Tarihin Matanin Kur’ani Da Na Littafi Mai Tsarki

Tarihin Matanin Kur’ani Da Na Littafi Mai Tsarki

JOHN GILCHRIST


Nazarin Kur’ani da Littafi Mai Tsarki

Yawancin Musulmi ba su gaskata cewa rashin hankali ne ga Musulmi na gaske ya soki addinin wani ba. Akwai wasu da suka sha dabam da suke keta wannan ka’idar, ɗaya daga cikin irin waɗannan shi ne Ahmed Deedat wanda sau da dama yana kai hari ga Kirista da addininsu cikin ruhun Jihadi irin na zamanin dā. Ɗaya daga cikin yunƙurinsa na sukar Kristanci a cikin ɗan littafinsa mai suna “Ko Littafi Mai Tsarki Maganar Allah Ne?, Cibiyar Farfagandar Islama tasa da ke a Durban ita ta fara buga shi a 1980.

A Cikin ɗan littafin nan Deedet yana ƙoƙari ne don ya tabbatar cewa Littafi Mai Tsarki ba zai taɓa zama Maganar Allah ba. Wannan zai iya burge jahilai da waɗanda ba su san irin fassararsa ba, ba wuya ma ya rinjaye su, amma waɗanda suke da ainihin sani game da su matani da kuma tarihin matanin Kur’ani da Littafi Mai Tsarki, za su gane shirmensa nan take.

Bisa ga dukan alamu dai Deedat yana sane sarai da kāsawarsa cikin wannan batu, don ya lulluɓe kāsawar, sai ya ɓuge da wani irin ƙarfin hali da maganganun ƙalubala don ya nuna dogon surutunsa mai rinjayarwa don ya kange idanun mai karatu. A S K Joommal ya ba da rahoton wata muhawara da Deedat ya shiga, ya ce: “Ko gadarar mutum ba ta da ƙarfi, babu kuma kāriya, mutum yana iya kutsawa ya sami rinjaye da tagomashi wurin taron mutane ta wurin yawan surutu da iya daɗin baki”.

Mun sani Joomal ya dogara ga irin wannan dabarar a cikin littafinsa mai suna Littafi Mai Tsarki: Maganar Allah ko Maganar Mutum? (A turance ana kiran littafin “The Bible: Word of God or Word of Man?”), ga maganar ɗan littafin ne Deedat ya juya a shafi na 44 da 51, ba shakka Deedat kansa ga irin wannan dabarar ne ya ɓuge a cikin ɗan littafinsa gāba da Littafi Mai Tsarki. Duka biyunsu tabbatacce ne suna fama da “ƙarancin cancantar” famansu na gāba da Littafi Mai Tsarki namu.

Deedat, da ƙarfin hali a cikin ɗan littafinsa a shafi na 14 ya ba da shawara cewa, idan har Musulmi zai miƙa littafinsa ga mishanerin Jehovah’s Witnesses ya kuma nemi amsa a rubuce daga gare shi, to, ba zai taɓa ƙara ganinsa ba – balle fa a sami amsa.

Mu Kirista mun gaji da fafitikar da mutumin nan yake yi shekara da shekaru don ya ƙasƙantar da gaskatawarmu, amma domin a watsar da daɗin bakinsa na lamfa cewa, ɗan littafinsa zai kori kowane mishaneri ya koma gida, mun yanke shawara mu ba shi amsar da yake bukata. Mun amsa wa sauran littattafan da ya buga a baya mun kuma lura cewa, duk inda muka kā da shi cikin wulakancinsa, sai ya tabbata cewa ba zai iya ƙara cewa kome ba cikin amsa mana. Wannan ma ya tabbatar da wani abu.

1. “INGANCI UKU NA SHAIDA”

Deedat ya fara ɗan littafinsa da kwasowa daga rubutun Shehunnan marubutanmu Kirist, Scroggie da Cragg inda yake nuna yiwuwar alamun hannun mutum cikin Littafi Mai Tsarki. Gabagaɗi ya ƙarasa da cewa:

Waɗannnan likitocin addinin suna faɗa mana a sarari yadda kowane ɗan adam zai iya ganewa cewa, Littafi Mai Tsarki aikin hannun mutum ne. (Ɗan littafin Deedat mai suna Is the Bible God’s Word? Wato Ko Littafi Mai Tsarki Maganar Allah Ne? Shafi na 2).

Cikin mugun wayo, sai Deedat ya tsallake, ya ƙi sanar da masu karantunsa abu na farko, cewa Ikilisiyar Kirista a koyaushe ta amince da cewa, mutane ne suka rubuta Maganar Allah ta wurin bishewar hurewar Ruhu Mai Tsarki (2 Bitrus 1:20,21), abu na biyu kuma shi ne, waɗannan marubuta ba sun “fitar da kyanwa daga cikin jaka” ba ne (Kamar yadda Deedat ya sha faɗi cikin shayinsa) amma suna nan domin su nuna yadda Allah ya bayyana maganarsa.

Deedat ya ɗauko daga rubutun Cregg mai suna “The Call of the Minaret” (Ma’ana kiran salla), daga mahallin rubutun Deedat, akwai dabarar da ya yi amma abin bai shiga ba sam. Creg yana maganar abin da mutum ya yi cikin Littafi Mai Tsarki don ya nuna fa’idar da Littafi Mai Tsarki yake da ita fiye da Kur’ani. Kur’ani dai an ce babu ko alamar hannun ɗan adam a ciki, cikin Littafi Mai Tsarki kuwa da nufi ne Allah ya zaɓi ya bayyana maganarsa ta wurin rubutun hurarrun annabawa da manzanninsa, yadda ba kai maganarsa ga ’yan adam kaɗai za su yi ba, amma har sadar da ita ga mutum yadda zai gane, da kuma ikon rarrabe ta da kyau. Ba karɓar Maganar Allah kaɗai manzo ya yi ba, amma shi da kansa ya iya ba tare da sa ta kāsa ba, Ruhu Mai Tsarki ya hure shi, domin ya ɗauki ma’anarta ga masu karatunsa. Abin da Kur’ani ba zai iya yi ba ke nan idan ba ta da hannun ɗan adam kamar yadda ake ikirari.

Deedat, cikin wayonsa ya raba Littafi Mai Tsarki cikin “shaida iri uku dabam dabam” (Ko Littafi Mai Tsarki maganar Allah ne “Is the Bible God’s Word? shafi na 4), ga su, Maganar Allah “Word of God”, Maganganun Annabin Allah, “Words of a Prophet of God” da kuma Maganganun Masanin Tarihi “Words of Historian” Sai kuma ya ɗauko wasu sassa inda Allah yake magana, wasu kuma inda Yesu ya yi magana, na ƙarshe kuma inda aka faɗi abubuwa a kan Yesu, cikin girmankai Deedat yana nuna cewa Musulmi suna da hankalin da za su rarrabe waɗannan sassa guda uku. Ya ce Kur’ani kaɗai ne yake da maganar Allah, Hadisi kuma yake da maganganun Annabi, sauran littattafai kuma suke da rubuce - rubucen masana tarihi. Ya gama da cewa:

Da kishi Musulmi suke tsare shaidun nan iri uku a keɓe da aka ambata nan sama, cikin amintaccen ingancin iko. Bai taɓa daidaita su ba (ɗan littafin Deedat mai suna Ko Littafi Mai Tsarki Maganar Allah ne? “Is the Bible God’s Word?” shafi na 6).

Mun ga babban abin mamaki, a ce mutumin da ya nuna kansa a shi babban malamin Islama ne, sai ga shi yana yin irin wannan iƙirari. Ba shakka dole ya san cewa babu gaskiya a cikin maganarsa ko kaɗan. Da farko dai Kur’ani ya ƙunshi sassa da dama da aka rubuta kalmomin annabawan Allah. Alal misali, mun karanta cewa Zakariya annabi ya ce:

“Ya Ubangiji! Yaya yaro zai samu a gare ni, alhali kuwa lalle tsufa ya same ni, kuma matata bakarariya ce? (Suratul Al Imrana 3:40).

Idan kamar yadda Deedat yake faɗa, Kur’ani ya ƙunshi Maganar Allah kaɗai, maganganun annabawa kuwa ana samun su cikin Hadisi kaɗai, zai yi matuƙar wuya ƙwarai a ga yadda za a ce Allah ne ya yi su! Abu na biyu, akwai wani sashi a cikin Kur’ani wanda a sarari ya ƙunshi maganganun mala’iku zuwa ga Muhammadu, ba Maganar Allah ba ce zuwa gare shi kamar yadda ake iƙirari:

(Suna masu cewa)” Kuwa ba mu sauka face da umarnin Ubangijinka ( Muhammadu). Shi ne da mulkin abin da ke gaba gare mu, da abin da ke a bayanmu, da abin da ke a tsakanin wannan.” Kuma Ubangijinka bai kasance wanda ake maimaitawa ba. (Suratu Maryam 19:64).

Babu ko alama cikin Kur’ani a kan ko wane ne yake magana, amma waɗannan maganganu a sarari yake cewa masu yin su suna magana ne kaitsaye da Muhammadu. Daga ayan nan kanta a sarari yake cewa waɗannan maganganun mala’iku ne, ba Allah ba.

Bugu da ƙari kuma mun samu a cikin Hadisi maganganu da yawa waɗanda ba na wani annabi ba ne, amma na Allah ne Kansa. Qudsi (faɗe-faɗen allahntaka) ga misalin wasu a nan:

Abu Huraira ya ruwaito cewa, Annabin Allah (bari salama ta kasance tare da shi) ya ce: Allah, Maɗaukaki Mai Daraja, ya ce: Na shirya wa bayina masu ibada abin da ido ba ya gani, kunne ba ya iya ji, kuma babu zuciyar ɗan adam da za ta iya fahinta irin wata wadata ina barin waɗannan da Allah ya sanar da kai a gefe guda (Sahih Mulim, Kundi na 4, shafi na 1476).

Hadisai suna cike da irin waɗannan maganganun. Bugu da ƙari akwai sassa da yawa daga Kur’ani da Hadisai in an karanta su suna nan kamar na cikin Littafi Mai Tsarki waɗanda ake iƙirari cewa maganganun masana tarihi ne. Wani sashi a cikin Kur’ani da ya ba da labarin haihuwar Yesu daga mahaifiyarsa Maryamu, in an karanta za ka ji daidai kamar “iri na uku” da Deedat ya kwashe a cikin ɗan littafinsa:

Sai ta yi cikinsa, sai ta tsallake da shi ga wani wuri mai nisa. Sai naƙuda ta kai ta zuwa ga wani kututturun dabiniya (Suratu Maryam 19:22,23).

Abin da Kur’ani ya ce a nan a game da Maryamu ba shi da bambanci mai yawa daga labarin da aka ba da a cikin Markus 11:13 a game da Yesu. Amma duk da haka Deedat ya Mori wannan aya daga cikin Markus don misali, yana cewa irin waɗannan labaru ba a samun su a cikin Kur’ani!

Dole mu ƙarasa da cewa, ƙoƙarin Deedat na rarrabe tsakanin Kur’ani da Littafi Mai Tsarki yana kan cikakken zato na ƙarya ne. Kur’ani yana ɗauke da maganganun annabawa, da labarun tarihi a dukan shafukansa, in za a faɗi zahirin gaskiya ba wanda zai ce Kur’ani yana ɗauke da maganganun Allah da na annabawa. Lokacin da Deedat ya ce waɗannan shaidu iri uku - maganganun Allah , da na annabawa, da na masu tarihi – Musulmi sun keɓe su “cike da kishi,” sai ya yi wata magana a ƙaryace - ƙaryar da ɗaya ce daga cikin masu yawa irinta da muka samu daga cikin littafinsa.

Tabbatacce ne tun daga farko cewa gardandamin Deedat gāba da Littafi Mai Tsarki ba su da tushe, haka abin yake cikin dukan littafinsa.

2. RIÄANYAR LITTAFI MAI TSARKI IRI IRI

Deedat ya fara surarsa ta uku da yin musun cewa Littattafan Yahudawa da na Kirista da suka haɗa Littafi Mai Tsarki, ba su ne Kur’ani ya girmama ba a matsayin Attaura da Linjila (Dokoki da Bishara, wato Tsoho da Sabon Alkawari). A maimakon haka, sai ya ce Attaura da Linjila na ainihi gaba ɗaya littattafai ne na dabam waɗanda aka bayyana wa Musa da Yesu bi da bi.

Wannan ƙoƙari na rarrabe tsakanin littattafan Littafi Mai Tsarki da waɗanda ake maganarsu a cikin Kur’ani yana da wuya ma a yi la’akari da shi, ko ta yaya aka ɗauki wannan ra’ayi a duk fāɗin duniyar Musulmi, babu wata shaida ta kowace iri da take goyan bayan wannan.

Babu wani lokaci a cikin tarihi da aka taɓa cewa akwai wani tabbaci cewa an “bayyana” irin waɗannan littattafai na dabam ga Musa da kuma Yesu, ko wata Attaura (Doka) ko Linjila (Bishara) baya ga Tsoho da Sabon Alkawari da ake da su tun asali. Bugu da ƙari, kamar yadda za mu nuna, Kur’ani kansa bai rarrabe waɗannan littattafai daga Littattafai Masu Tsarki ba na Yahudawa da na Kirista, amma ya yi akasin haka, a sarari ya yarda cewa su ne littattafan nan waɗanda Yahudawa da Kirista kansu suka riƙe su zama maganar Allah.

Cikin ƙoƙarin da Deedat yake yi don ya nuna cewa lalle akwai wasu Attaura da Linjila baya ga waɗanda suke cikin Littafi Mai Tsarki, babu makawa ya fāɗi warwas. Sai ya yi ta faffaka “Mu musulmi mun gaskata . . . mun gaskata . . . da gaske mun gaskata . . . amma ya kāsa samar da ko da ɗan ɓarɓashin abin da yake shaidar da ya goyi bayan waɗannan gaskatawan. Abin mamaki, sai ga shi yana tabbatar da laifinsa na ainihin “wawanci” da ya ɗora wa Kirista a cikin ɗan littafinsa (duba shafi na 3 a cikin ɗan littafin nasa).

Abin da za mu iya cewa don maida martani ga waɗannan ƙagaggun gaskatawa shi ne, dukan abin shaida na tarihin suna gāba da waɗannan ƙage-ƙage, dukansu kuma tsantsar zace-zace ne, fanko marasa tushe. Dole ne mu yi shirhi cewa, bisa ga iƙirarin Deedat mai cewa Allah kansa ya kiyaye Kur’ani daga karambanin ɗan adam har tsawon ƙarni goma sha huɗu (a ɗan littafin mai suna a Turanci: “Is the Bible God’s Word?” shafi na 7) zai zama abin mamaki a ga cewa shi Allahn da ya kiyaye Kur’ani yanzu ya kāsa, ko da gaskiyar labarin cewa Attaura ko Linjila sun taɓa kasancewa balle ya kiyaye littattafan kansu! Yana da wuya ƙwarai a gare mu mu iya yarda da wannan rikitacciyar rashin gaskiya, a ce madawwamin Mai mulkin dukkanin duniya ya yi abu kwan gaba kwan baya a dukan lokatan nan. Ai, ba za ka sa zuciyar ganin mu mu yarda cewa Allah cikin mu’ujiza ya kiyaye ɗaya daga cikin littattafan nan daidai ba, amma ya zama marar ikon kiyaye ko da labarin kasancewar sauran littattafan ba a cikin tarihin ɗan adam. Wannan zai yi mana wuyar haɗiyewa ƙwarai da gaske.

A cikin kowane al’amari, kamar yadda muka riga muka gani, Kur’ani kansa ya fito muraran ya tabbatar da cewa Attaura ta Yahudawa littafi ne kamar yadda yake a zamanin Muhammadu, haka kuma Linjila littafi ne da Kirista suke da shi a wancan lokaci wanda su da kansu suka ɗauka maganar Allah ne. A cikin dukan lokacin tarihi babu lokacin da Yahudawa da Kirista suka ɗauki wasu littattafai dabam don su zama Maganar Allah Tsattsarka baya ga waɗannan da ke cikin Tsoho da Sabon Alkawari yadda muka san su a yau.

A zamanin Muhammadu, Yahudawa a duk fāɗin duniya sun san Attaura guda ɗaya kaɗai – littattafan Tsohon Alkawari kamar yadda suke daidai a yau. Haka kuma yake ga Kirista, sun san Linjila – littattafan Sabon Alkawari, suna nan daidai kamar yadda suke a yau. Akwai ayoyin (Matanin) Kur’ani masu amfani ƙwarai da gaske wajan tabbatar da wannan batu; ga su nan:

Kuma yaya suke gabatar da kai ga hukunci, alhali a wurinsu akwai Attaura, a cikinta akwai hukuncin Allah? (Suratul Maida 5:430).

Kuma sai mutanen Injila su yi hukunci da abin da Allah ya saukar a cikinta. (Suratul Maida 5:47).

Ba zai taɓa yiwuwa ba a ce Kirista na zamanin Muhammadu za a hukunta su da Linjila idan ba su da ita a hannunsu. A cikin Sura ta 1:157 Kur’ani ya yarda cewa, Attaura da Linjila waɗanda Yahudawa da Kirista suke da su a zamanin Muhammadu su ne littattafan da ƙungiyan nan biyu su da kansu su ka karɓa wato Doka da Bishara bi da bi. Babu wanda zai ce waɗannan littattafai biyu wasu ne dabam ba Tsoho da Sabon Alkawari ba ne kamar yadda aka same su a cikin Littafi Mai Tsarki a yau.

Bugu da ƙari, abu mafi muhimmanci ne a lura cewa, wasu fitattun masharhanta kamar su Baidawi da Zamakshari a sarari sun yarda cewa Linjila ba ainihin kalmar Larabci ba ce, amma an yi aron ta ne daga kalmar Suriyanci wadda Kirista da kansu suka mora wajen bayyana Bishara (Linjila). Ba shakka, haka ma wasu masanan Kur’ani na farko suka yi ƙoƙarin gano asalinta na Larabci, waɗannan mutum biyu ƙwararru ba su yarda da wannan ba, sun ƙi ba tare da ƙumbuya-ƙumbuya ba (Littafin Jeffery mai suna a Turance “The Foreign Vocabulary of the Qur’an” Wato baƙin kalmomi na Kur’ani, shafi 71). Wannan yana ƙara tabbatar da watsi da batun nan mai cewa Linjila ba ainihin littafin da aka saukar wa Yesu ba ne, dukan baƙin bincike-bincike sun tsuce amma sai Sabon Alkawari kansa na ainihi kamar yadda muka san shi a yau. Haka kuma yake ga Attaura wadda kalma ce ta ainihin Ibrananci, sunan da kuma Yahudawa da kansu a koyaushe suke kiran littattafan Tsohon Alkawari da shi kamar yadda muka san Attaura a yau.

Saboda haka, ba tare da wasu ɓoye-ɓoye ba Kur’ani ya yarda cewa Littafi Mai Tsarki kansa maganar Allah ne da gaske. Deedat ya san gaskiyan nan, don haka ya ke ƙoƙarin karkatar da wannan gaskiya ta wurin cewa akwai “riɓanyar” Littafi Mai Tsarki iri-iri da ke ko’ina a duniya a yau. Wannan duk mugun wayo ne na karkatar da gaskiyar al’amari.

Ya kāsa sanar da masu karatunsa cewa yana magana ne a kan juyawa iri-iri cikin Turanci da suke shiga ko’ina a cikin duniya a yau. Suna nan cikin Turanci iri-iri kamar yadda kuka sani, amma a ƙashin gaskiya, ya kamata ya fayyace wa makarantansa cewa waɗannan ba wasu littattafai masu Tsarki ba ne dabam, juyi ne kawai cikin Turanci iri-iri na Littafi Mai Tsarki: (KJV; RV; RSV). Dukansu uku daga ainihin harsunan Ibrananci da Hellenanci ne nassoshin Tsoho da Sabon Alkawari bi da bi, waɗanda Ikilisiyar Kirista ta kiyaye su cif tun ƙarni da dama kamin zamanin Muhammadu. Haka mu kuma muna iya la’akari da bambamce-bambace a tsakaninsu, amma zai zama da amfani idan muka duba irin hargowar da ta taso a tsakankanin shugabannin Musulmi na Afrika ta kudu a 1978 saboda rabar da juyin Kur’ani cikin Turanci wanda Muhammad Asad ya yi. (Kamar Littafi Mai Tsarki, akwai juyi da dama iri-iri na Kur’ani a cikin Turanci kuma).

Tofin Allahtsine da aka yi ta yi wa juyin Asad ya yi ƙamari har sai da Majalisar Islama ta Afrika ta Kudu ta fito ƙarara ta yi furci a bainar jama’a suka hana rarrabar da wannan littafi a cikin Musulmin Afrika ta Kudu. Ba a taɓa yi wa juyin Turanci na Littafi Mai Tsarki irin wannan cin zarafi ba. Saboda haka, kada makaranta na Deedat a shammace su da maganarsa ta ruɗi cewa akwai “riɓaniyar” Littafi Mai Tsarki, kuma ya kamata su yaba wa wannan bayani mai kware lulluɓin da ya rufe idanun makaranta na Deedat mai cewa Ikilisiyar Kirista ba Littafi Mai Tsarki ɗaya kaɗai take da shi ba.

3. AFOKIRIFA

Daga nan Deedat ya ci gaba da tafka wani zargi na ƙarya inda ya ke cewa ’yan Protestant sun soke littattafai bakwai gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki (ɗan littafin Deedat mai suna “Is the Bible God’s Word?” a shafi na 9), littattafan da suka zama Afokirifa. Akwai alamar cewa ya sami karkataccen bayani a kan Littafi Mai Tsarki a game da littattafan nan da suke daga asalin Yahudawa, marubutansu kuma ba su taɓa niyyar rubuta maganar Allah ba, wato Tsohon Alkawari wanda mu Kirista muka yarda maganar Allah ne. Saboda haka, ba soke su aka yi ba daga Littafi Mai Tsarki kamar yadda Deedat yake zargi a karkace. Roman Katolika ne kaɗai suka ba littattafan nan ikon zama maganar Allah saboda wasu dalilai na kansu da suka fi kowa sani.

4. “MUMMUNAN LAHANI”

Tare da irin zafin ran da ya saba, Deedat yana ƙalubalantar Kirista mai bi da ya jira dèka mafi girma na rashin kirki da zai far masa ko da shike gaba ɗaya ba mu san abin da ya ke shirin faɗi ba. Ya ɗauko kalmomin nan daga gabatarwar RSV waɗanda aka ja layi a ƙarƙashinsu a cikin ɗan littafinsa:

Juyin King James yana da mummunan lahani . . . waɗannan lahani suna da yawa kuma da zafi ƙwarai har dole sai an sāke juyin.

(ɗan littafin Deedat mai suna “Is the Bible God’s Word?” shafi na 11)

Waɗannan kalmomi ba lahani ba ne, ba kome ba ne kuma, bambamci ne kawai cikin karanta su, waɗanda masu juyawar ba su sani ba, wato waɗanda suka haɗa KJV tun cikin ƙarni na goma sha bakwai. Juyin RSV kuwa na wannan ƙarni ya gano waɗannan karatun, an kuma sa su a matsayin matuni a shafukan da suka dace na mataninsu. Bugu da ƙari kuma a aya kamar 1Yahaya 5:7 a cikin KJV (domin masu juyin sun ɗauko ta daga kundaye na daga bisani). RSV kuwa ya tsallake ta gaba ɗaya (domin ba su sami ayar ba a cikin daɗaɗɗun matanin Sabon Alkawari cikin Hellenencin ainihi).

Da fari dai dole mu ƙara nuna cewa KJV da RSV juyi ne zuwa Turancin Inglishi daga Hellenanci na ainihi, yadda aka kiyaye su domin mu, ba su da wata sākiya ko alama. (Muna da wajen matani 4000 na Hellenanci waɗanda suna nan tun wajen shekara ɗari biyu kafin ɓullowar Muhammadu da Islama).

Abu na biyu, babu wani canji na kowane iri a cikin tsari, da koyarwa ko cikin rukunan Littafi Mai Tsarki cikin juyin da ake magana a kai. Cikin dukanin KJV, da RSV, da sauran juye-juye na harshen Turanci, ainihin Littafi Mai Tsarki da dukan abin da ya ƙunsa, ko alama babu canji.

Abu na uku, waɗannan ba mabambantan juyin Littafi Mai Tsarki ba ne. Mun ji ana cewa akwai “Kur’ani ɗaya tak” Kirista kuwa suna da Littafi Mai Tsarki iri-iri dabam dabam. Wannan kwatanci na waɗannan juyi bai shiga ba, ƙarya ce zallanta. Akwai bukatar mu ƙara faɗi, juyin Turanci ne kaɗai daga matanin Ibrananci da Hellenanci na ainihi. Akwai irin waɗannan juye-juyen na Kur’ani zuwa Turanci, amma ba wanda ya ce waɗannan juye-juyen sun bambanta Kur’ani ya zama iri-iri dabam dabam. Haka yake a gare mu muna da juyi da dama cikin Turanci, amma kamar yadda gaggawar kwatanta waɗannan nan da nan zai nuna, muna da Littafi Mai Tsarki guda ɗaya tak.

A Sarari yake cewa mun yarda akwai bambancin hanyar karantu a cikin Littafi Mai Tsarki. Mun gaskata cewa, a matsayinmu na Kirista, kasancewa ma su yi da gaskiya a kowane lokaci lamirinmu ba zai bar mu mu kauce wa gaskiya ba, ba kuma za mu gaskata kowane irin abu da za a cim ma wa ba ta wurin ruɗi mu ce ai babu irin waɗannan bambanci a cikin karatu.

A akasin wannan, ba mu ɗauki waɗannan bambancin karatu cewa tabbaci ne mai nuna an canja Littafi Mai Tsarki ba. Ɗan lahanin da ke nan bai taka kara ya karya ba a littafin, hakika, ba ma za mu bi ta kansu ba, mun sani muna iya amincewa, da dāgewa a kan cewa, Littafi Mai Tsarki, dukaninsa, cif yake, ba a kuma taɓa canja shi ba ko da ƙaƙa.

Ba mu daina mamaki a kan irin iƙirarin da Musulmi suke yi ba cewa, ba a taɓa canja Kur’ani ba, Littafi Mai Tsarki kuwa wai an daddagula shi, har ba kamar yadda yake tun da fari ba, yanzu ma ba maganar Allah ba ne. Dukan shaidar da tarihi ya kawo mana suna nuna cewa duka littattafan biyu Kur’ani da Littafi Mai Tsarki suna nan cif-cif cikin yadda suke tun asalinsu yadda a ka rubuta su, ko wannan ma ba a kāsa samun wasu ’yan bambamce bambance na karatu nan da can ba cikin wasu matani. Muna iya ɗauka cewa yaudarar cewa Kur’ani ba shi da kuskure, Littafi Mai Tsarki kuma an daddagula shi, muna ɗauka cewa tatacciyar ƙarya ce. Attaura da Linjila dai tabbatace ne ainihin na Kirista ne ba na Islama ba cikin abin da suke ɗauke da kuma abin da suke koyarwa. Ko mene ne dalilin wannan irin yamutsi dai, mu mun sani gaskiya ce mu ke faɗa a duk lokacin da muke faɗin cewa, Kur’ani ba shi da canji alhali kuwa an sassāke Littafi Mai Tsarki sau da dama, wannan ƙarya ce aka shara wadda babu irinta cikin sunan gaskiya.

Lokaci ya yi da manyan malaman Musulmi a duniya duka da za su fito su faɗi gaskiya ga almajirai da ɗalibansu. Akwai ɗunbin shaida masu nuna cewa, lokacin da Halifa Uthman ya tattara rubutun Kur’ani da fari cikin matsayin matani guda, akwai masu yawan gaske da suke ɗauke da bambance-bambancen karatu. A zamanin mulkinsa, sai aka kawo masa rahotanni cewa, a wasu sassa na ƙasar Syria, da Armenia, da kuma Iraki, Musulmi suna karanta Kur’ani dabam da yadda ake yi a ƙasar Sa’udi Arabia. Nan da nan sai Uthman ya yi umarni a tattaro kundin Kur’anin dake a wurin Hafsah (ɗaya daga cikin matan Muhammadu, wadda take ’yar Umar ce), ya kuma umarci Zaid-b-Thabit da wasu mutum uku da su yi wasu kofe na wannan kundin Kur’anin, su yi gyaran da ya dace. Bayan an kammala wannan aiki, mun karanta cewa Uthman ya ɗauki tsattsauran mataki dangane da sauran kundayen Kur’ani da suke akwai:

Uthman ya aika da kofen Kur’aninsa guda zuwa kowane lardi na Musulmi, ya kuma Umarta a tattaro dukan sauran kofe ko kundayan Kur’ani waɗanda ba shi ya gyara ba don a ƙone su ƙurmus. (Sahih al-Bukhari, Kundi na 6, shafi na 479).

A cikin tarihin Kirista ba a taɓa samun mutumin da ya ƙuduri daidaita Littafi Mai Tsarki ya zama kofe guda yadda ya ke so ba, har kuma ya yi ƙoƙarin ƙone dukan sauran Littattafai masu Tsarki. Don me Uthman ya yi irin wannan umarni dangane da sauran Kur’ani da suke wurare dabam dabam? Za mu iya ɗauka cewa don ya gaskata sun ƙunshi “munanan lahani” masu “yawan gaske har ba za a iya kira” don a yi gyaransu ba, sai dai a ƙone su ɗungurungun. Muna iya cewa, idan muka kintata mahallin tarihin Kur’ani yadda yake, za mu sami cewa Kur’anin da aka daidaita ya zama na daidai shi ne wanda mutum (ba Allah ba), bisa ga yadda ya ga ya yi masa kyau (ba bisa ga wahayi ba), ya zartar da umarni wannan ne na gaskiya. Mun kāsa gane ta wane dalili wannan kofe ne kaɗai ya zama cikakke da ake iya samu, kuma a ɗan lokaci kaɗan ya samar da abin shaida cewa kundin Ibn Mas’ud yana iƙirari a shi ne mafi duka da ake iya samu. (Babu shakka, ba wanda za a iya ɗauka a matsayi cikakke saboda bambancin karance-karance masu yawa da suke a tsakaninsu).

Babu wata tantama, a aikace yake cewa babu wani Kur’ani dake akwai wanda ya yi daidai da na Hafsah, domin dukan sauran an yi umarni da a ƙone su duka ƙurmus. Wannan irin shaida babu wata shakka, babu yadda za ta iya kāre iƙirarin nan marar gaskiya mai cewa, ba a taɓa canja Kur’ani ba ko ta ƙaƙa.

Da fari dai, akwai wata shaida marar makawa mai cewa, wannan Kur’ani ma da aka tace, ba shi da wani lahani ko kaɗan. A cikin wasu ayyuka na Hadisin Islama da aka fi girmamawa mun karanta cewa ko bayan da aka aikar da kofen wannan Kur’ani, sai ainihin wannan mutum, Zaid ya tuno da wata aya da ta ɓace. Ya shaida kamar haka:

Ayar Surutul Ahzab ce ta ɓace mini lokacin da muke kofe Kur’ani, na kuma ji Manzon Allah yana faɗin ta. Don haka muka bincika muka same ta tare da Khuzaima-bin-Thabit al Ansari. (Sahih al-Bukhari, Kundi na 6, shafi na 479).

Ayar ita ce Suratul Ahzab 33:23, Saboda haka, idan ma za a gaskata shaidar (babu kuwa wani abin jayayya), babu wani Kur’ani a wancan lokaci da Uthman ya ke kammalawa da yake cikakke. Abu na biyu kuma shi ne, akwai wata shaida mai kama da wannanm har zuwa yau, akwai ayoyi, har ma da wasu sassa gaba ɗaya da har yanzu sun ɓace daga cikin Kur’ani. An faɗa mana cewa, a zamanin mulkin Umar a matsayin Halifa cewa wasu ayoyi da suka danganci jajjefewa saboda zina an ji Muhammadu yana faɗar su, sashin Kur’ani ne a zamanin rayuwarsa:

Allah ya aiko Muhammadu, ya kuma aiko masa Littafi. Ɗaya daga cikin sashin da ya aiko akwai na jajjefewa, mun karanta shi, an koya mana shi, mun kuma saurare shi. Manzo ya yi jifa, mu kuma mun jajjefe su a bayansa. Ina jin tsoro, a zamani na gaba mutane za su ce ba su ga inda aka ambaci jajjefewa ba a cikin littafin Allah, don haka suka ɓace cikin ratsewa daga farillar da Allah ya saukar. Hakika, a cikin littafin Allah akwai hukuncin jajjefewa a kan maza da mata da aka kama da laifin zina. (Ibn Ishg, Sirat Rasulullah, shafi na 684).

Wannan ya zama fayyatacciyar shaida mai nuna cewa, a yadda Kur’ani yake a yanzu haka, ko kaɗan ba “cikakke” ba ne, da shike har yanzu babu aya a cikin matani a kan jajjefewar mazinata. Mun sami ƙarin shaida a kan wannan a cikin wani sashi na Hadisi cewa, akwai wasu ayoyi da wasu sassa waɗanda a dā sashi ne na Kur’ani, amma yanzu babu su a cikin matani. A sarari yake, cewa, ainihin kundin Kur’ani da ke akwai a duniya yau ba shi ne na tun farko ba.

Komawa ga matani waɗanda aka ƙone, za mu ga a kowane hali akwai bambamce-bambance da dama a tsakaninsu da matanan da Uthman ya amince da su bisa ga yadda ya ga ya dace su zama, su ne na daidai da zama Kur’ani mafi kyau duka. Bugu da ƙari, waɗannan bambance-bambance ba na karin harshe zalla ba ne kamar yadda ake iƙirari. Sau da dama mun gane cewa “ainihin bambamcin matani ne, ba batun karin harshe ne kawai ba” (Jeffery, The Qur’an as Scripture).

A wasu fannoni akwai bambancin baƙaƙe a cikin wasu kalmomi, a waɗansu kuwa bambancin ya shafi dukan sheɗara, nan da can akwai kalmomi da sheɗaru cikin wasu kundayen da aka tsallake, ko aka bari ba a same su a cikin sauran ba. Bambance-bambancen nan sun shafi kundaye goma sha biyar.

Yanzu sai mu yi la’ikari da matanin Abdulllah ibn Mas’ud. (Abin da ake faɗa a game da kundinsa gaba ɗaya ya shafi sauran kundayen da aka ƙone bisa ga umarnin Uthman). Mataninsa ne jama’ar Kufa suka riƙe hukumance a shi ne Kur’aninsu na ainihi sa’ad da Uthan ya fara ba da umarni a ƙone dukan kundayan Kur’ani in banda kundin da ke hannun Hafsah, har wani tsawon lokaci Ibn Mas’ud bai yarda ya rabu da nasa kundin ba, sai ya zama nasa yana gāsa da kundin Hafsah a hukunmance.

Ibn Mas’ud shi ne na farko cikin Musulmi, kuma ɗaya daga cikin malaman farko da suka koyar da karatu da haddacen Kur’ani. Ba shakka, a ko’ina an girmama shi a zaman wanda ya fi duka sanin matanin Kur’ani. A wani lokaci sai da ya hadacce surori fiye da sabia’in na Kur’ani a gaban Muhammadu, ba wanda ya sami kuskure cikin shahararrun hadisai da ake girmamawa na Iman Muslim muna karanta cewa:

Bisa ga rahoton Masruq: Sun ambaci Ibn Mas’ud a gaban Abdullah b. Amr inda ya ce: Shi mutum ne wanda a koyaushe ƙaunarsa tana nan sabuwa ce a zuciyata bayan na ji manzon Allah (bari salama ta kasance tare da shi) yana cewa: Ku koyi hadacce Kur’ani daga mutum huɗu: daga Ibn Mas’ud, Salim, wanda ke haɗe da Abu Hudhaifa, Ubayy b. Ka’b, da kuma Mu’adh b. Jabal. (Sahih Muslim, kundi na 4, shafi na 1313)

Bisa ga aikin wani Hadisi, an ce wannan Ibn Mas’ud yana nan a lokacin da aka ce Muhammadu yana hadacce Kur’ani tare da Jibra’ilu kowace shekara (Ibn Sa’d, Kitab al-Tabagat al-Kabir kundi na 2, shafi 441). Cikin wani hadisi mai kama da wannan mun karanta cewa, Muhammadu ya ce:

Ku koyi haddace Kur’ani daga mutum huɗu: Abdullah bin Mas’ud – ya fara da shi – Salim, wani ’yantaccen bawa na Abu Hudhaifa, Mu’adh bin Jabal, da kuma Ubai bin Ka’b. (Sahih al-Bukhari, kundi na 5, shafi na 96-97).

Ƙananan rubutun nan sharhi ne na mai kawo rahoton hadisi, sunansa Masruq. Sun nuna cewa, dukan Musulmin wancan lokaci, Ibn Mas’ud shi ne masani mafi duka a kan Kur’ani.

Akwai labarin bambance-bambancen Karatu da dama a cikin kundayen Salim duk da na Ubai Ka’b da suke a nan, amma kamar yadda aka ware na Ibn Mas’ud ya zama na musamman, Muhammadu da kansa ya ware shi, to, abin mamaki ne a gane cewa mataninsa ya bambanta da sauran (Har da na Hafsah) sau da dama irin wannan bambanci cikin karatu an same su daga cikin shafi fiye da tasa’in na littafin Arthur Jeffery inda ya tattara karatun da suka bambanta da juna a cikin kundaye iri iri (Littafin Jeffery, mai suna a Turance. Materials for the History of the Text of the Qur’an, shafi na 24 - 114). Marubucin ya samo abin shaidarsa daga wurare masu yawa na Islama da suke rubuce a cikin littafinsa. A cikin Sura 2 kaɗai ba za su kāsa 149 ba, inda mataninsa ya sha dabam da na sauran da ake aiki da su, musamman ma na Hafsah.

Bugu da ƙari, ɗaya daga cikin dalilan da suka sa ya ƙi rabuwa da nasa ya ɗauki na Hafsah shi ne, matani na daga bisani Zaid-b-Thabit ne ya haɗa shi, shi kuwa har yanzu yana a ƙarƙashin mara bi ne lokacin da ya riga zama ɗaya daga cikin waɗanda suka fi zama na kurkusa da Muhammadu.

Abu biyu suka wakana daga wannan duka. Na fari, wannan ya nuna cewa matanin Mas’ud yana da tushe fiye da na Hafsah cikin kofen Kur’anin da suke akwai a yau – musamman ma da shike Muhammadu ya shaide shi da zama na fari daga su huɗu da suka fi goguwa a game da sanin Kur’ani. Abu na biyu kuwa shi ne, akwai ɗumbin bambance-bambancen karatu tsakanin matanin nan guda biyu - sun kai dubbai, dukaninsu suna nan a rubuce cikin littafin Jeffery.

Don ƙarin tabbaci, akwai wajen dozin na kundayan farko na wasu fitattun mutane kamar su Salim, da Ubai bin Ka’b, waɗannan sun bambanta ƙwarai da gaske daga matanin Hafsah kanta (sau da yawa sukan yarda da matanin Ibn Mas’ud a maimakon sauran!), bisa ga waɗannan shaidu, muna iya ƙarshewa da ƙin yarda da batun ruɗin nan mai cewa babu tabbas da ke nuna cewa an taɓa canja Kur’ani. Littafin Jeffery ya ƙunshi shafi 362 na tabbatattun shaidu masu nuna mafiya yawan kundayen Kur’ani na farko sun bambanta ƙwarai da gaske tsakaninsu da juna ta hanyoyi dabam dabam. Saboda haka Kur’ani ma ya sha fama da bambance-bambancen karatu, kuma ba yadda za a ce mutum amintacce wanda lamirinsa yake sarai a gaban Allah ya yarda cewa Kur’ani ba shi da “mummunan lahani” a cikin tarihin mataninsa yadda kuma aka samu cikin tarihin matanin Littafi Mai Tsarki. Wannan duk dabara ce ta mugun wayon ruɗi na karkatar da ainihin gaskiya.

Gaskiyar ita ce, tarihin matanin Kur’ani ya yi kama da na Littafi Mai Tsarki (Guillume, Islam shafi na 58). Duka littattafan biyu an kiyaye su da kyau. kowannensu yana nan daidai yadda aka yi shi, kuma abin da kowanne ya ƙunsa yana nan yadda aka rubuta tun da farko. Amma ba ɗayansu da ya rasa kuskure ko lahanin matani. Dukansu sun sha fama da bambance-bambancen karatu a cikin kundayen da muka sani, kuma ko ta halin ƙaƙa ba wanda aka dagula. Kirista da Musulmi na ainihi za su san wannan gaskiyar.

Bambancin dake nan kaɗai da ke tsakanin Kur’ani da Littafi Mai Tsarki a yau shi ne, Ikilisiyar Kirista, ta tsare gaskiya, ta kiyaye/tsare bambance-bambancen karatu da ke cikin matanin Littafi Mai Tsarki; Musulmi kuwa a zamanin Uthman ya ga ya dace a ɓatar da dukan wasu shaidu masu nuna bambance-bambancen karatu da sunan tsayar da tabbataccen kundi guda ɗaya tak domin dukan duniyar Musulmi. Zai yiwu akwai matani guda ɗaya na Kur’ani da ake aiki da shi kaɗai a yau, amma ba wanda zai iya iƙirari a ƙashin gaskiya cewa shi ne Kur’anin da Muhammadu ya danƙa wa abokansa tun asali. Babu wanda ya taɓa nuna dalilin da ya sa kundin Hafsah ya zama marar kuskure, kuma aka ɗauke shi abin shaida, a akasin wannan kuma aka ɗauka cewa kundin Kur’ani na Ibn Mas’ud shi ne mafi daidai fiye da kowanne da ake da shi. Waɗannan tabbaci ya kamata a koyaushe a yi la’akari da su dangane da tushen ƙarin shaidun da ke cikin Hadisi masu cewa, har yanzu Kur’ani da ake da shi a yau ba cikakke ba ne.

Cewa dukan kundayen Kur’ani da ake da su a duniya a yau daidai da juna suke, ba zai yi taimako ba. Ƙarfin ɗaurin yana da ƙarfi kaɗai daidai da rashin ƙarfin mahaɗin - rarraunan mahaɗin a cikin maɗaurin tarihin kundin Kur’ani an same shi a daidai wurin nan, inda a mayuwatan kwanakin nan na farko, aka sha fama da bambance-bambancen kundayen Kur’ani da ake da su a zamanin can, an kuma ba da wani abin shaida cewa ƙarshe an daidaita matsayin Kur’ani ya zama guda ɗaya mafi kyau, amma har yanzu bai zama cikakke ba ko kaɗan.

Sai waɗanda kaɗai ba su ƙaunar gaskiya, ba su kuma martaba abubuwan shaidu da suke akwai na gaskiya, su za su yi iƙirarin cewa an degular da Littafi Mai Tsarki, Kur’ani kuwa ba a taɓa yin wani canji a cikinsa ba. Irin mutanen nan zai yiwu suna ƙaunar yin shayin cewa an cika imaninsu kawai da dagulalliyar gaskiya. Amma Allah, wanda yake na gaskiya, wanda kuma yake gaskiya, hakika, zai kafa fuskarsa gāba da farfagandarsu marar gaskiya.

5. KURAKURAI GUDA DUBU HAMSIN?

Deedat ya kwaso daga abin da aka rubuta cikin wata mujalla mai suna “Awake” (wato Farkawa), an wallafa ta shekara ashirin da uku da suka gabata, ƙungiyar Jehovah’s Witnesses ne suka wallafa ta (ba ɗarikar Kirista ba ce, amma ƙarama ce ta tsafin asiri) wadda ita ma ta kwaso daga wata mujalla mai suna “Look” (wato Duba) mai cewa akwai wasu “almajiran zamani” masu cewa akwai “Kurakurai 50,000 a cikin Littafi Mai Tsarki”.

Wani muhimmin abu a game da wannan shi ne, ba a ambaci wata shaidar kasancewar waɗannan almajirai na wai-wai ba, ko wata ’yar alamar shaida ta samfurin wannan zargi na ɗumbin kurakurai. Muna iya ɗauka kaɗai cewa, wannan zargi daɗin baki ne zalla, da kuma ƙage daga matsananciyar gāba da Littafi Mai Tsarki da dukan abin da yake koyarwa.

Abin baƙin ciki shi ne, masu jin wannan ƙiyayyar, ƙi da so suna yarda da kowane abin da yake gāba da Littafi Mai Tsarki – kome rashin gaskiyar abin. Haka Deedat yake ɗauka kamar abin da aka tabbatar da gaskiyarsa; kome ya karanta gāba da Littafi Mai Tsarki ba ya ƙoƙari ko kaɗan ya tantance abin. Ya yi mana wuya mu ɗauke shi mai faɗar gaskiya a lokacin da yake cewa:

Ba mu da lokaci ko filin da za mu bi cikin dubun dubban manya ko ƙananan lahanin da marubutan RSV suka yi ƙoƙarin gyaggyarawa. (Ɗan littafin Deedat mai suna a Turance “Is the Bible God’s Word?” Ko Littafi Mai Tsarki Maganar Allah Ne? shafi na 14).

Wannan yana nufin ke nan cewa Deedat bai san dubun dubban kurakuran da ke cikin Littafi Mai Tsarki ba. Daga cikin kurakurai dubu hamsin da ake zargi, Deedat ya samr da guda huɗu da za mu yi la’akari da su. Yanzu dole mu ɗauka cewa mutum irin wannan mai zargin akwai tulin kurakurai da ya samu haka, sai guda huɗu kacel zai iya tabbatarwa su zama shaida na jimlar kurakuran da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Hakika, mun isa mu yi zaton cewa waɗannan misali huɗu da ya ba da, su kaɗai ne iyakar abin da zai iya samarwa. Bari mu auna su.

a) Na fari – “kuskure” – wanda aka fi zato a cikin Littafi Mai Tsarki shi ne zargin da su ke yi a cikin Ishaya 7:14:

“Ubangiji fa da kansa zai ba ku alama; duba, budurwa za ta yi juna biyu, za ta haifi ɗa, za ta kira sunansa Immanuel” (Ishaya 7:14). (Tsohon Juyi).

{Wannan gardama tana cikin na Turanci ne, babu damuwa cikin na Hausa}. KJV ya ce “Budurwa” RSV kuwa ya ce “Yarinyar mace” za ta yi ciki (juna biyu) – (cikin sabo da Tsohon juyi na Hausa babu damuwa domin an ambaci budurwa wanda babu shakka ana nufin budurwa wadda ba ta kai ga yin aure ba, balle fa ta san namiji). Bisa ga ra’ayin Deedat wannan ya zama kuskure mafi girma a cikin Littafi Mai Tsarki.

A cikin ainihin Ibrananci ana kiran kalman nan ta budurwa “almah” – kalmar da aka samu a cikin kowane matani na littafin Ishaya. Saboda haka babu canji na kowane iri a cikin matani na ainihi. Matsalar dai ta tafinta ce da kuma juyi daga wannan harshe zuwa wancan zalla. Kalmar da aka fi mora domin budurwa ita ce “bethulah” Kalmar “almah” kuwa tana nufin yarinyar mace – a koyaushe ana nufin yarinyar da ba ta yi aure ba. Saboda haka juyin RSV daidai yake babu wani muni. Amma kamar yadda yake a koyaushe, juyi zai yi ƙoƙari ya fito da ainihin ma’ana a sarari na ainihin kalmar, mafi yawa na juyin Turanci sun juya kalmar zuwa budurwa. Dalilin shi ne, mahallin kalmar ya bukaci irin wannan tafintar (fassara). (Musulmin da suka juya Kur’ani zuwa Turanci sun sha fuskantar irin waɗannan matsaloli da matanin ainihi na Larabci. Zahirin karatun kalma ko matani yana iya rasa ma’anar da ke cikin ainihin harshen).

Ɗaukar juna biyun yaron alama ce za ta zama ga Isra’ila. Yanzu kuwa babu wata alama daga ɗaukar juna biyu na macen da ba ta yi aure ba. Irin wannan abu sananne ne a ko’ina cikin duniya. Alamar a sarari take cewa budurwa za ta yi juna biyu ta kuma haifi ɗa. Wannan zai zama ainihin alama, don haka shi ne lokacin da Yesu Almasihu ya cika wannan annabci ta wurin yadda aka ɗauki cikinsa (juna biyu) ta wurin Budurwa Maryamu.

Ishaya ya mori kalmar “almah” a maimakon “bethulah” domin “bethulah” ba tana nufin budurwa kaɗai ba, amma kuma tana nufin wadda mijin budurcinta ya rasu (kamar yadda yake a cikin Joel = Yowel 1:8). Waɗanda suka juya kalmar zuwa yarinyar mace (Kamar yadda yake a cikin RSV) suna ba da zahirin ma’ana daidai da ta masu juya kalmar a matsayin budurwa (yadda yake a cikin KJV) sun ba da ma’ana daidai cikin mahallin. Kowace kalma aka faɗa yarinyar mace budurwa ce kamar yadda Maryamu take lokacin da ta ɗauki cikin (juna biyu) Yesu. Matsalar ta taso ne daga juyi da fassara daga ainihin Ibrananci zuwa Turanci. Babu abin da ya taɓi ainihin mutuncin mahallin Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, iƙirarin Deedat ya fāɗi ƙasa warwas.

b) Mataninsa na biyu shi ne Yahaya 3:16 mai cewa (kamar yadda yake a cikin Tsohon Juyi):

“Gama Allah ya yi ƙaunar duniya har ya ba da Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana ba da gaskiya gare shi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada” (Yahaya 3:16).

A cikin juyin RSV Turanci, muna karanta cewa ya ba da makaɗaicin Ɗansa, sai Deedat ya ce an tsallake kalman nan “haifaffe” wannan yana tabbatar da cewa an sassāke Littafi Mai Tsarki. Har yanzu, a nan ma maganar tafinta ne da juyi daga ainihin Hellenanci wadda take nufin mabambanci. Ko ta yaya babu wani bambanci tsakanin “makaɗaicin Ɗa” da “Ɗa haifaffe kaɗai” domin duka juyi ne da ya dace na ainihin Hellenanci, suka fito da batu guda: Yesu mabambancin Ɗan Allah ne. (Ba mu iya ganewa da iƙirarin Deedat ba mai cewa RSV ya kawo Littafi Mai Tsarki kurkusa da Kur’ani, ga shi kuwa yana musun cewa Yesu Ɗan Allah ne. A cikin juyin RSV, gaskiyar cewa ba shakka shi mabambancin Ɗan Allah ne an ƙarfafa shi cikin manufar da take cikin juyin KJV). Muna bukatar ƙara ƙarfafa cewa babu canji ko kaɗan cikin matanin Hellenanci, matsalar dai ta tafinta da juyi ne zalla. Saboda haka iƙirarin Deedat na biyu shi ma ya fāɗi ƙasa warwas.

Muna iya ƙara misalta batunmu ta wurin yin magana a kan abin da Deedat ya ɗauko daga Kur’ani Sura 19:88 inda muke karanta cewa Kirista suna cewa Allah mafi jinƙai ya haifi Ɗa. Ya ɗauko wannan daga juyin Kur’ani na Yusuf Ali. Yanzu a cikin juyin su Ricktehall, da Muhammad Ali da Maulana Daryabadi, mun duba, ba mu sami kalma haifa ba, amma akwai ta ɗauka. Idan za a yarda da irin tunanin Deedat, to, shaida ta samu ke nan mai nuna cewa an canja Kur’ani shi ma!

Mun sani makarantanmu Musulmi nan da nan za su gaya mana cewa, waɗannan juyin Turanci ne kaɗai, kuma ba a sāke canja ainihin Larabci ba ko da shike ba a sami kalmar “haifa” ba a cikin wasu juyi na Kur’ani. Don haka muna roƙon ku da ku dubi wannan da ainihin gaskiya kuma – babu abin da za a faɗa gāba da mutuncin Littafi Mai Tsarki don kawai saboda kalmar “haifa” kamar yadda yake a cikin Kur’ani, an samu daga juyi guda amma babu a cikin guda.

c) Misali na uku na Deedat shi ne, mun yarda cewa lahani guda na juyin RSV ya nuna zai yi gyaransa. A cikin 1Yahaya 5:7 cikin juyin KJV mun sami aya mai karkasa ɗayantuwar Uba, da Kalma da kuma Ruhu Mai Tsarki ba a sa shi a juyin RSV ba. Wannan ya nuna ke nan wannan aya matini ne kawai aka rubuta a gefen shafi cikin matanin farko, don haka kuskure ne marubutan da suka zo daga baya suka yi a kan matani na ainihi. An fitar da ita daga dukan juyi na zamani, domin yanzu muna da matanai daɗaɗɗu masu iko ƙwarai ba a sami ayan nan a cikinsu ba.

Deedat yana cewa, wannan aya ita ce mafi kurkusa da abin da Kirista suke kira Tirnity Mai Tsarki a cikin kundin jerin abbuwa da suke kira Littafi Mai Tsarki (ɗan littafin Deedat mai suna a Turanci “Is the Bible God’s Word?” shafi na 16). Idan ma har ita ce, ko idan dukan rukunan Tirniti sun kafu a kan wannan matanin aya kaɗai, to, ba shakka da abin zai zama abin da za a yi la’akari da shi ƙwarai da gaske. A akasin haka, duk wani mai fassarar tauhidin Littafi Mai Tsarki, ba da wata – wata ba zai yarda – kamar yadda dukan ’yan Katolika, da ’yan Protestants, da sauran Kirista gaba ɗaya – cewa rukunan Tirnity ne kaɗai rukunan Allah wanda za a iya samu daga koyarwar Littafi Mai Tsarki gaba ɗayansa. Hakika aya ta biyu ita ce ta fi zama mafificciyar aya 1Yahaya 5:7:

“Don haka sai ku je ku almajirtar da dukkan al’ummai, kuna yi musu baftisma da sunan Uba, da Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki” (Matiyu 28:19).

Suna ɗaya kaɗai na mutum ukun nan aka yi batu ba jam’i ba. Cikin Littafi Mai Tsarki kalmar “suna” an more ta cikin irin wannan mahallin yana magana ne a kan hali na mutum ko wurin da aka bayyana. Saboda haka Yesu yana maganar suna ɗaya kaɗai Uba, Ɗa da Ruhu Mai Tsarki – yana ambaton cikakkiyar ɗayantuwa a tsakaninsu – kuma na suna guda ɗaya kaɗai – yana ambaton cikakken kamancin hali da ainihi. Wannan aya cikakken Tirnity ne abin da ta ƙunsa ta kuma ƙarfafa, 1Yahaya 5:7 kuwa ta buga ƙusa a kai ne kawai, ba mu ga aibu ba da ya shafi tsallake wannan aya a cikin juye juye na yanzu har da zai yi lahani ga rukunan Kirista. Don haka babu dalilin yin wani matsanancin la’akari na kowane iri a kan wannan.

d) Batunsa na huɗu wani babban abin mamaki ne dangane da irin zurfin jahilcinsa mara matuƙa. Yana cewa “hurarrun” marubutan Bisharu ba su rubuta labarin HAWAN Yesu zuwa sama ba, ko da kalma ba su rubuta ba, (ɗan littafin Deedat mai suna a Turance “Is the Bible God’s Word?” shafi na 19). Ya yi wannan iƙirari ne don bin diddigin batun hawan Yesu zuwa sama a cikin Bisharun Markus da Luka wanda RSV ya bayyana a zaman bambancin karatu wanda muka yi batunsa tun da fari. Baya ga ayoyin nan, marubutan Bishara, bisa ga zargi ba su yi ambato na kowane iri a game da hawan Yesu zuwa sama ba. Akasin wannan, mun sami cewa duka su huɗun suna sane da wannan sarai. Yahaya ya ambata wannan ba zai kāsa sau goma sha ɗaya ba. A cikin Bishararsa, Yesu yana cewa:

“Ina hawa wurin Ubana kuma Ubanku, Allahna kuma Allahnku” (Yahaya 20:17).

Luka kuwa ba Bishararsa kaɗai ya rubuta ba, amma har da Littafin Ayyukan Manzanni, a cikin na ƙarshen, abu na farko da yake ambatawa shi ne hawan Yesu zuwa sama:

“Da ya faɗi haka, suna cikin dubawa, sai aka ɗauke shi Sama, wani gajimare ya tafi da shi” (Ayyukan Manzanni 1:9).

Matiyu da Markus sun yi ta maganar zuwan Yesu na biyu daga sama (dubi Matiyu 26:64 da Markus 14:62). Zai yi wuya a ga yadda Yesu zai zo daga sama idan tun da fari bai hau sama ba.

A ƙarshe, dole mu nuna cewa Markus 16:9-20 da Yahaya 8:11 ba a taɓa share su ba daga cikin Littafi Mai Tsarki sa’an nan aka sāke komo da su daga baya kamar yadda Deedat yake faɗi. A cikin juyin Turanci na RSV an haɗa da su yanzu cikin matani, domin masana sun tabbatar cewa hakika suna cikin matani na tun asali. Gaskiyar batun ita ce, a cikin daɗaɗɗun rubuce-rubucen an same su a cikin wasu matani, a cikin wasu kuwa babu. Editocin RSV ba su yi karambani da Littafi Mai Tsarki ba kamar yadda Deedat ya ke iƙirari – sun dai yi ƙoƙari kaɗai su kawo juyin Turanci namu kurkusa da ainihin matani tun na farko – ba kamar editoci irin su Uthman ba, wanda ya hallakar da sauran kundayen Kur’ani don kawai sun bambanta da nasa matanin.

A ƙarshe duka babu abin da ke tabbatar da cewa dukan rubutun asali – waɗanda daga gare su ne aka rubuta littattafan Littafi Mai Tsarki karo na farko – a ce sun ɓata, an halakar da su kamar yadda yake gaskiya a kan matanin farko na Kur’ani. Matani mafi daɗewa na Kur’ani har yanzu ya kasance tun daga ƙarni na biyu bayan Hijirah, an kuma haɗa shi cikin kundi cikin rubutun Larabci na farko “al-mail”. Wasu Kur’ani na farko an yi su cikin rubutun “Kufic” su kuma duk a lokaci guda ne da na “al-mail”.

6. ALLAH A CIKIN LITTAFI MAI TSARKI

A shafi na 22 cikin ɗan littafinsa mai suna “Is the Bible God’s Word?” Deedat ya samar da wata ’yar takarda don ya nuna cewa Kalmar Larabci Allah wai an same ta cikin Littafi Mai Tsarki juyin da ake kira da Turanci “Scofield”. Abin farin ciki a cikin wannan matsala da aka sa a gabanmu shaida ce da za mu yi la’akari. An samar da shafi guda daga Littafi Mai Tsarki juyin “Scofield”, a cikin matani mun sami cewa kalmar Ibrananci ita Deedat ya ɗauka don ya tabbatar cewa an sami kalmar Larabcin Kur’ani cikin Littafi Mai Tsarki!

Wata tatsuniya, kuma mafarki shi ne, ƙoƙarin tabbatar da wani batun da yake da wuyar ko a yi shayin sa. Kalmar Ibrananci ita ce “alah”, sananniyar kalma ce mai ma’ana “yi rantsuwa”. Ta yaya za a zaci wannan zai tabbatar da cewa kalman nan Allah na Kur’ani cikin Larabci za a iya samunsa cikin Littafi Mai Tsarki, ai, wannan yana da wuyar ganewa a gare mu. Ƙoƙarin Deedat na murɗe abubuwan gaskiya ya ci gaba da ƙara cewa Elah cikin Ibrananci (Ma’ana Allah) editoci sun shirya baƙaƙen cikin juyin Deedat mai suna a Turance “Is the Bible God’s Word?” shafi na 21). Wannan ya sa mun kāsa iya yarda mu jure da wannan. Waɗannan editoci a sarari suka fayyace kalma ta ƙarshen nan wadda ma’anarta ita ce “Yi rantsuwa”.

Kamar waɗannan abubuwan da aka buga da su a baya ba su isa ba, ya zamar mana dole mu ƙara jurewa da rashin kangadon tunanin Deedat lokacin da ya ke cewa, rashin sa Kalmar Allah cikin juyin baya-bayan nan na Scofield tabbaci ne mai nuna cewa an share kalmar ... daga cikin karɓaɓɓen Littafi Mai Tsarki! (ɗan littafin Deedat mai suna a Turance “Is Bible God’s Word?”, shafi na 21). Abin da ke nan a game da wannan shi ne, an tsallake shi daga matuni cikin matanin Littafi Mai Tsarki kansa! A wani wuri kuma canji a cikin matanin Littafi Mai Tsarki kansa! A wani wuri kuma Deedat ya yi iƙirari cewa Kirista ba su ɗauki matuni a ƙasan shafin Littafi Mai Tsarki ya zama sashi na Maganar Allah ba (cikin ɗan littafinsa mai suna Is the Bible God’s Word?, shafi na 17). Babban abin tausayi ne yadda mutumin nan bai iya yin abin da ya ke so wasu su yi masa ba.

Zai zama da amfani a nuna cewa, babu wani abu mabambanci a game da kalman nan Allah na Kur’ani, ko dole a ɗauke ta muhimmiya don kawai ta fito daga asalin Kur’ani. A akasin wannan, a sarari yake cewa ta samo asali ne daga kalmar Syriac Alaha (ma’ana “Allah”). Sananniya ce a tsakanin Kirista tun zamanai kamin ɓullowar addinin Islama (gwada hujjar da Jeffery ya nuna cikin littafinsa mai suna a Turance The Foreign Vocabulary of the Qur’an, shafi na 66). Kuma an sha morar kalmar a cikin Larabawa kafin zuwan Islama kamar yadda za a iya gani daga sunan Abdullah mahaifin Muhammadu (wato bawan “Allah”). Tabbatacce ne kuma kalman nan Allah an more ta da ma’anarta ta “Allah” tun kafin bayyanar Islama cikin waƙe (Littafin Bell, mai suna a Turance The Origin of Islama in its Christian Enviroment, shafi na 53). Haka kuma babu abin da yake mabambanci ko kaɗan a game da wannan suna. Cikin al’amuran nan duka, mun kāsa ganin abin da Deedat yake ƙoƙarin tabbatarwa, ko a kan me yake ta ɗoki.

7. SASSA DAIDAI DA JUNA CIKIN LITTAFI MAI TSARKI

Ba mu bukatar ɗaukar dogon lokaci da surar Deedat mai suna a Turance, “Damning Confessions”, da shike waɗannan ba kome ba ne amma yarda da gaskiya, mu yarda cewa Littafi Mai Tsarki ya sha fama da kurakuran matanai irin waɗanda muka rigaya muka yi maganarsu a baya. Kamar kuma yadda muka riga muka gani Kur’ani ma ya sha fama da irin waɗannan matsaloli, ba mu amince ba cewa ya wajaba mu ƙara bi cikin wannan da zurfi.

Muna mamaki, da maganar Deedat wadda ba daidai take ba, mai cewa, “daga fiye da rubuce -rubuce dubu huɗu iri dabam-dabam da Kirista suke fāriya a kansu, iyayen ikilisiya sun zaɓi guda huɗu kaɗai waɗanda suke ta terere da su suna kuma kiran su Bisharun Matiyu, Markus , Luka da Yahaya saboda nukura” (Ɗan littafin Deedat mai suna a Turance Is the Bible God’s Word?, shafi na 24). Deedat a nan ya ƙara fallasa wawancin jahilicinsa na batunsa a kan rubuce-rubuce dubu huɗu, waɗannan kofen littattafai 27 da suka haɗa jimlar Sabon Alkawari. Ɗaruruwan waɗannan kofe ne Bisharu huɗu da ya ke ɓaɓatu a kai. Furci irin waɗannan su ke tilasta mana mu tsuce/ƙarashe da cewa, ɗan littafin da Deedat ya rubuta ba yadda za a ɗauke shi a aikin masani ƙwararre mai sukar Littafi Mai Tsarki, amma fankon dogon surutu ne kawai gāba da Littafi Mai Tsarki daga mutumin da jahilcinsa ya haɗu da tsananin nukurarsa kawai gāba da Littafi Mai Tsarki.

Irin nukuran nan a fili ta fallasu a shafi na gaba inda yake iƙirarin cewa littattafai biyar na Musa ba za a ɗauke su maganar Allah ne ko na Musa ba, saboda wasu magana kamar waɗannan, Ubangiji ya faɗa wa Musa..., a matsayin mutum na uku, irin wannan ya bayyana sau da dama. Da shike Deedat ba ya la’akari ko da na ƙanƙanin lokaci don ya iya gane cewa Musa yana iya maida kansa a matsayin mutum na uku; Deedat yana ikirarin cewa waɗannan kalmomi sun fito daga “mutum na uku karkatacciyar koyarwa ce” (ɗan littafin Deedat mai suna a Turance, Is the Bible God’s Word? shafi na 25).

Idan haka ne, to, Kur’ani shi ma dole ya warwatse da shike shi ba maganar Allah ko ta annabi ba ce, amma ta “mutum na uku ce aka rubuta ta daga karkatacciyar koyarwa domin akwai irin waɗannan maganganun cikin shafunan Kur’ani, kamar waɗannan:

A lokacin da Allah ya ce, “Ya Isa ɗan Maryama! Ka tuna ni’imata a kanka” (Suratul Maida 5:110).

Ba mu ga wani bambanci ba a tsakanin cewa inda Ubangiji ya yi magana da Musa a cikin Littafi Mai Tsarki, da kuma inda Allah ya yi magana da Yesu a cikin Kur’ani. Hakika, duk wata sèka a kan bayanin Littafi Mai Tsarki dole irinta ta kama Kur’ani.

A ƙarshe, ba shakka Musa bai rubuta labarin mutuwarsa ba kamar yadda Deedat ya ɗauka. Sura ta talatin da huɗu ta Littafi Maimaitawar Shari’a, annabi Joshuwa magājinsa ne ya rubuta, shi ne kuma ya rubuta littafin da ke ɗauke da sunansa, wanda ke biye da Maimaitawar Shari’a.

Sura ta shida ta Deedat tana batu ne a kan ingancin Bisharu huɗu. Deedat ya fara da cewa abin shaida na ciki yana nuna cewa Matiyu ba shi ne marabucin Bishara ta fari ba( ɗan littafin Deedat mai suna A Turance Is the Bible God’s Word? shafi na 26) don kuwa Matiyu ya nuna kansa kamar mutum na uku ya ke magana. Mun riga mun ga irin rashin ƙarfin tunaninsa a kan wannan. Ana iƙirarin cewa Allah ne marubucin Kur’ani duk da haka ya bayyana kansa sau da dama, wurare dabam dabam a matsayin mutum na uku. Har yanzu, ba mu ga yadda Musulmi na sosai zai yi shakkar ko wa yake marubucin kowane littafin cikin Littafi Mai Tsarki ba don kawai marubucin ya nuna kansa cikin mutum na uku.

Bugu da ƙari, ɗan taƙaitaccen bin ƙididdigi na samar da gabatarwar Bisharar Matiyu wanda J B Phillips ya yi a cikin ɗan littafin Deedat yana tabbatar da ƙarin haske ƙwarai da gaske. Phillips ya ce:

Hadisan farko sun nuna manzo Matiyu ne ya rubuta ta, amma masana na wannan zamani kusan dukansu sun ƙi yarda da wannan ra’ayi. Marubucin da har yanzu muka amince ba tare da wata damuwa ba wanda muke kira Matiyu, ya shigo ta asirtacciyar hanya “Q”, wanda zai zama an tattaro daga hadisan da aka faɗa da ka. (Ɗan littafin Deedat mai suna a Turance Is the Bible God’s Word? shafi na 28)

Duk wanda ya san ma’anar bayanin nan “dalili mai zaƙi” zai yi la’akari mai zurfin gaske a game da waɗannan abubuwan gaskiya:

1. Hadisin Kirista na farko gaba ɗaya suka bayyana wannan Bishara Matiyu ne ya rubuta ta. Ba za a ɗauki gaskatawa ko ra’ayin masana na wannan zamani a auna shi gāba da shaidar waɗancan da suka yi rayuwa a lokacin da aka fara rubuta kofen wannan Bishara ba, har aka rarrabar da ita. Muna shakkar sharhin nan ƙwarai da gaske mai cewa, kusan dukan masana ba su yarda cewa Matiyu ne marubucin wannan Bishara ba. Wata ƙungiyar masana ce kaɗai suka yi wannan – su ne waɗanda ba su gaskata labarin halitta ba waɗanda suka yi watsi da labarin Nuhu da rigyawa, sun ɗauka tatsuniya ce kawai, suna kuma yin ba’a ga labarin Yunana wanda ya yi kwana uku a cikin cikin kifi. Mun tabbata, Musulmi masu karanta rubutunmu, za su san ko me za su samu daga irin waɗannan “masana”. A akasin wannan, waɗancan masana da suka yarda cewa labarun nan na gaskiya a tarihince, kuma haka yake a aikace, banda ragi kuma sun yarda cewa Matiyu ne ya rubuta wannan Bishara.

2. Phillips ya ce, marubucin yana iya zama Matiyu ne zalla domin babu wani dabam da ya cike gurbinsa don rubuta wannan Bishara, tarihin Ikilisiyar farko kuma ba ta taɓa ambatar wani marubuci dabam ba.

3. Asirtaccen “Q” ya zama na asiri kaɗai domin ƙage ne kawai na “masana”. Ba asiri ba ne, ba kuma labarin ƙarya ba ne. Babu wani abin shaida na tarihi na kowane iri inda irin wannan hadisi na kā ya taɓa kasancewa.

A ƙarshe dai, zai yi mana wuya mu yi wani la’akari a game da tsegumin Deedat a kan cewa wai Matiyu ya kofa ne daga Markus, kuma wata sura cikin Ishaya 37 an maimaita ta a cikin 2Sarakuna 19. Dalilin da ke biye da tunaninsa gaba ɗaya kamar na yara ne yadda yake a cikin ɗan littafinsa (Is the Bible God’s Word? shafi na 29). Wannan ya kawar da dukan jayayyarsa mai hana yiwuwar kasancewar Littafi Mai Tsarki a matsayin Maganar Allah, yana da wuya ƙwarai a iya yarda da wannan.

Sai mutum ya san tushen Bisharar Markus sa’an nan zai iya ganin wautar gardamar Deedat. Wani daga cikin Iyayen Ikilisiya na farko, Papias ya bar mana labarin gaskiya cewa Manzo Bitrus shi ne sassalar bayanin Bisharar Markus.

Bitrus ya fi Matiyu samun bayanai a game da rayuwar Yesu. An bayyana maganar Bitrus a cikin sura ta 4 ta Bisharar Matiyu, maganar Matiyu kuwa ta bayyana cikin sura ta 9 kaɗai – da daɗewa bayan al’amura masu yawa waɗanda Manzo Bitrus ya shaida sun riga sun faru.

Bugu da ƙari kuma, sau da yawa Bitrus yana tare da Yesu, Matiyu kuwa ba haka ba. Bitrus yana nan a lokacin sākewar kamannin Yesu (Markus 9:2) yana nan kuma a Lambun Gatsemani (Markus 14:33) Matiyu kuwa ba ya nan a waɗannan wurare.

Da wuya Matiyu ya sami wata dogararriyar hanyar samun bayanai domin Bishararsa, sa’ad da yake kofe matanin maganar Allah, don haka ba mu ga yadda Bishara za ta iya rasa hatimin ikonta ko ainihinta ba.

Idan har Deedat zai iya nuna yadda labarun Littafi Mai Tsarki irin waɗanda ya samar sun yi daidai da ayyukan Littafi Mai Tsarki gabanin Bisharu, inda irin ayyukan nan tattaruwar ƙagaggun labaru ne, to, da za mu ɗauki batunsa da muhimmanci. A akasin wannan, da shike babu wannan daidaici cikin batutuwa bisa ga Littafi Mai Tsarki, akwai labaru da dama a cikin Kur’ani, mai kama da labarin gaskiya, wanda yake da wuyar daidaita da littattafan Yahudawa da suke tun kafin zuwan Islama masu ɗauke da ƙagaggun labaru – da tatsuniyoyi na tsibbu. Za mu duba misali guda ɗaya kaɗai.

Kur’ani ya ba da labrin kisan da Kayinu ya yi wa ɗan’uwansa Habila (Suratul Maida 5:27-32) labarin kuma da ake samu a cikin Littafi Mai Tsarki cikin Littafin Farawa. A wani wuri, mukan sami wasu maganganu waɗanda ba na safai ba, waɗanda ba su da wani daidaici da na Littafi Mai Tsarki:

Sai Allah ya aiki wani hankaka, yana tono a cikin ƙasa domin ya nuna masa yadda zai turbuɗe gawar ɗan’uwansa (Suratul Maida 5:31).

A cikin littafin ƙagaggun labaru da almara na Yahudawa, mun karanta cewa Adamu ya yi kukan mutuwar Habila, bai kuwa san yadda zai yi da gawar ba, sai da ya ga hankaka yana tone ƙasa ya binne abokinsa da ya mutu. Daga nan ne Adamu shi kuma ya yi kamar yadda hankakan ya yi. (Littafin Pirke Rabbi Eliezer, Sura ta 21).

A cikin Kur’ani, Kayinu ne ya ga hankakan, a littafin Yahudawa kuwa Adamu ne, amma baya ga wannan ɗan bambancin kamanci tsakanin labarin biyu, babu kuskure. Da shike littafin Yahudawa ya girmi Kur’ani, da alama Muhammadu ya ɗebo labarin ne ya yi masa kwaskwarima, aka rubuta a cikin Kur’ani ya zama haka – musamman ma lokacin da muke la’akari da aya ta biye cikin Kur’ani mai cewa:

Daga sababin wannan, muka rubuta a kan Bani Isra’ila cewa, lalle ne wanda ya kashe rai ba da wani rai ba, ko barna a cikin ƙasa, to, kamar ya kashe mutane duka ne, kuma wanda ya raya rai, to, kamar ya rayar da mutane ne gaba ɗaya (Suratul Maida 5:32).

A gefe guda na ayan nan ya nuna babu mahaɗi da labarin da ya gabata. Don me rayuwa ko mutuwar mutum za ta zama ceto ko halakar dukan mutane, wannan ko kaɗan babu wani haske. Idan kuma muka juya wajen takalidan Yahudanci, mun ga mahaɗi a tsakanin labarin da abin da ya bi baya. Mu juya ga Mishnah kamar yadda H. Danby ya juya, a nan muna karanta waɗannan kalamai:

Mun ji an ce game da batun Kayinu wanda ya kashe ɗan’uwansa, “Muryar kukan jinayen ɗan’uwanka (Farawa 4:10). Ba a ce jini guda ɗaya ba, amma jinaye cikin jam’i, wato jinin kansa da na zuriyarsa. An halicci mutum gudansa domin a nuna cewa wanda ya kashe mutum guda za a lasafta shi a ya kashe dukan zuriya, amma wanda ya tserar da ran mutum guda, za a lasafta shi, cewa ya tserar da dukanin zuriya. (Mishnah Sanhedrin,4:5).

Bisa ga rabbin Yahudawa wanda ya rubuta kalaman nan, morar jam’in jini a cikin Littafi Mai Tsarki bai tsaya a batun jinin mutum guda ba, amma na dukatanin zuriyarsa. Mun ɗauki fassararsa ta zama marar tabbas, amma in ma haka ne, ya zamar mana dole mu yi tambaya a kan yadda ya zama cewa wahayin Allah da a ke iƙirari a cikin Kur’ani keɓaɓɓen maimaicin gaskatawar rabbi ne kawai! Sai kawai mu ƙarasa da cewa Muhammadu ya yi wa batun kwaskwarima ne a game da dukan al’umma daga abin da ya samo daga Yahudawa ba tare da nuna inda mahaɗin ya samo asali ba (kila ma bai sani ba!).

Ta wurin kwatantawar, ya nuna a sarari cewa wannan ne ya sa Muhammadu ya yi wannan bauɗiyar: ba shakka ya sami wannan ka’ida daga masu ba shi labaru lokacin da suke faɗa masa wannan al’amarin. (Geiger, Judaism and Islama, shafi na 81).

Babban sakamakon labarin hankaka da ke tsakanin Kur’ani da almarar Yahudawa, da kuma ra’ayoyin masana ussan ilimi da suka biyo baya da suka shafi batun kisan mutun guda tare da dukan zuriyarsa, a sarari wannan ya nuna cewa Muhammadu ya dogara ne ga masu ba shi labari, ayoyin nan kuma ba su fito daga wurin Allah ba. Ƙarshen maganan nan kuwa ba shi kawuwa:

Labarin mutun mai kisan kai na fari a duniya ya isa zama misali mafi bayyana rinjayen Yahudanci a bayan al’amuran. (Wannan daga wani littafi ne da wani mai suna Guillaume ya rubuta “The Influence of Judaism on Islam”, The Legacy of Isra’el, shafi na 139).

A maimakon kafa hujjoji daga sassa na cikin Littafi Mai Tsarki waɗanda suke da daidaici da wani wuri cikin Littafi Mai Tsarki, ya kamata Deedat ya ba mu wani bayani dabam a kan dalilin da ya sa sassan Kur’ani a kunyace suke dogara ga littattafan ƙagaggun labaru da al’amara na Yahudawa.

Ya rufe surarsa da bayyana waɗanda suka gaskata cewa kowace kalma da waƙafi, da ɗigo na Littafi Mai Tsarki Maganar Allah ne “Masu dundu ga Littafi Mai Tsarki” (Ɗan littafin Deedat mai suna “Is the Bible God’s Word?” shafi na 33). Ba shakka, ba ma tausaya wa ’yan riƙau masu yin matsanancin iƙirari a kan Littafi Mai Tsarki, amma bisa ga abin shaida da muka yi nazari zuwa yanzu, muna iya amsa cewa haka yake kuma ga ’yan riƙau Musulmi waɗanda su ma suka yi irin wannan iƙirari a kan Kur’ani gāba da dukan abubuwan shaida a akasi, dole mu dubi wannan da ba’a, ya kuwa cancanci wannan ba’ar su ne “Masu dundu ga Kur’ani”!

8. ZARGIN DAGULAWA CIKIN LITTAFI MAI TSARKI

Deedat ya fara surarsa ta bakwai da iƙirari mai ɗaci cewa akwai rikitarwa tsakanin 2Sama’ila 24:1, inda muka karanta cewa Ubangiji ya iza Dawuda ya ƙidaya Isra’ilawa, kuma cikin 1Tarihi 21:1 tana cewa Shaiɗan ne ya tsokani Dawuda ya yi wannan. Duk mutumin da ke da ilimin da ya dace na Littafi Mai Tsarki duk da Kur’ani, nan da nan zai fahimci cewa Deedat yana fallasa cikakken rashin saninsa, da ganewarsa na rarrabe tauhidin duka littattafan biyu. A cikin Kur’ani kansa mun sami irin wannan nassin wanda ya ba da haske ƙwarai a kan wannan batu:

Shin, ba ka gani ba cewa mun saki Shaiɗanu a kan kafirai suna shushuta su ga zunubi shushutawa? (Suratu Maryam 19:83).

A nan mun karanta cewa Allah ne yake saka aljannu a kan marasa bi. Saboda haka, inda Allah ne yake motsa su don ruɗarwa, shi yake morar aljannu su tsokane su ga in haka. Haka yake, daidai, Allah ne ya motsa Dawuda, ya kuma mori Shaiɗan ya tsokani Dawuda har ya ƙidaya Isra’ilawa. Kamar yadda ya faru a cikin Littafin Ayuba cikin Littafi Mai Tsarki, muna karanta cewa, aka ba Shaiɗan iko a kan Ayuba don ya azabta shi (Ayuba 1:12) amma daga baya Allah ya yi magana sai ka ce shi ne aka motsa gāba da shi (Ayuba 2:3). Duk lokacin da Shaiɗan ya tsokani mutane, a fakaice akan ɗauka tamkar Allah ne ya motsa shi, domin kuwa idan ba tare da yardar Allah ba, ba abin da Shaiɗan zai iya kammalawa. An ɗauko wannan daga sharhin Zamakshari ne a kan Suratul Baƙara 2:7 (Allah ya sa hatimi a kan zukatansu, da a kan kunnuwansu) a ganinsa ya kamata wannan ya isa ya zama magana ta ƙarshe a kan wannan matsala:

Yanzu ya zama zahiri, Shaiɗan ko mara bi ne aka hatimce wa zuciya. Amma duk da haka, tun da shike Allah ne ya ba shi iznin, da yiwuwar aikatawa, an ɗora hatimcin a kansa a shi ne sanadin aikatawar. (Littafin Gatje mai suna a Turance “The Qur’an and its Exegesis”, shafi na 223).

Ya kamata marasa ƙwarewa kamar Deedat su ɗauki darasi cikin tauhidin Kur’ani daga shahararun masana kamar su Zamakshiri kafin su fallasa kansu ga zama abin ba’a ta wurin far wa Littafi Mai Tsarki da sèka.

Wasu batutuwan Deedat a kan annobai uku ko bakwai a cikin 2Sama’ila 24:13 da 1Tarihi 21:11 da sauran wasu ’yan kurakurai makamantan wannan da sukan zama tuntuɓen alkalami, inda masu rubutu sukan gauraye alƙaluma ko adadai. Alal misali, a cikin Ibrananci wata ’yar ƙaramar kalma aka more ta a kan 2000 cikin 1Sarakuna 7:26 sun yi kusa da juna ƙwarai da adadin 3000 na cikin 2Tarihi 4:5 (duba ɗan littafin Deedat mai suna “Is the Bible God’s Word”, shaffi na 42). Duk mai bincike da niyyar gaskiya zai gane sarai wannan yana iya zama kuskuren marubuci na ƙarshe ya ɗauki 200 a matsayin 3000. Cikin dukan waɗannan matsaloli da Deedat ya kafa, muna da ƙananan kurakurai da masu buga keken rubutu sukan yi, akan gane su da sauƙi, irin waɗannan ba su zama kuskure don rikitarwa ko dagularwa ba kamar yadda a ke iƙirari. Ba wanda ya taɓa nuna mana lahanin da waɗannan ’yan kurakurai suka yi wa abin da dukanin Littafi Mai Tsarki ya ƙunsa.

9. MAGANAR BATSA A CIKIN LITTAFI MAI TSARKI

A cikin surarsa ta biye, Deedat ya cika surutu a kan labarin lalatar da Yahuza ya yi da Tamar (labarin yana cikin Farawa 38). Da wasu labaru makamatan wannan a cikin Littafi Mai Tsarki (kamar na Lutu da ’ya’yansa mata); ya kuma yi ikirari cewa Littafi Mai Tsarki ba zai zama maganar Allah ba saboda irin labarun nan da ke cikinsa.

Irin wanna tunani na Deedat yana da wuya ƙwarai mu bi shi. Hakika, littafin da ya ke iƙirarin Maganar Allah ba za a ƙi shi ba kamar haka saboda kawai yana nuna mutane – har ma da mafiya nagari a cikinsu – da suka yi mummunan abu. Dukan labarun da Deedat ya ke maganarsu a kan muguntar mutane ne, da kuma yadda aka tone zunuban mutane, ba mu iya gane yadda wannan zai iya hana Littafi Mai Tsarki ya zama maganar Allah ba. Cikin dukanin Littafi Mai Tsarki, ana nuna Allah shi cikakken tsarki ne, cikakken adalci, cike da ƙauna mai banmamaki. Muhimmin abu shi ne, babu inda Deedat ya yi iƙirarin cewa an zargi halin Allah a cikin Littafi Mai Tsarki, hakika kuma wannan shi ne abin da mu duka muka fi la’akari da shi lokacin da muke yanke ƙuduri ko littafin Maganar Allah ne. Idan Littafi Mai Tsarki ya fallashe zunubin mutane kakaf a yadda suke, bai kuma yarda ya rufe na mafiya ingancinsu ba, ba shakka yana da ’yanci sosai na yin iƙirarin zama Maganar Allah – domin yana la’akari ne da yabonsa ba yabon mutane ba. Littafi Mai Tsarki yana la’akari ne da ɗaukakar Allah – ba ɗaukakar banza ta mutane ne!

Wani muhimmin abu kuma shi ne, a sawwaƙe Deedat ya kauce wa wani labari a cikin Littafi Mai Tsarki wanda yake bayyana wata muguwar mugunta fiye da waɗanda Deedat ya zaɓa ya yi magana a kai. A cikin 2Sama’ila 11 muna karanta cewa Dawuda ya ga Batsheba tana wanka, ya sa aka kawo masa ita, ya kwana da ita. Bayan wannan, lokacin da ta yi ciki, sai Dawuda ya sa aka kashe mijinta Uriya, ya ɗauke ta ta zama matarsa.

Wannan labari a ƙalla ya yi daidai da dukan waɗanda Deedat ya yi magana a kai saboda muguntarsa, amma Deedat ya zaɓi ya kauce wa wannan labari. Don me? Domin Kur’ani ma ya yi magana a kan labarin nan. Muna karantawa a Sura ta 38 cewa, mutum biyu suka bayyana a gaban Dawuda, mutum guda yana da tumaki 99, sai yana son guda ɗaya da guda mutumin yake da ita don ya ƙara da nasa. Bayan wannan, sai muka karanta cewa Dawuda ya gane misalin a kansa ne aka yi, Kur’ani kuma ya faɗo abin da Allah ya ke ce masa:

Dawuda ya gane cewa mun gwada shi, ya nemi gafarar Ubangijinsa, ya sunkuyar da kansa, ya fāɗi ƙasa warwas ya tuba. Don haka muka gafarta masa wannan. (Suratu 38:25,26).

Kamar yadda yake a labarin Kayinu da Habila jerin al’amuran ba su da wani kangado ko mahaɗi da abin da ya biyo baya. Yaya Allah ya gwada Dawuda, me kuma ya yi da har ya tuba, ya sami gafarar Allah? Sai mu juya don mu sami amsa daga Littafi Mai Tsarki. A cikin 2Sama’ila 12 muna karanta cewa Annabi Natan ya zo wurin Dawuda, ya ba shi labarin wani mai arzaki mai garken raguna, amma ya bukaci guda ɗaya don ya shirya abincinsa, sai ya ɗauki tunkiya mai daraja ta ɗaya daga cikin barorinsa. Dawuda ya husata da mai arzikin nan, amma sai Natan ya ce masa:

“Kai ne mutumin. In ji Ubangiji Allah na Isra’ila, ‘Na naɗa ka Sarkin Isra’ila, na cece ka daga hannun Saul. Na kuma ba ka gidan ubangidanka da matansa. Banda wannan kuma na ba ka gidan Isra’ila da na Yahuza. Da a ce wannan ya yi maka kaɗan, da na ƙara maka kuma kamar haka. Me ya sa ka raina maganar Ubangiji, har da ka aikata mugun abu haka a gabansa? Ka kashe Uriya Bahitte ta hannun Ammonawa, ka ɗauki matarsa ta zama matarka” (2Samai’ila 12:7-9).

Yanzu a sarari yake yadda Allah ya shar’anta Dawuda. Yana da kome a wadace fiye da bukatarsa, yana da mata da yawa, amma ya ɗauke mata guda ɗaya ta baransa ta zama tasa. Da Dawuda ya amsa sai ya ce, “Na yi wa Ubangiji zunubi.” Natan ya amsa ya ce, “Ubangiji ya gafarta maka” (2Sama’ila 12:13). Labarun cikin Kur’ani da Littafi Mai Tsarki sun yi kama da juna, duk sun yi magana a sarari a kan matsala guda – Zinar Dawuda da Batsheba. Abu biyu kawai za mu faɗa a cikin wannan al’amura. Abu na fari, ba shakka Deedat ya zaɓi ya yi watsi da labarin nan na muguntar Dawuda domin ya san cewa Kur’ani ya ci gaba da labarin. Abu na biyu, da shike Kur’ani yana mutunta labarun Littafi Mai Tsarki, wannan yana nuna cewa babu tushen ƙin yarda da labaru makamantan wannan inda sauran annabawa suka aikata ƙananan laifofi, an sa su cikin Littafi Mai Tsarki na Kirista.

Dukan annabawa mutane ne masu nama, suna kuma iya fāɗuwa cikin mugun laifi kamar kowane kāsasshen ɗan adam, Littafi Mai Tsarki kuwa ba zai raga musu ba wajen fallasa ayyukansu. Ko Muhammadu ma mutum ne mai ɗabi’a irin ta mutane, ko da shike yana da mata wajen tara a lokaci guda bai iya daure sha’awarsa ta wasu mata ba, yakan ɗauki duk wadda ransa ya ke so a maimakon ya tare ga waɗannan nasa, ya riƙa ba kowacce kwananta. Lokacin da aka bayyana Suratul Ahzab 33:51, wadda ta ba shi kaɗaicin allahntaka na ya ɗauki duk wadda ya ke so (shi kaɗai) ta zama matarsa bisa ga wadda ya ga ta dace masa, mowarsa, A’isha ya zamar mata dole ta yi sharhi:

Ina ji kamar Ubangijinka yana hanzarta ka wajen cika muradinka da sha’awace - sha’awacenka (Sahih al-Bukhari, kundi na 6, shafi na 295).

Yesu Almasihu ne kaɗai wanda ya yi rayuwa marar zunubi, bai ba da kai ga sha’awace-sha’awace da fāɗuwar sauran mutane ba. Deedat ya yi tambaya, bisa ga hasken 2Timoti 3:16, a ƙarƙashin wasu kan magana da za mu iya aza labarun da ya ambata. Da mutunci tilas in samar da amas:

1. Rukunai: Dukan mutane masu zunubi ne, duk da annabawa da mutane mafiya kirki. Duka suna bukatar gafara wadda take samuwa ta wurin alherin Allah cikin Yesu Almasihu.

2. Tsautawa: Mutane ba za su yi zunubi Allah ya ƙyale su ba tare da sun sami sakamako ba. Abin sha’awa ne ƙwarai da gaske a ga yadda nan da nan bayan labarin lalatar da Yahuza ya yi, ɗan Yakubu da mu ka ji labarinsa shi ne Yusufu - ɗan da a dukan shafunan littafin Farawa ba mu ji labarin aibunsa ba.

Ya yi nasara cikin amincinsa a lokacin da ’yan’uwansa suka rusuna masa har a kan gwiwoyinsu a gabansa, suka roƙe shi ya ba su abinci don su rayu.

3. Gyara: Ko da shike Allah zai gafarta mana zunubanmu, duk da haka zai sa mu sha wuyar sakamakon domin amfanin kanmu. An gafarta wa Dawuda zinar da ya yi, amma ya sha wuyar hasara har sau huɗu a cikin rayuwarsa a sakamakon zunubinsa. Amma duk da haka don ya zama gyara ne a gare shi domin bai ƙara yin wani mugun abu kamar wannan ba.

4. Koyarwa cikin Adalci: Dukan al’amuran nan suna nuna cewa, mutum ba shi da wani ƙwazo na zaman adalci, amma mafi ƙwazon mugun aiki, an ba shi zarafi, don ya aikata zunubai mafiya muni. Muna bukatar mu biɗi adalcin Allah wanda yake samuwa ta wurin bangaskiya cikin Almasihu Yesu. Bayan da ya tuba da mugun laifin da ya aikata, sai Dawuda ya yi addu’a:

Ka halitta tsarkakakkiyar zuciya a cikina, ya Allah, ka sa sabon halin biyayya a cikina. Kada ka kore ni daga gabanka, kada ka ɗauke mini Ruhunka Mai Tsarki. Ka sāke mayar mini da farin ciki na cetonka, ka ƙarfafa ni da zuciya ta biyayya (Zabura 51:10-12).

Masu zunubi suna iya samun adalcin Allah ta wurin tuba daga zunubansu, su nemi gafarar Allah, suna dogara gare shi domin cetonsu. Kamar yadda Manzo Bitrus ya faɗa:

“Sai ku tuba, a yi wa kowannenku baftisma, kan kun yarda da sunan Yesu Almasihu, domin a gafarta zunubanku, za ku kuwa sami baiwar Ruhu Mai Tsarki” (Ayyukan Manzanni 2:38).

10. SASSALAR YESU ALMASIHU:

Deedat ya fara surarsa ta ƙarshe da iƙirarin cewa akwai rikitarwa a tsakanin sassalar Yesu a cikin, Bisharar Matiyu da ta Luka don kawai in ji shi akwai ƙaton bambanci cikin sunayen da marubutan biyu suka jera. Bisa ga Deedat, wannan bambanci na waɗannan jeri ya tabbatar da cewa “marubutan biyu manyan maƙaryata ne” (Ɗan littafin Deedat mai suna Is the Bible God’s Word? shafi na 54). Ya yi mana wuya ƙwarai mu yarda cewa, mutanen da suka yi matsanancin aikin rubuta koyarwa mafi tsarki da gaskiya da aka taɓa saukar wa ’yan adam, sai a juya a kira su “manyan maƙaryata” kamar yadda Deedat ya yi iƙirari.

Abin farin ciki shi ne, ba za mu ɗauki hassadar Deedat gāba da Littafi Mai Tsarki abin damuwa ba, za mu iya fuskantar wannan tambayar da ma’ana. Babu shakka, kowanne cikin mutanen nan yana da jerin sassala biyu – ɗaya ta wajen ubansa, ɗayan kuma ta wajen mahaifiyarsa. Yusufu ba uba na jiki ba ne na Yesu, amma ana iya ɗaukarsa tamkar uba saboda sassalarsa kamar yadda dukan Yahudawa suna da jerin sunayen sassalarsu ta wurin ubanninsu.

Saboda haka Matiyu, ba tare da ƙarin ƙorahi ba, ya rubuta sassalar Yesu ta hanyar Yusufu, kuma cikin labarin da yake biye a kan haihuwar Yesu, ya fi mai da hankali ga aikin Yusufu a matsayin mai kula da Yesu ta fuskar jiki, kuma mijin Maryamu mahaifiyar Yesu.

Da niyya Deedat ya ke ambaton cewa, bisa ga Luka 3:23, Yusufu ne uban Yesu (Ɗan littafin Deedat mai suna, Is the Bible God’s Word? shafi na 52) ba tare da ya ƙara wani sharhi ba. A nan, cikin kalma guda, akwai mabuɗi ga sassalar Yesu a cikin Bisharar Luka. Cikin dukan jerin kakannin da ya faɗi sunayensu ba mu ga inda ya ambaci mace ba. Ko da shike ya fi mai da hankali a kan aikin Maryamu cikin haihuwar Yesu, da ya zo a kan sassalarta, bai bayyana Yesu a matsayin ɗan Maryamu ba, amma a matsayin ɗan Yusufu, ma’ana, yana bin layin sassalar maza, ya sa sunan Yusufu a madadin Maryamu. Luka cikin lura ya haɗa da Yusufu (wanda da shi ne uba na jiki amma ba haka ba) a cikin sassalarsa don kada ruɗami ya shigo, domin kuma masu karatu su san cewa ba ainihin sassalar Yusufu ba ne aka rubuta. Wannan sawwaƙaƙƙen bayani nan da nan ya kawar da rikitarwar matsalolin da ake iƙirari.

Ko da shike an bayyana abubuwan da suke gaskiya tun ƙarni da dama, hassada ta makantar da mutane ba fāsawa don su yi ta wannan zargi irin na yarantaka a kan rikitarwa gāba da marubutan nan, wato Matiyu da Luka, (Ɗan littafin Finlay mai suna, Face the Facts, wato Fuskantar Abubuwan Gaskiya, shafi na 102).

Da Deedat ya ke ƙoƙarin tsare iƙirarinsa mai cewa, akwai rikitarwa a tsakanin marubutan – Bishara, sai kuma ya zargi Matiyu da cewa ya ba Yesu wulakantattun kakanni ta wurin ambatar “mazinata da zuriyar masu lalata” (Ɗan littafin Deedat mai suna Is the Bible God’s Word? shafi na 52) su zama kakannin Yesu, cewa wannan zai shafi cikakken tsarkinsa.

Idan muka auna Bisharar Matiyu za mu sami mata huɗu da ya ambaci sunansu cikin sassalar Yesu. Su ne, Tamar wadda ta yi lalata da Yahuza; Rahab, wadda karuwa ce, kuma Ba’al’umma; Rut, ita ma Ba’al’umma; da kuma Batsheba, wadda take mazinaciya. Da muhimmanci ƙwarai Matiyu ya ambaci matan nan huɗu cikin jerin kakannin Yesu masu lahani cikin rayuwarsu. Ba shakka ya yi wannan da niyya, a sarari yake kuma bai yi wannan don ya ƙasƙantar da Yesu ba ta wurin ambata sunayen irin matan nan. Idan da akwai wani abin kunya a game da wannan irin kakancin, da ba shakka sai ya ambaci wasu mata masu tsarki da Yesu ya fito ta tsatsonsu, kamar su Saratu da Rifkatu. Don me ya zaɓi waɗannan mata huɗu musamman waɗanda suka yi wa “tsarki” karantsaye? Nan da nan Matiyu ya ba mu tasa amsar. Lokacin da mala’ika ya zo wurin Yusufu, ya yi maganar yaron da za a haifa:

Za ka kuma sa masa suna Yesu, domin shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu (Matiyu 1:21).

Tabbatacce ne, Yesu ya zo duniya saboda mutane irin su Tamar, da Rahab, da Rut, da Batsheba. Ya zo domin ya ceci irin mutanen nan daga zunubansu, ya kuma samar da cetonsa ga dukan mutane, Yahudawa duk da Al’ummai. Kamar yadda shi kansa ya faɗa wa Yahudawa da kuma almajiransa a wani lokaci:

“Ai, lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya. Sai ku fahimci ma’anar wannan tukuna, ‘Ni kam, zaman jinƙai nake nema a gare ku, ba hadaya ba’. Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai masu zunubi” (Matiyu 9:12,13).

Idan kai mai karatu, kana shayin cewa ƙoƙarin addini da ka ke yi shekara da shekaru shi zai sa ka sami adalci a gaban Allah, kuma Allah zai share zunubanka, Allah da bai kula da irin yadda zunubanka suke karo da tsarkinsa ba, to, sai ka yi ta bin hanyarka marar amfani don adalcin kanka. Ba ka bukatar ka dubi Yesu, don ba zai iya taimakon ka ba. Babu wanda zai iya taimakonka.

Amma idan ka san cewa zunubanka suna da yawa, ka kuma gane ainihin kanka, idan kuma ka gane cewa babu wani adalci a cikin ka, illa muguwar mugunta; idan har za ka yi wa kanka gaskiya, ka yarda da abubuwan gaskiyan nan, to, sai ka juyo wurin Yesu domin ya zo ne domin ya ceci mutane irinka, yana iya tsarkake ka, ya kuma kuɓutar da kai daga dukan zunubanka.

Ba mu yi niyyar fama da wasu kiraye-kiraye na Deedat ba a game da marubutan littattafan Littafi Mai Tsarki ba. Yesu ya tabbatar cewa dukan littattafan Tsohon Alkawari kamar yadda Yahudawa suka karɓe su hurarrun Maganar Allah mai iko, ya sha faɗar su a kai – a kai, yana kuma nuna cewa Maganar Allah kamar yadda suka karɓe ta, ba za a taɓa ƙarya ta ba (Yahaya 10:35), Ruhu Mai Tsarki kuma gaba ɗaya ya shaida haka ta wurin dukan zamanan Ikilisiyar Kirista ga daidaitaccen ikon littattafan Sabon Alkawari.

Kamar yadda muka gani, Kur’ani shi ma ya ba da cikakken goyan baya ga littattafan Yahudawa da na Kirista, a zamanin Muhammadu ya ɗauke su ainihin Attaura da Linjila ne, ainihin Maganar Allah ne. Waɗannan littattafai su ne Tsoho da Sabon Alkawari kamar yadda muka sansu. Babu mai son zahirin gaskiya da zai yi shakkarsu.

11. ƘARSHEN MAGANA

Za mu ƙarashe da batu guda ɗaya daga dukan abin da aka faɗa. Deedat ya kāsa raunana Littafi Mai Tsarki daga zama Maganar Allah. Kamar Joommal wanda ya rigaye shi, sai kawai ya fallasa kansa, ya zama mai sèka marar tasiri na littattafan Kirista.

Bugu da ƙari kuma, abin baƙin ciki ne a ga ruhun akasi da halin ƙi sun mamaye kowane shafi na ɗan littafinsa. Ba inda za a ga ya yi magana mai ma’ana a game da abin da Littafi Mai Tsarki ya ƙunsa. Ko sau ɗaya bai faɗi wata kalma ba a game da Littafi Mai Tsarki, abin da ya ba mu mamaki kuma shi ne, kowa yana iya karance Littafi Mai Tsarki ya yi rubutu a kansa wanda yake cikakkiyar sèka. Daga shafin farko zuwa na ƙarshe mai karatu zai yi ta karo da ruhun matsananciyar hassada, lalle mutumin bai cancanci iƙirarinsa ba wai shi “masanin Littafi Mai Tsarki” ne.

A shafi na 41 na ɗan littafin, yana iza masu karatun littafin da su sami kofen Littafi Mai Tsarki kyauta daga ƙungiyar zumuntarmu. Wata rana na yanke shawara na ziyarci ɗaya daga cikin Musulmi masu yawa da suka rubuto mana suna neman Littafi Mai Tsarki saboda kiran da Deedat ya yi, sai na tarar wannan matashi ya bi shawarar Deedat a shafin nan cewa ya sa alama a dukan zarge-zargen da Deedat ya yi. Bai ɓata lokaci cikin neman matanin da yake nema ba na zargen-zargen da Deedat ya yi na ɓatanci wanda a banzace ya alkawarta masa cewa zai “rikitar ya kuma ruɗar da kowane mishaneri ko wani masanin Littafi Mai Tsarki” (Is the Bible God Word?, shafi na 41) da ya gifta a gabansa. Baya ga waɗannan matani, wannan matashi bai yi ƙoƙarin ƙara karanta Littafi Mai Tsarki ko ya nemi ya gane ainihin abin da ya koyar ba.

Mun yi begen cewa zuwa yanzu an riga an binne ruhun Jihadin Kirista, amma da alama wasu Musulmi suna so su farfaɗo da shi a cikin matasan Musulmi a yau. Babu shakka, duk Musulmi na gaskiya zai yarda cewa irin wannan fuskanta da ake yi wa Littafi Mai Tsarki, abin da za a yi shakkarsa ne. Wace riba za a ci ta wurin bi cikin littafi ba don kome ba sai don neman laifi kawai? Wane irin tunani ne wannan da yake zuga mutane don su nemi kurakurai kurum a cikin littafi tun ma kafin su karanta ko da kalma ɗaya? Daidai wani marubuci Kirista ya faɗa a game da Littafi Mai Tsarki:

Haka kalma mai banmamaki Allah ya ba ɗan adam. Tana da zurfi da kyau kuma, amma masu karatu don sèka kawai suna yin hasara ƙwarai da gaske (Littafin Young, mai suna, Kalmarka Gaskiya ce “Thy Word is Truth” shafi na 138).

Abin ya taɓa mini zuciya da na sami wasiƙu daga Musulmi suna roƙon Littafi Mai Tsarki, wannan ya nuna matakin girmamawa mai zurfin gaske dominsa, abin ƙarfafawa ne kuma a ga yadda akwai wasu Musulmi marubuta a duniya waɗanda suka ɗauki wani salo na dabam dangane da Littafinmu Mai Tsarki. Wata ƙungiya da ake kira “Islamic Foundation”, sananniyar ƙungiya ta Musulmi wadda ta buga littattafai masu yawa a kan Islama, sun ɗauki halin balaga da girmamawa ga Littafi Mai Tsarki. Tana ƙarfafa dukan Musulmi da su yi haka, ga kuma abin da suke faɗa a kan bangaskiyar Kirista cikin ɗaya daga cikin littattafansu:

Muhimmancin Musulmi ya yi binciken Kristanci ai, ba sai an faɗa ba ... Alhali kuwa ɗalibai Kirista suna ta binciken Islama, Musulmi kima ne kawai suka ɗauki binciken Kristanci da Muhimmanci... Al’amarin da Musulmi suka sami kansu a yau yana bukatar su yi nazari/binciken Kristanci... Ba shakka, hanya mafi kyau ta fuskantar binciken Kristanci ita ce a nemi shawarar sassalar Kristancin, a ƙididdige tunani da kuma abubuwan da mabiya suke gabatarwa, a maimakon fāɗawa cikin cacar baki kawai, kamar yadda wasu marubuta Musulmi suka riƙa yi a can baya. (Littafin Ahmad Von Denffer, mai suna a Turance “General and Introductory Books on Christianity”, shafi na 4).

Ai, waɗannan kalaman hikima ne! Amma abin baƙin ciki da muka gani shi ne, ba marubuta Musulmi na dā kaɗai suka tsunduma cikin cacar baki gāba da Littafi Mai Tsarki kawai ba. Har yanzu akwai masu fama da wannan hauragiyar a yau ta wurin mutane kamar su Deedat da Joomal. Sa zuciyar kaɗai da muke da shi a kan wannan maganar da aka kwaso, dole kuma mu ce wa Musulmi masu karanta takardunmu shi ne, ba za su sami kome ba in banda dagulallun ra’ayoyi na Kristanci daga ’yan littattafai kamar irin wanda muka gama ba da amsa a cikin wannan littafin.

Kamar yadda wani Musulmi mai hikima ya ce, hanya mafi kyau da Musulmi zai sami fahimta ta gaskiya a game da bangaskiyar Kirista ita ce mutum ya sami littattafan da Kirista ne suka rubuta, Kirista da suke bi da gaskiya. Wannan batun da aka kwaso lalle sun cancanci Musulmi na gaskiya ya yi la’akari da su:

Babu dalilin da zai hana waɗanda suka kafu cikin bangaskiyarsu su karanta Littafi Mai Tsarki. Wannan ya shafi waɗanda suke da ƙarfi cikin bangaskiyarsu ta Islama. Mallakar Kur’ani bai kange Musulmi daga neman ganewa ko fahimtar littattafai irin mabambantan tarihi, da halin kirki ba, da muhimmancin koyarwa/umarni domin dukan mutane da ake samu a cikin Littafi Mai Tsarki. Musulmi da dama da fari, ta wurin rashin sani, sun ƙi Littafi Mai Tsarki, amma daga baya da suka gane gaskiyar da ya ƙunsa sun yarda da dukiyar da ke ciki marar misaltuwa. (Littafin Harris mai suna a Turance, “How to lead Moslems to Christ” wato Yadda za a kawo Musulmi ga Almasihu, shafi na 17).

Da yardar ranmu za mu ba da Littafi Mai Tsarki kyauta ga duk Musulmin da zai karanta shi da zuciya ɗaya da muradi na ainihi domin gane ainihin abin da yake koyarwa, ba wanda zai nemi ya muzanta shi ba kamar yadda Deedat yake ba da shawarar a yi ta wurin shafa launi ga matanansa (Is the Bible God’s Word?, shafi na 41), wanda kuma zai girmama Littafi Mai Tsarki kamar yadda ya ke so ya ga Kirista yana girmama Kur’ani. Waɗanda suke ɗauke da hassada irin ta Deedat, kada ma su damu da buɗe Littafi Mai Tsarki, sai lokacin da suka sāke halinsu dangane da Littafi Mai Tsarki. Suna kama da waɗanda Kur’ani ya yi magana a kansu, lokacin da ya ce, kamanninsu kamar na jaki ne da yake ɗauke da littattafai (Suratul Jumu’a 62:5). Kamar yadda jaki bai san darajar kayan da yake ɗauke da shi ba, haka yake ga mutane da suke da jahilcin dukiyar ruhaniya da suka ɗauka da hannuwansu marsa wanki.

Bari Allah Mai Iko Dukka, cikin girman jinƙai da ƙaunarsa ya ba mu ikon da dukanmu za mu kai ga sanin gaskiyarsa mai tsarki – mu kuma yarda mu neme ta duk inda take samuwa. Bari dukan Musulmi waɗanda suka sami mallakar Littafi Mai Tsarki su iya gane maɗaukakiyar gaskiya, da martaba ta wurin karanta shi da zuciya ɗaya, da muradi na gaskiya don sani da ganewar koyarwarsa da bishewarsa.

KACINCI-KACINCI

Idan ka karanta ɗan littafin nan a hankali, za ka iya amsa tamboyoyin nan, waɗanda suke sashi ne na Makarantarmu ta Littafi Mai Tsarki a Gida:

  1. Yaya aka rubuta Maganar Allah a cikin Littafi Mai Tsarki?

  2. Ka rubuta ayoyi biyu na Kur’ani masu tabbatar da rashin sākewar Tsoho da Sabon Alkawari. Ka ba da sura da ayarsu.

  3. Ina bambanci tsakanin juyin Littafi Mai Tsarki da rubutun Littafin Mai Tsarki?

  4. Don me Uthman ya umarta a ƙone dukan rubutattun Kur’ani sai nasa kaɗai aka bari?

  5. Yaya ka fahimci kalman nan “budurwa” Ko “almah” kamar yadda take cikin Ishaya 7:14?

  6. Ka rubuta wasu ayoyin Sabon Alkawari da suke magana a kan hawan Yesu zuwa sama.

  7. Don me mai bishara Matiyu ya mori Bisharar Markus ta zama littafin samun bayani da Matiyu ya rubuta Bishararsa?

  8. Yaya za ka iya sasanta 2Sama’ila 24:1 da 1Tarihi 21:1?

  9. Yaya za ka bayyana rubutun labarin Yahuza da Tamar a cikin Farawa 38?

  10. Yaya za ka iya daidaita tsakanin sassalar Yesu a cikin Bisharar Matiyu da ta Luka?

Ka rubuta amsoshin tambayoyin nan a wata warkar takarda ba tare da wani sharhi ba. Idan ka amsa mafiya yawa na tambayoyin nan da kyau, za mu aiko maka da wani daga cikin littattafanmu, domin ka ƙara ƙarfafa kanka cikin bangaskiya, da ƙauna.


P.O.Box 66
CH - 8486 
Rikon
Switzerland