YA UBANGIJI KA KOYA MINI HANYARKA!

YA UBANGIJI KA KOYA MINI HANYARKA!

Iskander Jadeed


TAMBAYOYI:

Islama, da shike zaɓaɓɓen Addini ne na Allah, addini ne da Allah ya saukar domin masu yi masa sujada.

Amma akwai wasu sauran addinai da yawa. Ko a cikinsu akwai mai wani abu da ya fi Islama?

Idan kuwa har akwai, me kake tunani a game da furcin Allah, cewa: Gaskiya ne addini karɓaɓɓe ga Allah shi ne Islama!

A.G. MAROCCO

A cikin littafinsa mai suna Ruhun Addinin Islama (A Turance ana kiran shi “The spirit of the Islamic Religion”), babban malamin nan Afif Tabbara ya ba da sassalar kalmar Al-Islam daga “Salima” ma’ana:

1. Kuɓuta ce daga laifuka ɓoyayyu ku tonannu

2. Sulhuntuwa da zaman lafiya

3. Biyayya da miƙa wuya

(“The spirit of the Islamic Religion,” shafi na 17), (wato Ruhun Addinin Islama shafi na 17).

A game da ma’anar ruhaniya bai iyakance kansa ga addinin da Muhammadu ɗan Abdullahi ya yaɗa ba, amma ya haɗa da kowane addini basamaniye wanda ya ɗayanta Allah. Kur’ani kansa ya shaida wannan gaskiyar, wadda aka tabbatar ta wurin faɗin nan, “Ibrahim bai kasance Bayahude ba, kuma bai kasance Banasare ba, amma ya kasance mai karkata zuwa ga gaskiya, mai sallamawa, kuma bai kasance daga masu shirki ba” (Suratu Al Imrana 3:67).

Ibrahim ya yi zamaninsa dubban shekaru kafin zamanin shigowar Musulunci, sanin kowa ne wannan. Duk da haka Kur’ani ya ɗauke shi a shi musulmi ne, domin ya gaskata cewa Allah ɗaya ne.

Ba shakka, cikin fassarar da Jalalaini ya yi a kan ayan nan ta Imrana 67 mun karanta, “Ibrahim ya kauce wa dukan sauran addinai don ya rungumi bangaskiyar da ke daidai (Musulmi ke nan) yana gaskata ɗayantakar Allah, don Ibrahim ba mai bautar gumaka ba ne.”

Haka kuma matanan Kur’ani suka nuna cewa, kalman nan “Islama” ta shafi Yahudawa, su da suke riƙe da Attaura. Muna karanta wannan batu: “Lalle ne mu, mun saukar da Attaura, a cikinta akwai shirya da haske, annabawa waɗanda suke sun sallama, suna yin hukunci da ita ga waɗanda suka tuba (Yahudu), da malaman tarbiyya da manyan malamai... ” (Suratul Maida 5:44). Fassarar Jalalaini ta kalman nan “sallamawa” a nan tana nufin miƙa wuya ga bishewar Allah.

Ta kuma shafi Kirista kamar yadda Kur’ani ya tabbatar, da ya ce, “To, a lokacin da Isa ya gane kafirci daga gare su, sai ya ce, ‘su wanene mataimakana zuwa ga Allah?’ Hawariyawa suka ce: ‘Mu ne maitaimakan Allah. Mun yi imani da Allah. Kuma ka shaida cewa, lalle ne mu, masu sallamawa ne’” (Suratu Al Imrana 3:52).

Yanzu manzanni a nan su ne almajiran Almasihu su goma sha biyu, waɗanda suka bi shi tun daga farkon aikinsa, wannan fa tun kafin zamanin shigowar addinin Islama ne, ƙarnoni da dama da suka gabata. Har su ma Kur’ani ya kira su “Musulmi”(miƙa wuya).

Ya shar’anta muku, game da addini, abin da ya yi wasiyya da shi ga Nuhu, da abin da muka yi wahayi da shi zuwa gare ka, da abin da muka yi wasiyya da shi ga Ibrahim da Musa da Isa, cewa ku tsayar da addini sosai, kuma kada ku rarrabu a cikinsa” (Suratush Shura 42:13).

Daga nan, bisa ga ayan nan Islama ya gaskata Musa da Yesu (Isa) yana kuma riƙe da Attaura da Linjila. A wani kuma Kur’ani yana danƙa wa mutane addinin Ibrahim, da Musa, da Yesu, alal misali addinin Attaura da Linjila tare. Kamar yadda muka karanta wannan batu a nan:

“Ku ce ‘mun yi imani da Allah, da abin da aka saukar zuwa gare mu da abin da aka saukar zuwa ga Ibrahim da Isma’ila, da Ishaku, da Yakubu da Jikoki, da abin da aka bai wa Musa da Isa, da abin da aka bai wa annabawa daga Ubangijinsu, ba mu rarrabewa a tsakanin kowa daga gare su, kuma mu, a gare shi, masu sallamawa ne’” (Suratul Baƙara 2:136).

“Waɗancan ne waɗanda muka bai wa Littafi da hukunci da annabci. To, idan waɗannan (mutane )sun kafirta da ita, to, hakika, mun wakkala wasu mutane gare ta, ba su zama game da ita kafirai ba. Waɗancan ne Allah ya shiryar, saboda haka ka yi koyi da shiryarsu” (Suratul Anam 6:89,90). “Sai wata ƙungiya daga Bani Isra’ila ta yi imani, kuma wata ƙungiya ta kafirta. Sai muka ƙarfafa waɗanda suka yi imani a kan maƙiyansu, saboda haka suka wayi gari marinjaya” (Suratus saff 61:14).

Muhimmin abin da ke cikin ayoyin nan shi ne, Kur’ani ya yarda, ya kuma amince Yahudawa masu bin Musa ne, daga bisani kuma ya amince da masu bin Almasihu, yana kiran su “Musulmi”. An umarci Muhammadu ya sami bishewa daga goguwarsu, an kuma umarce shi ya riƙa tambayarsu don ya iya kawar da shakku a game da addini, kuma yadda yake cikin ayoyin nan:

“To idan ka kasance a cikin shakka daga abin da muka saukar zuwa gare ka, sai ka tambayi waɗanda suke karatun littafi daga gabanninka Lalle ne, hakika gaskiya ta je maka daga Ubangijinka domin haka kada ka kasance daga masu kokanto” (Suratu Yunus 10:94).

Zuwa ga Aboki,

Ka kira Kur’ani don ya yi iƙirarin cewa Islama ne kaɗai addinin da Allah ya zaɓa, ka manta cewa, Kur’ani kansa ya mutunta Linjila sa’ad da ya nuna:

“Kuma sai mutanen Linjila su yi hukunci da abin da Allah ya saukar, a cikinta. Kuma wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah ya saukar, to, waɗannan su ne fasiƙai” (Suratul Maida 5:47).

Ya ku waɗanda suka yi imani da Allah da Manzonsa, da Littafin da ya sassaukar ga Manzonsa da Littafin nan wanda ya saukar daga gabani. To, wanda ya kafirta da Allah da mala’ikunsa da Littattafansa, da Manzanninsa, da Ranar Lihira, to, lalle ne ya ɓace, ɓata mai nisa” (Suratun Nisa 4:136).

Zai yiwu ayoyin biyu za su i maka ka yi la’akari da matsayinka dangane da addinin Allah cikin Linjila; tun da shike suna kira gare ka ka bi umarninsu, wanda gaba da kome shi ne gaskatawa da Yesu Almasihu wanda ya ce:

“Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina” (Yahaya 14:6).

“Ai, ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai. Wanda ya gaskata da ni, ko ya mutu zai rayu” (Yahaya 11:25).

“Ba kuwa wanda ya san Ɗan sai dai Uban, ba kuma wanda ya san Uban sai Ɗan da kuma wada ya so ya bayyana wa. Ku zo gare ni dukanku masu wahala, masu fama da kaya, ni kuwa zan hutasshe ku” (Matiyu 11:27,28).

Ba shakka babu wani addinin da ya fi wanda yake gudanowa daga ƙaunatacciyar Linjila ta Allah. Ta yi dabam, ba don ta kasance wasiƙar da aka aiko ba, amma ta wurin mutumin allahntaka da ya zo a lokacin da ya dace, ya zama mutum domin ya bayyana ƙaunar Allah cikin fansa, ya kuma ceci duniya ta wurin alheri. Linjila ce take cewa:

“Tun fil azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah yake, Kalman nan kuwa Allah ne. Shi ne tun fil azal yake tare da Allah. Dukan abubuwa sun kasance ta gare shi ne, ba kuma abin da ya kasance na abubuwan da suka kasance sai ta game da shi. Shi ne tushen rai, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane. Haske na haskakawa cikin duhu, duhun kuwa bai rinjaye shi ba.

“Akwai wani mutum da Allah ya aiko, mai suna Yahaya. Shi fa ya zo shaida ne, domin ya shaidi hasken, kowa ya ba da gaskiya ta hanyarsa. Ba shi ne hasken ba, ya zo ne domin ya shaidi hasken. Akwai hakikanin haske mai shigowa duniya da ke haskaka kowane mutum.

“Da yana duniya, duniya ma ta wurinsa ta kasance, duk da haka duniya ba ta san shi ba. Ya zo ga abin mulkinsa ne, jama’a tasa kuwa ba ta karɓe shi ba. Amma duk iyakar waɗanda suka karɓe shi, wato masu gaskatawa da sunansa, ya ba su ikon zama ’ya’yan Allah wato waɗanda aka haifa ba daga jini ba, ba daga kwaɗayin jiki ko nufin mutum ba, amma daga wurin Allah.

“Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakrsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Ubansa.

“Yahaya ya shaide shi, ya ɗaga murya ya ce, ‘Wannan shi ne wanda na ce, “Mai zuwa bayana ya zama shugabana, domin da ma yana nan tun ba ni.’” Dukanmu kuwa daga falala tasa muka samu, alheri kan alheri. Domin shari’a ta hannun Musa a ka ba da ita, alheri da gaskiya kuwa ta wurin Yesu Almasihu suka kasance. Ba mutumin da ya taɓa ganin Allah daɗai. Makaɗaicin. Ɗa, wanda yake yadda Allah yake, wanda kuma yake a wurin Uba, shi ne ya bayyana Shi” (Yahaya 1:1-18).

Kalamin manzanci daga Bulus jarumin bangaskiya yana cewa: “Haka yake a gare mu, wato sa’ad da muke kamar yara, a cikin ƙangin bautar al’adun duniya muke. Amma da lokaci ya yi sosai, sai Allah ya aiko Ɗansa, haifaffen mace, haifaffe kuma ƙarƙashin shari’a, domin ya fanso waɗanda ke ƙarƙashin Shari’a, a mai da mu a matsayin ’yan’yan Allah” (Galatiyawa 4:3-5).

Addinin Kirista, addini ne na fansa, wadda in ba tare da ita ba, har yanzu da muna nan a danne ƙarƙashin nauyin kayan zunubi, marasa bage a cikin duniya, kuma ƙaddararru zuwa gidan wuta. Amma Allah da yake mawadacin jinƙai, ya shirya ceton mutum ta wurin mutuwar hadaya ta Almasihu, ta haka ya nuna ƙaunarsa marar iyaka kuma mai banmamaki. Almasihu ya bayyana wannan ƙauna da yake cewa:

“Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya, har ya ba da Makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya halaka, sai dai ya sami rai madawwami” ((Yahaya 3:16).

Addinin Buddah yana cewa:

“Nagarta da adalci duka biyu hanyoyi ne waɗanda suka nufi zuwa wurin da ake kira Nirvana, wato nagarta mafi girma.”

Addinin Yahudanci yana cewa:

“Musa ya rabuta a game da adalcin Shari’a, duk wanda ya kiyaye ta, ta wurinta zai rayu.”

Addinin Islama yana cewa:

“A waccan rana, gaskiya ce mai nauyi. Waɗanda awonsu ya fi nauyi, su ne masu nasara.”

Dukan abubuwan nan da aka ambata, suna da kyau, amma suna matsa wa mutum ne ya yi abin da ba zai iya ba. Ya zama kamar a ce wa shanyayye ya yi tafiya ne, ko kuwa a ce wa mataccen mutum ya rayu!

A game da batun adalci, Sarki Dawuda ta wurin hurawar Ruhu Mai Tsarki ya ce: “Daga sama Ubangiji ya dubi mutane, ya ga ko akwai masu hikima waɗanda ke yi masa sujada. Amma dukansu sun koma baya, su duka mugaye ne, ba wanda ke aikata abin da ke daidai, ba ko ɗaya” (Zabura 14:2,3)

A game da kiyaye Shari’a kuwa, doka ta fari mafi girma, kuma tana umartar mutum cewa, “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan ƙarfinka, da dukkan hankalinka, ka kuma ƙaunaci ɗan’ uwanka kamar kanka” (Luka 10:27).

Aukuwar abubuwan yau da kullum suna koya mana cewa, ba wanda zai iya cika wannan umarni na Shari’a. Saboda haka ne waɗanda suke ƙoƙarin aikata umarnin Shari’a sukan fāɗa ƙarƙashin la’ana, gama an rubuta cewa, “Gama duk waɗanda ke dogara da bin shari’a la’anannu ne, don a rubuce yake cewa ‘Duk wanda bai tsaya ga aikata duk abin da ke rubuce a littafin Shari’a ba, la’ananne ne’” (Galatiyawa 3:10). A kan batun nauyin ayyukanmu kuwa Allah ya faɗa ta bakin bawansa Dawuda cewa, “Kabilan hamada za su durƙusa a gabansa, abokan gābansa za su kwanta warwas a cikin ƙura” (Zabura 72:9).

Annabi Ishaya ya ce, “Dukanmu muka cika da zunubi har ayyukanmu mafiya kyau ƙazamai ne duka. Saboda zunubanmu, muka zama kamar busassun ganyaye waɗanda iska take faucewa ta tafi da su” (Ishaya 64:6).

Manzo Bulus ya ce, “Babu wani mai neman Allah. Duk sun bauɗe, sun zama marasa amfani baki ɗaya, babu wani mai aiki nagari, babu kam, ko da guda ɗaya” (Romawa 3:11,12)

Gaskiya ne cewa, Shari’a tana da tsarki, kuma umarnanta masu tsarki ne, daidai ne, kuma masu adalci, amma ba ta iya ba da cikakken ceto ga mai zunubi. “Abin da ba shi yiwuwa Shari’a ta yi domin ta kāsa saboda halin ɗan adam, Allah ya yi shi, wato ya ka da zunubi cikin jiki, da ya aiko Ɗansa da kamannin jikin nan namu mai zunubi, domin kawar da zunubi. Wannan kuwa domin a cika hakkokin Shari’a ne a gare mu, mu da ba zaman halin mutuntaka mu ke yi ba, sai dai na Ruhu” (Romawa 8:3,4).

Wannan ne ya sa bangaskiyar Kirista ta sha dabam. Addini ne na fansa, ba shi barin mutum cikin rashin ceto. Domin kuwa Allah yakan yi hulɗa da shi bisa ga alheri sa’ad da shi mutum ya yarda da hadayar mutuwar Almasihu a kan gicciye.

Tun da shike Shari’a ba ta iya kuɓutar da mutum daga ikon zunubi da na mutuwa, to, kuwa ta kāsa kawo masa ceto, ta kuma kāsa tsarkake shi ke nan, ba ta kuma iya sa ya cancanci mulkin Allah ba. Almasihu, wanda yake Ubangiji daga sama ya ɗauki jiki irin na ɗan adam, ya yi tarayya cikin jiki da jini na mutum, domin ya ba da kansa a madadin hadaya ta zunubi, ya halaka zunubi, ya karya ƙangin da ta ke riƙe mutum da shi, ya kuma ɗauki hukunci a madadin mutum. Ta wurin wannan aikin fansa ne mai wuya ya biya bukatarmu domin dukan abubuwan da shari’a take biɗa daga gare mu, ya kuma cika faɗin annabci: “Amma ya daure da wahala wadda a ainihi tamu ce, raɗaɗin da ya kamata mu ne za mu sha shi. Mu kuwa muna tsammani wahalarsa hukunci ne Allah ya ke yi masa. Amma aka yi masa rauni saboda zunubanmu, aka daddoke shi saboda muguntar da muka aikata. Hukuncin da ya sha ya ’yantar da mu, dukan da aka yi ta yi masa, ya sa muka warke. Dukanmu muna kama da tumakin da suka ɓata, kowannenmu ya kama hanyarsa. Sai Ubangiji ya sa hukunci ya sauko a kansa, hukuncin da ya wajaba a kanmu” (Ishaya 53:4-6). Zai zamar maka da wuya ka yarda da ra’ayin nan na fansa, domin kuwa fansa ta kahu ne a kan mutuwar Almasihu ta kunya a kan gicciye - batun da yake laifi ne mai ban takaici ga Musulmi. Amma duk da haka, al’amuran da suke tabbatar da mutuwar Almasihu a kan gicciye suna da yawa, kuma babu tantama a kansu. Na harhaɗe su cikin wani ɗan littafi da aka kira a turance, “The Cross in the Gospel and the Koran” ma’ana Gicciye a cikin Linjila da Kur’ani, kana iya samunsa daga “Kiran Bege”.

Daga cikin fitattun abubuwa na bangaskiyar Linjila su ne umarnan kyautata rayuwar jama’a da suka dace da kowane zamani, ko tsara, ko jama’a, ko harshe ko al’umma. Waɗannan umarni sun kahu a kan “ƙaƙƙarfar Doka” wadda Almasihu ya kafa. Ya ce, “Saboda haka duk abin da kuke so mutane su yi muku, kuma sai ku yi musu domin wannan shi ne Attaura da koyawar annabawa” (Matiyu 7:12).Wannan Doka ta hana sonkai, da ƙiyayya, da ɗaukar fansa, da rikici, da ruɗi, da zamba, ta kuma kafa haɗa kan dukan ’yan adam, da daidaitakar dukan membobinta, ta kuma nemi kowa ya kyautata wa sauran mutane.

Wannan doka a taƙaice ne kawai, amma kiyaye ta da zai hana husuma da yaƙe-yaƙe, ya kuma sa wannan duniya ta zama aljanna mai cike da farin ciki. Don kuwa a cikin dokan nan ne ake samun ainihin abin da Shari’a da Annabawa su ke koyarwa, tun da manufar dokar ita ce don ta sa mutum ya ƙaunaci ɗan’uwansa kamar kansa.

A ƙashin gaskiya, wannan Doka mai daraja tana koya mana yadda za mu cika dokar da take cewa, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” wadda manzo Bulus ya yi sharhi a kanta cewa; “... don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Shari’a ke nan. Umarnan nan cewa, ‘kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka yi ƙyashi,’ da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma cewa, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ ƙauna ba ta cutar maƙwabci, saboda haka ƙauna cika Shari’a ce” (Romawa 13:8-10).

Kuma don Almasihu ya kawar da dukan abin da zai hana zaɓaɓɓunsa iya samun wannan irin ƙauna mai daraja ƙwarai, sai ya ce musu: “Amma ni ina gaya muku, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa masu tsananta muku addu’a, domin ku zama ’ya’yan Ubanku wanda ke cikin sama. Domin yakan sa rana tasa ta fito kan mugaye da kuma nagargaru, ya kuma sako ruwan sama ga masu adalci da marasa adalci. In masoyanku kawai kuke ƙauna, wace lada ce da ku? Ashe, ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba? In kuwa ’yan’uwanku kaɗai kuke gayarwa, me kuka yi fiye da waɗansu? Ashe, ko al’ummai ma ba haka suke yi ba? Saboda haka, sai ku zama cikakku, kamar yadda Ubanku na sama yake cikakke” (Matiyu 5:44-48).

Sa’an nan, waɗannan ka’idodi, cikin fifikonsu, ratarsu, da zurfinsu, suna nuna fifikonsu a kan ƙaunar da aka saba da ita, da ƙaunar jama’a da suka kahu bisa ka’idar sonkai, waɗanda suke kurarinsu shi ne, cuɗa ni in cuɗe ka, wato in na baka, sai kai ma ka ba ni, Saboda haka Almasihu yana nufin mu yi ƙauna saboda ingancinta, mu kuma yi muradin zaman jin daɗin sauran jama’a, mu kuma lazamci adalci da halin kirki saboda darajarsu, wato adalci da zaman kirki.

Manzannin Almasihu sun fāɗaɗa koyarwar mai gidansu a kan ƙauna cikin kyawawan bayanai ta wurin hurewar Ruhu Mai Tsarki. Ga irinsu:

1. Manzo Yahaya

“Ya ku ƙaunatattuna, ba fa wani sabon umarni nake rubuto muku ba, a’a, daɗaɗɗen umarnin nan ne wanda kuke da shi tun farko. Daɗaɗɗen umarnin nan kuwa, ai shi ne maganar da kuke ji. Har wa yau sabon umarni nake rubuto muku, wanda ke tabbatacce ga Almasihu, da kuma a gare ku, domin duhu yana shuɗewa, hakikanin haske kuma na haskakawa.

“Kowa ya ce yana cikin haske, yana kuwa ƙin ɗan’uwansa ashe, a duhu yake har yanzu. Mai ƙaunar ɗan’uwarsa, a haske yake zaune, ba kuma wani sanadin sa tuntuɓe a gare shi. Mai ƙin ɗan’uwansa kuwa, a duhu yake, a cikin duhu yake tafiya, bai san ma inda yake sa ƙafa ba, domin duhun ya makantar da shi” (1 Yahaya 2:7-11).

“Ya ku ƙaunatattuna, sai mu ƙaunaci juna, domin ƙauna ta Allah ce. Duk mai ƙauna kuwa haifaffen Allah ne, ya kuma san Allah. Wanda ba ya ƙauna, bai san Allah ba sam, domin Allah shi ne ƙauna. Ta haka aka bayyana ƙaunar Allah a gare mu, da Allah ya aiko da Ɗansa makaɗaici a duniya, domin mu sami rai madawwami ta wurinsa. Ta haka ƙauna take, wato ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunce mu, ya aiko Ɗansa hadayar sulhu saboda a gafarta zunubanmu. Ya ku ƙaunatattuna, tun da yake Allah ya ƙaunace mu haka, ai mu ma ya kamata mu ƙaunaci juna. Ba mutumin da ya taɓa ganin Allah daɗai, amma kuwa in muna ƙaunar juna, sai Allah ya dawwama cikinmu ƙaunan nan tasa kuma ta cika a cikinmu.

“Ta haka muka sani muna zaune cikinsa, shi kuma cikinmu, saboda Ruhunsa da ya ba mu. Mun duba, muna kuma ba da shaida, cewa Uba ya aiko ɗan ya zama Mai Ceton duniya. Kowa ya bayyana yarda, cewa Yesu Ɗan Allah ne, sai Allah ya dawwama cikinsa, shi kuma a cikin Allah. Mun sani, mun kuma gaskata ƙaunar da Allah ke yi mana.

“Allah shi ne ƙauna, wanda ke a dawwame cikin ƙauna kuwa, ya dawwama a cikin Allah ke nan, Allah kuma a cikinsa. Ta haka ne ƙauna ta cika a gare mu har mu kasance da amincewa a ranar Shari’a, domin kamar yadda yake, haka mu ma muke a duniya nan. Ba tsoro ga ƙauna, amma cikakkiyar ƙauna takan yaye tsoro. Tsoro kansa ma azaba ne, mai jin tsoro kuwa ba shi da cikakkiyar ƙauna.

“Muna ƙauna domin shi ne ya fara ƙaunarmu. Kowa ya ce yana ƙaunar Allah, alhali kuwa yana ƙin ɗan’uwansa, to, maƙaryaci ne. Don wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa da ya ke gani, ba dama ya ƙaunaci Allah wanda bai ma taɓa gani ba. Wannan kuma shi ne umarnin da muka samu daga gare shi, cewa mai ƙaunar Allah, sai ya ƙaunaci ɗan’uwansa kuma” (1 Yahaya 4:7-21).

2. Manzo Bitrus.

“Da yake kun tsarkake ranku kuna yi wa gaskiya biyayya har kuna nuna sahihiyar ƙauna ga ’yan’uwa, sai ku himmantu ga ƙaunar juna da zuciya ɗaya” (1 Bitrus 1:22).

“Ƙarshen dukan abubuwa ya gabato. Saboda haka sai ku kame kanku, ku natsu, domin ku yi addu’a. Fiye da kome kuma, ku himmantu ga ƙaunar ’yan’uwa kuma gaya, domin ƙauna takan yafe laifofi masu ɗumbin yawa” (Bitrus 4:7,8).

“Saboda wannan dalili musamman sai ku yi matuƙar himma, ku ƙara bangaskiyarku da halin kirki, halin kirki da sanin ya kamata, sanin ya kamata da kamunkai, kamunkai da jimiri, jimiri da bin Allah, bin Allah da son ’yan’uwa kuma da ƙauna. In kuwa halayen nan sun zama naku ne har suna yalwata, za su sa ku kada ku yi zaman banza, ko marasa amfani wajen sanin Ubangijinmu Yesu Almasihu” (2 Bitrus 1:5-8).

Fiye da waɗannan duka, ku ɗauki halin ƙauna, wadda dukkan kammala ke ƙaulluwa a cikinta” (Kolosiyawa 3:14).

3. Manzo Bulus

“Ko da zan yi magana da harsunan mutane, har da na mala’iku, amma ya zamana ba ni da ƙauna, na zama ƙararrawa mai yawan ƙara ke nan, ko kuwa kuge mai amo. Ko da zan yi annabci, ina kuma fahimtar dukkan asirai, da dukkan ilimi, ko da kuma ina da matuƙar bangaskiya har yadda zan iya kawar da duwatsu, muddin ba ni da ƙauna, to, ni ba kome ba ne. Ko da zan sadaukar da duk abin da na mallaka, in kuma ba da jikina a ƙone, in har ba ni da ƙauna, to, ban amfana da kome ba.

“Ƙauna tana sa haƙuri da kirki. Ƙauna ba ta sa kishi, ba ta kumbura. Ƙauna ba ta sa ɗaga kai ko rashin kāra, ƙauna ba ta sa sonkai, ba ta jin tsokana, ba ta riƙo. Ƙauna ba ta farin ciki da mugunta, sai dai da gaskiya. Ƙauna tana sa daurewa cikin kowane hali, da bangaskiya cikin kowane hali, haka sa zuciya cikin kowane hali, da jimiri cikin kowane hali.

“Ƙauna ba ta ƙarewa har abada. Annabci zai shuɗe, harsuna za su ɓace, ilimi kuma zai gushe. Ai, hakika iliminmu ba cikakke ba ne, annabcinmu kuma ba cikakke ba ne. Sa’ad da kuwa cikakken ya zo, sai ɗan kiman nan ya shuɗe. Sa ad da nake yaro, nakan yi magana irin ta ƙuruciya, nakan yi tunani irin na ƙuruciya, nakan ba da hujjoji irin na ƙuruciya. Da na isa mutum kuwa, sai na bar halin ƙuruciya. Gama yanzu kamar a madubi muke gani duhu-duhu, a ranan nan kuwa za mu gani ido da ido. Yanzu sanina sama sama ne, a ranan nan kuwa zan fahinta sosai, kamar yadda aka fahimce ni sosai.

“To, yanzu abubuwan nan uku sun tabbata, bangaskiya, da sa zuciya, da kuma ƙauna, amma duk mafi girma a cikinsu ita ce ƙauna” (1 Korantiyawa 13 – wani lokaci akan san ta da ‘Surar Ƙauna’).

Wannan shi ne Kristanci na ainihi. Addini ne da yake kafe cif cikin ruhun fansa, wanda in ya yiwu a gafarta laifofi har bakwai sau saba’in. Addinin Kirista ne ya fita dabam daga sauran addinan duniya ta dalilin darajar jinin Almasihu, wanda “yake maganar abubuwa masu kyau fiye da jinin Habila.” Don kuwa jinin Habila yana kai ƙara ne ga Allah don a ɗaukar masa fansa, amma jinin Almasihu ya yi kira ne na roƙon gafarar Allah domin masu kisansa. Mun karanta cewa Yesu ya yi kira daga kan gicciye cewa: “Ya Uba ka yi musu gafara don ba su san abin da su ke yi ba” (Luka 23:34).

TAMBAYAR

“Gaba ɗaya, Islama shi ne saƙo na ƙarshe, kuma shi ne addini domin kowa da kowa, wanda ya dace da kowane wuri da kowane zamani, ba kamar Kristanci ba, wanda ya duƙufa ga ibada a wuri guda cikin rayuwa irin ta zuhudu. Saboda haka ne wannan ya hana ku yin tunani da ƙoƙarin gwada Kur’ani da abin da kuke kira ‘Linjila (Bishara)’.

Mun samu cewa, Kur’ani maganar Allah ne, bari ya sami ɗaukaka, Linjila kuwa wato Bishara, ta ƙunshi maganganun mutane ne kawai, irin su Bulus da Yahaya.

A ƙarshe ina so in yi maka jagora zuwa ga madaidaiciyar hanya... domin kuwa irin shiryayun ƙarairayin nan, (aikin banza kawai) nan da nan ake iya gane su yanzu! Kun yi ta yin ƙoƙari fiye da sau ɗaya don ku fizge ɗaya daga cikin Musulmi, amma kun kāsa samun ko da guda ɗaya ne, alhali kuma Kirista masu tarin yawa sun rungumi addinin Islama.”

A.A.A. Mulkin Sa’udiyya

Daga bayanin da ka mora cikin wasiƙarka, a fili yake cewa, kai kam, mai kishin addini ne, yana kuma da kyau ga saurayi kamar ka ya zama mai kishin addininsa muddin dai bai wuce gona da iri ba cikin tattaunawa a tsakanin Kirista da Musulmi. Sa’ad da ka ƙalubalanci gaskatarwar “Mutanen Littafi” ta irin wannan hanya, to, ka karya umarnin Kur’ani ke nan mai cewa, “Kada ku yi jayayya da mazowa Littafi sai fa da magana wadda ta fi kyau...” (Suratul Ankabut 29:46).

Ba shakka ɗokinka ne ya kai ka wata kwana inda ba za ka iya jin daɗin wahayi/bayanin da Linjila take samarwa ba. Saboda haka, ban yi mamaki ba da ka ɗauki ’yan takardun sha’anin ruhaniya da muka aiko maka, ka maishe su tarin ƙarairayi da aikin banza kawai.

Ba na so in shiga gardama da kai a game da batun nan cewa, Islama ne saƙo na ƙarshe.

Amma duk da haka, zan jawo hankalinka, cikin ƙauna, ga ainihin gaskiya, wato lokacin da ka furta cewa Islama ta zarce dukan addinai har da na Kristanci, to, ka musunci Kur’ani ke nan ta wurin jahilcinka na matani, wato nassoshin da suke tabbatar da addinin Attaura da na Linjila (Bishara).

Zai yiwu ka sami wannan ra’ayin sharewa/sokewa daga littafin nan da ake kira a Turance “Guidance of seekers into Origins of Religion,” wato “Jagora ga masu neman sassalar addinai” wanda wani mutumin Farisa ya rubuta mai suna, Mawia Mohammad Takieddine Al Kashani, wanda ya ce Muhammadu ne annabin wannan zamani, addininsa kuma ya soke/share addinan annabawan farko.

Don in amsa maka wannan, zan ce maka: Kur’ani da kansa bai ce ya zo don ya zarce Attaura da Linjila ba balle ma a ce ya fi su; haka kuma Hadisan Annabawa ba su faɗi haka ba. Don haka wannan magana taka abar ba’a ce mai bantakaici, marar tushe kuma, sai dai masu rashin isasshen hankali ne waɗanda an riga an yi wa hankalinsu allurar dafin mugun kishin addini. In ma har wannan zargin bai juyar da koyarwar Kur’ani ba, to, a ƙalla ya kawo ruɗarwa cikin koyarwa, yana sa Kur’ani ya faɗi abin da bai ƙunsa ba. Kowa ya san cewa sharewa/sokewa (wani abin da ya zarce wani abu daban) ya shafi nassoshin Kur’ani ne kaɗai ya kuwa faru a wurare biyu:

1. “Abin da muka shafe daga aya, ko kuwa muka jinkirtar da ita, za mu zo da mafi alheri daga gare ta ko kuwa misalinta” (Suratul Baƙara 2:106).

2. “Kuma ba mu aika wani manzo ba a gabaninka, kuma ba mu umarci wani annabi ba, face idan ya yi buri, sai Shaiɗan ya jefa (wani abu) a cikin burinsa, sa’an nan Allah ya shafe abin da Shaiɗan ke jefawa, sa’an nan kuma Allah ya kyautata ayoyinsa. Kuma Allah masani ne, mai hikima” (Suratul Hajj 22:52).

Waɗannan ayoyi biyu ba su cewa Kur’ani ya zo don ya share (soke) Littafi Mai Tsarki ba, amma akwai wasu ayoyin Kur’ani da suka share juna. Wani shehin malami mai suna Al-Baidawi ya bar mana fayyatacciyar tattaunawa a game da batun sharewa a cikin Sura ta Hajji, kuma ya ambaci wasu batutuwa daga Suratun Najimi, waɗanda aka share. Kana iya duba fassarorin nan in kana so.

Wasu kuma sun ambaci wannan batu muhimmi, kamar su Yahaya, da Jalal - Ed- Din. An ambace su a fakaice a cikin littafin nan mai suna Rayuwar Annabi Ibn Hisham ya rubuta da yake ruwaita abin da Ibn Ishaq ya faɗa. Wani marubucin kuma mai suna Al-Tabari ya yi magana a game da wannan batu a cikin fassararsa da ya fāɗaɗa.

Ibn Hatem ya ba da labarin da ya samo daga Ibn Abbas cewa, “Mai yiwuwa ne cewa, wahayin ya sauko wa annabi da dare ne, shi kuma ya manta da kashegari. Saboda haka ne aka saukar da ayar, ‘kowace aya kuma da muka share ko muka jinkintar’ da dai sauransu” (dubu abin da aka ambata a bisa).

Al-Baidawi kuwa cewa ya ke yi, “Ita (wannan aya) ta sauko a lokacin da masu bautar gumaka ko Yahudawa suka yi zargin cewa, “Ba ku ga yadda Muhammadu ya umarci masu binsa, daga nan ya canza ra’ayinsa, ya kuma ba su wani umarni da yake akansin na fari!” Ta haka zarafin kawo wannan aya ya nuna a sarari don ba da amsa ga wannan shakku na marabuta, da kuma sauran Musulmi a game da sāke-sāke a cikin wasu ayoyin Kur’ani kansa.

Bugu da ƙari, Jalalaini ya ba da wannan fassara: Annabi yana karatu daga cikin Suratun Najm a gaban majalisa, “Shin kun ga Lata da Uzza? Da (wani gunki wai shi) Manata, na ukunsu?” (Suratun Najm 53:19,20). Shaiɗan ne ya ke sa waɗansu kalmomi a kan harshensa ba tare da sanin shi annabi ba: “Waɗannan talikai na sama, masu ji da ƙuruciya, masu ban sha’awa da kyan gani, muna sa zuciya za su yi roƙo domin mu.” Wannan ya sa su murna. Amma Jibra’ilu ya faɗa masa abin da Shaiɗan ya sa a harshensa. Sai ya yi nadama, ya kuma ta’azantad da kansa da wannan aya, “Amma Allah ya share abin nan da Shaiɗan ya saka, ya jefar, da dai sauransu.”

Bisa ga abin da Al-Sayauti ya ce, sharewa/sokewa ba baƙon abu ba ne ga al’umma, wato Islama ke nan.

In muka kafa ƙarshen maganarmu a game da wannan batu a kan sharhohin manyan masanan nan, muna iya cewa gabagaɗi ƙage-ƙagen da ake yi a game da cewa Kur’ani ya zarce Linjila (Bishara) ko Islama ta zarce sauran addinai, wannan ba daidai ba ne, kuma ba shi da tushe.

Cikin littafinsa mai suna “Bayyana Gaskiya”, Al-Hajj Rahmat Allah Al--Hidi yana cewa: “Faɗar da aka yi cewa, zuwan Zabura ya share Attaura, zuwan Linjila ya share Zabura, saukar Kur’ani kuma ya share Linjila (Bishara), wannan batu ba shi da tushe ko asali a cikin Kur’ani ko kuma cikin Al’adun Annabawa. Lalle kalaman shehin masanin nan gaskiya ne. Kur’ani ya ƙaryata batun sokewan nan da wasu suke yin iƙirari, Kur’ani ya bayyana cewa wannan batu ba gaskiya ba ne lokacin da ya ce: “Ya shar’anta muku, game da addini, abin da ya yi wasiyya da shi ga Nuhu da abin da muka yi wahayi da shi zuwa gare ka, da abin da muka yi wasiyya da shi ga Ibrahim da Musa da Isa, cewa ku tsayar da addini sosai, kuma kada ku rarrabu a cikinsa” (Suratush Shura 42:13).

Saboda haka, abokina, ka gani, kana sukar addininka ne da kanka, wato addinin Islama, ta wurin iƙirarin cewa addinai saukakku daga sama da suka rigayi na Islama wai an share/soke su. Hakika, kai da kake Musulmi, yanzu ka iya gaya mini, kai da ke gaskata Kur’ani, da faɗarsa, za ka iya yin wannan iƙirari mara tushe, ba tare da ka taki wata gaskiya ba?

Abokina, ko ka manta cewa, Kur’ani yana kira gare ka da sauran Larabawa cewa, a yi muku jagora da umurnan Mutanen Littafi? Ba shakka Kur’ani ya ce, “Allah yana nufi ya bayyana muku, kuma ya shiryar da ku hanyoyin waɗanda suke a gabaninku, kuma ya karɓi tubarku. Kuma Allah masani ne Mai Hikima” (Suratun Nisa 4:26).

A maimakon haka, kamata ya yi ka yi tambaya haka, “Ko mai yiwuwa ne addininmu ne aka zarce?” tun da yake Kur’ani ya umarci Muhammadu kansa ya bi jagorancin namu jagoran lokacin da ya ce:

“Waɗancan ne waɗanda muka bai wa Littafi da Hukunci da annabci. To, idan waɗannan (mutane) sun kafirta da ita, to, hakika mun wakkala wasu mutane gare ta, ba su zama game da ita kafirai ba. Waɗancan ne Allah ya shiryar, saboda haka ka yi koyi da shiryarsu” (Suratul An’am 6:89,90).

A maimakon haka, da sai ka yi tambaya, ta yaya aka soke ko aka canja addininmu, tun da Kur’ani kuwa ya umarci Muhammadu ya yi tambaya ga kakannimu, domin ya kawar da shakkunsa lokacin da Allah ya ke ce masa: “To, idan ka kasance cikin shakka daga abin da muka saukar zuwa gare ka, sai ka tambayi waɗanda suke karatun Littafi daga gabaninka” (Suratu Yunus 10:94).

Yanzu, ka gaya mini, ta yaya aka share addininmu, wato addinin Kirista, tun da yake Kur’ani kansa yana kira gare mu mu yi hukunci da abin da yake cikin Linjila (Bishara)? Ga fa abin da yake cewa:

“Kuma sai mutanen Linjila (Bishara) su yi hukunci da abin da Allah ya saukar a cikinta. Kuma wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah ya saukar, to, waɗannan su ne fasiƙai” (Suratul Maida 5:47).

Ya ƙaunataccen Abokina,

Ɗaya daga cikin fitattun abubuwa a game da Littafinmu Mai Tsarki shi ne, gaskiyar koyarwar da littattafansa da dama suka ƙunsa, suna nuna cikakkiyar muwafakarsu da juna, suna tafiya kuma bai ɗaya, sun doshi kusurwa guda, wato bayanin nufin Allah ga ’yan adam. Saboda haka babu sharewa/sokewa, ba a kuma share/soke shi ba ko koyarwar da ke cikinsa.

Littafin Allah, Littafi ne domin dukkan zamanai, da kuma tsararrki, da kuma addinin da Allah ne ya sa ya zama addininsa na ainihi tun fil azal, har abada abadin. A cikinsa akwai magana/batu na allahntaka: “Sararin sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta shuɗe ba” (Matiyu 24:35). Kur’ani ma ai,ya faɗa a cikin Suratul An’am 6:34 “Babu mutumin da zai musanya kalmomin Allah” (watoLinjila/Bishara). Cikin Suratu Yunus 10:64 ya ce, “Babu musanyawa ga kalmomin Allah” (Bishara). Kuma cikin Suratul Hijr 15:9 ya ce, “Lalle mu ne, muke saukar da ambato (Tunawa), kuma lalle mu, hakika, masu kiyayewa ne gare shi.”

Mun karanta kuma a cikin Suratun Nahli cewa, “Kuma ba mu aika daga gabaninka ba, face waɗansu mazaje muna yin wahayi zuwa gare su. Sai ku tambayi mutanen Ambato idan kun kasance ba ku sani ba” (suratun Nahli 16:43).

Wannan aya tana kai mu ga yin tambaya: Inda a ce taron Musulmi masu ibada, masu bin Kur’ani da aminci da za su je wurin mutanen Littafi su yi tambaya a kan al’amuran ruhaniya, waɗanda suka gagare su sani. A kan hanya kuma su gamu da wata ƙungiya ta masu iƙirarin ’sharewa/ sokewa’. Suka gaya musu cewa, ‘Za mu wurin matanen Littafi/Matanen Ambato mu tambaye su a game da al’amuran ruhaniya da ba mu sani ba’. Zan yi mamaki idan ƙungiyan nan ta masu ra’ayin sharewa za su ce musu: “kada ku je domin an share/soke Littafin nesa!” Ko da ma za su yi ƙoƙarin hana su, to, me zai zama matsayin amintattun Musulmin nan masu ibada? Za su gaskata su, ko za su gaskata Kur’ani da ya ce: “Ku tambayi mutanen Ambato idan har ba ku sani ba”.

Ba shakka, idan har suka yarda da masu ra’ayin sharewa/sokewa, to, ya zama ke nan sun amince cewa Allah ya kāsa cika alkawarinsa ke nan da ya ce: “Mu ne muka saukar da Ambato (Littafi) kuma muna kiyaye shi.”

Abokina na gaske,

Ban ga laifinka ba da ka yanke hukunci a kan Kristanci, a ganin ka addini ne na duƙufa cikin ibada da zaman zuhudu, wannan ya nuna rashin saninka a game da Kristanci.

Asalin zaman zuhudu ba daga Linjila/Bishara ba ne, amma ya taso ne daga ƙoƙarin ɗan adam, wanda ba zan iya wani sharhi a kai ba cikin filin wannan wasiƙa.

Yanzu me za ka iya cewa, idan na ɗauki ra’ayin masu bin Islama da ƙarfi, waɗanda ra’ayinsu ba a yarda da shi ba, waɗanda kuma ba su bin umarnin Kur’ani yadda ya kamata in soki addinin Islama da shi? Yin haka, na yi daidai ke nan? Na bar maka wannan ka amsa... Kuma a game da batunka cewa, Kur’ani maganar Allah ne, Linjila kuwa maganganu ne kawai na mutane irin su Bulus da Yahaya: wannan ma ya nuna irin raunin saninka a game da Kristanci.

Abokina, in ka yarda, ka fahinci cewa, Linjila/Bishara da asalinta ba kalmomin Bulus ko na Yahaya ba ne aka rubuta. Haka kuma, Linjila/Bishararmu ba Jibra’ila ne ya kawo ta sa’an nan mutane suka rubuta ba. Amma mutumin Uluhiya wanda ya zama mutum a cikar lokaci domin ya shaida ƙaunar Allah. Bugu da ƙari, cikin wannan ƙauna ya cika aikin fansa, domin ya ceci duniya ta wurin alheri.

A game da faman cika bakin da kake yi cewa, wasu Kirista sun rungumi addinin Islama, kana ambatar haka cewa, wannan tabbatarwa ce mai nuna addini guda ya fi ɗayan, ina roƙon ka ka yi sharhi a ainihin gaskiyar cewa, dubban Musulmi sun shiga/rungumi gaskatawar kwaminisanci, waɗanda ba su yarda da kasancewar Allah ba sam.

Menene kuma ra’ayinka, a kan dubun-dubatan mutanen Indonasia Musulmi da suka rungumi Kristanci ya zama addininsu?

Cikin zaman sauraron amsa daga gare ka, ina yi maka fatar alheri da salama na Allah. Ina addu’a musamman domin ka, yadda ƙaunarka za ta riƙa ƙaruwa, zai yiwu wannan ƙauna za ta kawo karɓuwa a gare ka. Zai yiwu ƙauna za ta sa ka yi bincike na neman gaskiya cikin basira. Daga nan ne za ka auna dukan abu ka riƙe mai kyau.

KACINCI - KACINCI

Zuwa ga mai karatu,

Idan ka karanta littafin nan a hankali, za ka iya amsa tambayoyin nan, har ka sami wani ɗan littafi daga littattafinmu da suna nan iri iri. Ba shakka kuma, ta haka za ka ƙaru cikin gaskiyar Allah da ƙaunarsa.

  1. Menene ma’ana iri dabam dabam ta kalman nan Islama?

  2. Don me Kur’ani ya ce Ibrahim “Musulmi” ne, ko da shike Islama bai kasance ba tukuna a zamaninsa?

  3. Don me Yahudawa da masu bin Almasihu su kuma aka ce Musulmi ne?

  4. Yaya Muhammadu ya ɗauki hurewar Allah ga Musa da Yesu?

  5. Waɗanne ayoyin Kur’ani ne suka kira Musulmi ya yarda ya kuma karanta ya kiyaye Attaura da Linjila/Bishara?

  6. Ka ba da kalmomi uku na Almasihu waɗanda ka ɗauka mafiya muhimmanci domin kai da kanka?

  7. Me ka fahinta daga ayoyin Littafi Mai Tsarki masu cewa, Almasihu “Kalman Allah” ne ya zama mutum?

  8. Ta yaya Bulus ya shaida cewa Yesu ya zama mutum?

  9. Menene ainihin tushen addinin Kirista?

  10. Yaya ka fahimci maganar cikin Yahaya 3:16?

  11. Waɗanne ne manyan ka’idodin sauran addinan duniya?

  12. Me Littafi Mai Tsarki ya ke cewa a game da nagarin ayyukan mutum?

  13. Waɗanne ne dokoki biyu mafiya muhinmanci cikin Attaura?

  14. Yaya Shari’a ta ke hukunta mutum?

  15. Don me Shari’a ba ta iya ba mutum ceto

  16. Yaya halin Yesu yake a game da Shari’a, kuma yaya ya ciccikata a aikace?

  17. Menene ma’anar “alheri” dangane da Shari’a, cikin koyarwar Linjila/Bishara?

  18. Yaya ka fahimci sanannen annabcin nan a game da Ɗan Rago na Allah cikin Littafin Ishaya?

  19. Ka rubuta kalmomin “Babbar Doka” ka kuma bayyana ma’anarta.

  20. Me ake nufi da cika Shari’a?

  21. Yaya Almasihu ya bayyana ƙaunatar magabci ga almajirinsa?

  22. Ka rubuta ayoyin da ka gani suka fi shigar maka a rai daga Manzo Yahaya.

  23. Wace shawara Manzo Bulus ya ba da ta

  24. Me ka koya daga “Surar ƙauna”– IKorantiyawa 13:1-7?

  25. Ina bambanci tsakanin kukan jinin Habila da na jinin Yesu Almasihu?

  26. Yaya ka fahimci ayan nan ta Kur’ani mai cewa “kada ku yi jayayya da Matanen Littafi”?

  27. Ta yaya batun nan mai cewa Islama ta share/soke Kristanci ya zama suka ga Kur’ani kansa?

  28. Ina ne asalin ra’ayin sharewa/sokewa?

  29. Ina matsala biyu ta sharewa/sokewa da suka iya shafar wasu ayoyin Kur’ani?

  30. Ta yaya manyan masanan Islama suka yi bayani, kuma suka kāre yiwuwar sharewa/sokewa cikin Kur’ani?

  31. Ta yaya Kur’ani ya tabbatar da rashin yiwuwar sharawa/sokewar wahayan farko da kuma kafa dokokin da suka gabata?

  32. Idan Musulmi yana shakkar wani abu cikin Kur’ani, wane matani/ayoyi ne za su jagorance shi zuwa ga Krista don samun koyarwa da bishewa?

  33. Bisa ga Suratul Maida 5:47, su wanene “Kafirai”?

  34. Me Almasihu ya ke cewa a game da dawwamar kalmominsa, ko da sama da ƙasa za su shuɗe?

Ka aiko da amsoshinka, da cikakken adireshinka da rubutu mai kyau zuwa ga adireshin nan:


P.O.Box 66
CH - 8486 
Rikon
Switzerland