaya -ɗaya da suka yi sukar dabarar ko hanyar farfagandar Mr. Deedat ta Islama wadda ta haifar da mugun tunani gāba da Musulmi (“The Muslim Digest”, Jul/Aug/Sept., 1984).

Za mu rufe da taƙaitaccen la’akari a kan gardamar Deedat cewa, idan har za a iya tabbatar da cewa Yesu bai mutu ba a kan gicciye, to, wannan zai tabbatar da cewa ko kaɗan ma ba a gicciye shi ba ke nan! A cikin rubuce-rubucen farko mun nuna cewa soki-burutsun gardamar Deedat ta taso ne daga halin ƙaƙa naka yi da Deedat ya jefa kansa a ciki ta wurin ra’ayinsa mai cewa Yesu ya jure gicciye. Kur’ani ya faɗa a sarari cewa “ba a gicciye ko kashe Yesu ba” (Suratun Nisa 4:157) kuma dubun dubatar mafiya yawan Musulmi a duk fāɗin duniya suna riƙe da wannan ra’ayi mai ma’ana cewa ba a taɓa gicciye Yesu ba ko kaɗan. Na yi wata tattaunawar musayar ra’ayi da Deedat a Benoni, kan magana shi ne ko an Gicciye Almasihu? (A Turanci: “Was Christ Crucified?”) a 1975, wata jarida kuma ta taƙaice gardamar Deedat sosai da sosai da ta ce, “An gicciye shi, amma bai mutu ba in ji Deedat. Da shike akwai Musulmi masu tunani da aiki da hankali, waɗanda suke cewa dukanin ra’ayin Deedat ba shi da tushe, ba don abin da Littafi Mai Tsarki kaɗai ya faɗa ba, amma har da abin da Kur’ani ya faɗa a game da gicciye, yanzu Deedat yana ƙoƙarin yakice kansa daga ruɗamin da ya jefa kansa a ciki.

Saboda haka ya yi gardama cewa “a gicciye” yana nufin a “kashe mutum a kan gicciye”, ya kuma ce, idan har mutum ya jure da gicciye, wannan yana nufin cewa ba a taɓa gicciye shi ba ke nan. Ya nuna cewa, cikin Turanci in an ce “an sa masa lantarki” ana nufin an kashe shi ke nan ta wurin lanƙaya masa lantarki, “ratayewa” kuma ana nufin an kashe she ta wurin ratayewa. Saboda haka ya ce, a cikin turanci “a gicciye” mutum ana nufin “kashe mutum ta wurin gicciyewa”, ya kuma yi iƙirarin cewa, ba laifinsa ba ne a game da rashin ingancin harshen turanci a kan wannan, wanda ba shi da wasu kalmomi da za su maye gurbin waɗannan da aka yi ƙoƙari da su a kan gicciyewa, lanƙaya lantarki, ko ratayewa.

Faɗin haka ya sa ya kuskure batun gaba ɗaya. Labarun gicciye a cikin Littafi Mai Tsarki tun asali an rubuta su cikin harshen Hellenanci ne, kuma fiye da shekara dubu sun wuce kafin a juya cikin harshen Ingilishi. Muhimmin batu ba na abin da “za a gicciye” yana nufin abin da Deedat ya fahimta ba ne a game da harshen Ingilishi, amma abin da ake nufi cikin Hallenanci ne a lokacin da aka rubuta Bisharu tun da fari. Ɗauko aya guda za ta wadatar ta nuna cewa “a gicciye” bisa ga zamanin Littafi Mai Tsarki shi ne a “ƙusance mutum a kan gicciye”. Manzo Bitrus ya taɓa nuna wa taron Yahudawa:

Shi Yesun nan fa, an ba da shi bisa ƙaddarar Allah da rigyasaninsa, ku kuwa kuka gicciye shi, kuka kashe shi, ta hannun masu zunubi (Ayyukan Manzanni 2:23).

Ayar tana nunawa a sarari, kun gicciye shi, kun kashe shi, ma’ana babu wata shakka ita ce “kun ƙusance shi a kan gicciye kun kuma kashe shi a can”. Saboda haka rashin hankali ne a ce idan a ainihi ba a kashe mutum a kan gicciye ba, to, ba a ma taɓa gicciye shi ba ke nan. Idan “a gicciye” ana nufin a kashe ne a kan gicciye kaɗai, da Bitrus cewa zai yi “kun gicciye shi”, amma ta wurin ƙarin da ya yi, “kuma kuka kashe shi”, ya nuna a fili cewa, “a gicciye” ana nufin ƙusancewa a kan gicciye ke nan. Deedat yana nan kan rikitarwarsa mai cewa ba shakka an gicciye Yesu amma bai mutu ba – ra’ayin da yake abin ƙyama ga Kirista na gaskiya haka kuma yake ga Musulmi na gaskiya.

Mutum zai yi ta fama in zai bi tunanin dake a hanyar da Deedat yake fuskantar al’amarin. Yana tsammani cewa idan zai iya tabbatar da cewa Yesu bai mutu a kan gicciye ba, to wannan yana tabbatar da cewa Kur’ani yana da gaskiya ke nan da ya ce Yahudawa ba su kashe shi ba. Amma ta yaya wannan batu zai iya tsayawa alhali kuwa dukanin gardamar ta yarda da wani abin da Kur’ani ya musunta - ainihin gicciyen Yesu? ko kaɗan babu wata ma’ana a cikin gardamarsa, ko kaɗan.

Quiz

  1. KACINCI-KACINCI

  2. Idan ka karanta ɗan littafin nan a hankali, za ka iya amsa waɗannan tambayoyi waɗanda sashi ne na makarantarmu ta Littafi Mai Tsarki a Gida:

  3. Ka rubuta misali uku daga rayuwar Almasihu da suke tabbatar da cewa bai shiga harkar siyasa ba.

  4. Yesu ya ce wa almajiransa, “Ya isa” lokacin da suka ce, “Ya Ubangiji, ai, ga takuba biyu” (Luka 22:38). Me Yesu ya ke nufi?

  5. Don me Yesu ya zaɓi ya hau jaki a lokacin da ya yi shigar nasara zuwa cikin Urushalima?

  6. Annabi Zakariya na Tsohon Alkawari, ya yi annabcin cewa Ubangiji zai kawar da laifin al’umman nan rana ɗaya (Zakariya 3:9). Yaya annabcin nan ya cika?

  7. Ka bayyana batutuwan gaskiya guda uku da Yesu ya sani a daren kashegarin gicciyensa tun kafin su faru: a) a game da Yahuza maci amana, b) a game da Bitrus, c) a game da dukan almajiran.

  8. Ka karanta Matiyu 17:22,23. Wane faɗi Yesu ya yi a cikin ayoyin nan biyu a game da abin da zai auka da shi?

  9. Ta yaya Bilatus ya sani ba shakka Yesu ya mutu?

  10. Ta yaya annabcin Daniyel ya cika, da ya ce, “Za a kashe naɗaɗɗe, ba zai sami kome ba” (Daniyel 9:26).

  11. Ka bayyana wurin da aka binne Yesu, kamar yadda Bisharu huɗu suka yi magana a kai.

  12. Ka karanta Luka 24:4-7. Waɗanne batutuwan gaskiya ne mala’ika ya shaida a kan Yesu a cikin ayoyin nan?

  13. Menene tamanin ceto a cikin Kristanci?

  14. Ka karanta Matiyu 27:62-64. Me Yahudawa suka sani a game da Yesu kamar yadda aka ambata a cikin ayoyin nan?

Ka rubuta amsoshin tambayoyin nan a wata takarda dabam, ba tare da wani sharfi ba. Idan ka amsa kashi biyu bisa uku na tamnayoyin da kyau, za mu aiko maka wani littafi guda daga cikin littattafanmu, domin ka ƙarfafa kanka a cikin bangaskiya, da bege da kuma ƙauna.


P.O.Box 66
CH - 8486 
Rikon
Switzerland